Monday 20 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (8) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
GIRMAMA FAHIMTAR WASU

Muna bayanin sanin irin maganar da za ka yi da abokan cinikayyanka ne ko abokan sana'a da sauransu, wannan kuma kamar yadda ya gabata a baya fanni ne mai matuƙar mahimmanci yadda ba za a iya saka shi a daraja ta biyu ba, ko a littafam mu na shari'a an nuna cewa iya magana don gamsar da mutum ma sihiri ne, don za ka iya tafiya da imaninsa ka sa shi ya amshi abinda bai yi niyya ba, ko ya biya abinda ba shi da shirin yin hakan, wani sa'i sai dai ka ji ana cewa an kwabsa wa mutum, wato an cuce shi ba tare da ya sani ba.

Yin Nazari Kafin yin Komai.. 

Marubuci: Baban Manar Alkasim

Karƙashin iya maganan nan akwai wasu abubuwa kamar haka:-

1. Yarda da kai: Ka gamsar da mai sauraronka yadda zai tabbatar wa zuciyarsa cewa lallai abinda kake faɗin nan haka yake ta wurin yi masa bayani cikin lafuzza masu daɗi, ƙarya a wannan matsayin ba zai taimaka ba, wanda ya fi kowa bin wannan hanyar ta gamsarwa don tallata kayansa shi ne magori, wato mai sayar da magani, koda kuwa maganin bera ne, in mai sayar da magani ya yi talla sai ka rantse da Allah in ka yi amfani da shi za ka warke nan take saboda tsabar iya magana, bokaye ma da daɗin baki suke cutar mata da masu raunin zuciya, mutum ya ce zai yi maka kuɗi, bayan kai ma fa kuɗin za ka ba shi kafin ya yi, tunda shi ke yi wa mutane ya yi wa kansa mana, don me zai karɓe ɗan na hannunka bayan taimako jama'a yake yi? Saboda iya magana dole ka yarda da shi.

Irin wannan tunanin ba zai taɓa zuwa ƙwaƙwalwar mutum a lokacin ba, haka zai ɗibi kuɗin ya miƙa wa wani ƙaton banza ba tare da ya yi tunani ba, an riga an gamsar da shi kuma ya yarda, da yawan masu sana'a hanyar da suke bi kenan wajen gamsar da abokan cinikin su, a ganina babban kuskure ne yin bayani don cuta, don duk wanda ka tsula masa kuɗi zai nuna wa wani ko ya gaya masa kuɗin da ya saya, daga ranar zai ɗauke ka macuci, ba zai sake dawowa ba, ba kuma zai kame bakinsa ba, ya dunga baza wa mutane kenan irin cutar da ka yi masa ƙila daga lokacin duk su ƙaurace maka saboda abinda aka faɗi a kanka, gaya wa mutane gaskiya don tsare gaba, daɗin baki don cutar da su kuskure ne.

2. Masaniya: Dole mai magana kan sana'a ko kayan kasuwanci ya kasance yana da masaniya sosai a kan abinda yake tallatawa, komai iya bayaninsa kuwa, in maras lafiya ya zo wurinka neman magani a ƙarshe ya fahimci ba ka san komai a kai ba ka bar ƙara ganinsa, ko kaya zai saya a wurinka in ya fahimci abinda kake gaya masa ba haka ba ne da ƙyar zai saya, kenan dole ne ka kiyaye abinda kake magana a kai, wasu daga bakinka suke ƙiyasta kyawun abu ko muninsa, an taɓa sanya wani ya yi wa wasu bayanin wata makaranta, gaskiya ya ɗan manta sunan makarantar, nan take masu sauraron sa suka ce a canja shi in ba so ake su yi tafiyarsu ba, don ko sunan makarantar ma bai sani ba, wanne irin bayani zai yi musu gamsasshe su fahimce shi?

3. Rarrabewa: Dole ne mai bayani ya iya rarrabe lafuzzan da suke da kyau da munana, koda kuwa bambancin karin harshe ne, don wasu za su ɗauke ka mai batsa a maimakon su tsaya su saurare ka sosai su ji abinda kake so ka faɗa, in ka ɗauki kifi kana son ka yi bayanin jelarsa, a Kano akan ce wutsiya, in ka ce bindi za su ji wani iri, kamar yadda mutanen Kaduna suke ganin wutsiya batsa ne bindi ya fi dacewa, kai mai bayani ka zaɓi kalmomin da masu sauraronka suke so su ji.

4. Haƙuri: Kai mai sana'a ko ɗan kasuwa ba dole ne kullum ka riƙa jin abinda kake so ba, lokacin da mutum yake gaya maka munanan magana a wurin sana'arka, ko lafuzzan da ba ka son ji, ka haƙura ka saurare shi har ya gama, kar ka yarda yana faɗi kana maimaitawa, shi tafiyarsa zai yi in kun gama, kai kuma wurin naka ne, kayan ma naka ne, bai da asarar komai, in za ka iya ka yi murmushi, in ranka ya ɓaci ka yi masa sai anjima, in haka zai dawo da shi ka yi murmushi kawai ka ƙyale shi, wannan ma zai tura masa haushi sama da a ce ka mayar masa da magana, don gardama ya ke so in ta so ku yi zage-zage, kar ka ba shi damar da zai ci nasara a kanka, yi amfani da ƙarfin zuciyar ka.

5. Girmama fahimtar Wasu: Masu sana'a a kullum sukan yi ƙoƙarin nuna wa abokan hurɗansu cewa sana'arsu tasu ce kuma sun fi kowa sanin kanta, in ka so ka nuna musu irin yadda kake so sai su yi maza su amshe maganar kafin ka ƙarisa, a dole sana'arsu ce ba za ka koya musu ba sun fi ka sanin kanta, abin haushi ma ba dole ne su yi maka bayanin da kai kake ƙoƙarin yi ba, abinda ya dace ka saurari mutum har sai ya kammala abinda yake so ya faɗa sannan kai mai sana'a ka ƙara masa da abinda bai sani ba, ko ka gaya masa yadda abin yake, gardama da abokin sana'a ba taka ba ce kana da abubuwan yi da dama, kar ka bari ku sami sabanin fahimta.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (6) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (7) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (9) Cikin Sauki

6. Karɓar Gyara: Wani sa'i mai sana'a ko ɗan kasuwa ba ya son ka gaya masa aibin kayansa, yana ganin kana son ka kashe masa kasuwa ne, to bare ɗan kasuwan ma, a lokacin da ka dage sai ya fahimci kuskurensa yana iya yin faɗa da kai, maganar gaskiya hakan kuskure ne, kowa yana iyayin kuskure, in ka ji wanda yake son gaya maka aibin kayanka, ko aikinka saurare shi ka yi ƙoƙarin gyarawa, ya fi a ce ya yi maka shuru ya je yana yayata wa jama'a kuma su zo su sami abin kamar yadda ya faɗi, in mutum ya ankarar da kai ka saurare shi ka yi masa godiya, kuma ka yi haƙuri ka bi diddigin maganar da ya yi ka gyara, ba kamai da masa da baƙa ba.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user