Saturday 25 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (10) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
BA WA KWAKWALWA DAMAR AIKI

Mutane sun karkasu zuwa gidaje daban-daban, akwai masu ƙoƙari waɗanda kullum cikin tunanin bunƙasa ayyukansu suke yi, in ɗan kasuwa ne wanda yake sayar da gwanjo, yakan fara tunanin cewa nan gaba fa zai iya tsallake wannan sana'ar zuwa wacce ta fi ta, kamar sayar da sabbin kaya waɗanda aka yiwo odarsu daga ƙasashen waje, in mai sayar da takalma ne a bakin titi yana bin motoci da gudu, zai fara tunanin cewa nan gaba fa jarinsa zai yi yawa zai kama shago, zai zama babban Ɗan Kasuwa har mutane su riƙa zuwa suna sarin kaya a wurinsa.

Kamaida Hankali akan abinda Kake son Cimma..

MarubuciBaban Manar Alkasim

In kuma malamin makaranta ne zai fara tunanin zai zama babba har ya yi fice a fagen ilimi, zai gina Makaranta tasa mai cin gashin kanta, in karen mota ne yana tunanin zai zama Direba zai sami mota ta kansa, zai zo ya sayi motoci nan gaba ya ɗauki Direbobi yana biyansu, waɗannan abubuwa ba su rabuwa da zuciyoyin gwarazan mutane, waɗanda duk abinda za su yi suna tunanin gaba, kamar mutum mai ƙaunar ibada kullum a masallaci, har ya fara burin a ce shi ne ladanin masallacin, yau da gobe ya zama na'ibin limamin, ko a ba shi limanci a wani masallacin, da yawa in mutum zai kama haya saboda zai yi aure za ka ga ya fara tunanin inda yaransa za su riƙa kwana da tarbiyar da za su samu a matattarar, bayan ko auren ba a ɗaura ba, tsari kenan.

Da yawa mutane masu himma sun sami abinda suke buri, wani zai gaya maka shi babban soja ne, kuma wallahi tun yana ƙarami bai da buri sai aikin sojan, wani zai ce maka likita ne shi, tun yana ƙarami burinsa kenan, wasu lamuran Allah kan dubi zuciyoyim mu ne ya biya mana buƙatummu, dubi dai waƙa da ake ganin abar banza ce, na dubi Hauwa Kululu wace Mamman Shata ya yi wa waƙa, tana cewa tun tana yarinya ba ta aikuwa sai in mutum zai yi mata waƙar Shata, asali ita yariya ce ƙarama, ba ita ce mai sayar da tuwon ba babarta ce.

Lamarinta ya riƙa ba masu sayen tuwon babarta al'ajabi, kwatsam sai ga Mamman Shata ɗin wata rana ya sauka wurin babarta, aka ba shi labari kuma aka nemi ya yi mata waƙa, Shata ya zauna ya waƙe ta fes, burinta ya cika, amma fa ba arha ta sami wannan daukakar ba, sai da ta tsaya kan burinta har ta kai ga gaci, sauran lamura da kake gani a rayuwa duk haka suke, ba yadda za a yi mutum ya kai ga biyan buƙata ba tare da ya tsaya ƙyam kan abinda yake so ba, kullum tunaninsa shi ne ya zan kai ga wannan ƙudurin nawa?

Burina a ce na zama malami, na fara koyarwa ne a makarantar Islamiyya ta dare, a hankali har na dawo ta safe, na koma furamare, na fara karantarwa a sakandare da ta manyan mutane, na karantar a kwaleji kafin yanzu na komo jami'a, tafiyar ba mai sauƙi ce ba kamar yadda na karanto haka, akwai jarabowoyi a tsakiya kala daban-daban, wasu har ba ka son ka tuna su, ba ka ƙaunar ka ga wanda ya san su, burin mutum a zuciya kawai ya isa wurin da yake hari, kuma zai isa ɗin amma sai da taimakon Allah (S.W.T), kenan tun farko shi ne mutum zai fara kamawa, in ya amince maka dole a baka, duk abinda za ka yi kar ka manta da mahaliccinka.

A cikin mutane akwai waɗanda suke son ci-gaban, kuma suna ganinsa tare da wani, amma ba sa ƙaunar su motsa, ba sa iya yin tunanin cewa za su zama wani abu nan gaba, wanda yake yankar farce dole ya saka cewa zai zama wani abu yadda nan gaba shi ma za a zo a yanke masa, bunƙasa sana'a dole ne in ba haka ba nan gaba za a rasa mai yi, amma ci-gaba ma wajibi ne, ba yadda za a yi ka ce kaza na gada kansa zan mutu, bai zama dole sai ka canja sana'a ba, amma ka yi tunanin ya za ka bunƙasa shi har mutane birjik su ƙaru da kai?

Ba yadda za ka bunƙasa gadon mahaifinka sai ka yi tunanin kawo na'urorin da za su sauƙaƙa aiki su inganta shi ta yadda za a riƙa yi da yawa, ko a canja salo, duk abinda ka sani a duniyan nan za a iya inganta shi, na san wani yaro da ya taso a gaban mahaifinsa tela, yanzu ya zama babban tela ya kawo manyan kekuna masu yi wa kaya ado, da haka ya mallaki gida na kansa da ma'aikata masu yawa, sana'ar ɗinkin ce dai ba a canja ba, amma an ƙawata ta, an faɗaɗa ta, an inganta ta, wannan ya sa aka ƙara samun dafifin jama'a dake burin ganin an yi musu dinki a shagon.

Duk wani babban mutum da kake gani wanda ya ci nasara a rayuwarsa ta hada-hada, ko cinikayya, ko wani fanni na aiki ko sana'a in zai gaya maka hanyoyin da ya bi don ganin ya cimma burinsa za ka taras sai da ya ci baƙar wahala.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (8) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (9) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (11) Cikin Sauki

Anan akwai abubuwa guda biyu:-

1. Ya sa abin a ransa don ganin ya cimma burinsa, ya yi ta bin hanyoyi daban-daban don ganin hakan ya wakana, ko dai karatu, ko mutanen da yake ganin za su taimake shi, ko bibiyar shawarwarin da za su isar da shi.

2. Aiki tuƙuru kan jiki kan ƙarfi, yin amfani da kuɗi wajen sayen kayan aikin da in ba a samo su ba aikin ba zai yuwu ba.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user