Tuesday 14 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (6) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
KYAKKYAWAN TANADI

Wani abu da ya zama dole a rayuwar mutum shi ne samun yanayi mai kyau ga abinda mutum yake buƙatar ya yi, da kuma shigar da ta dace,  suna ɗaya daga cikin abubuwan da suka wajaba ga mutum, duk abinda zai yi ya dubi dacewa da kuma yanayi, ko sana'a za ka fara ka duba inda za ka yi ɗin in mutanen wurin suna da buƙatar kayan da za ka sayar, ba yadda za a yi wanda yake son gina makaranta ko ɗakin watsa labarai ya je kasuwa inda ake hayaniya ga ƙara gami da hargowa ya ce anan zai yi.

Tsari Mai Kyau domin Cimma Buri.. 

MarubuciBaban Manar Alkasim

Wanda zai buɗe maƙerar da zai riƙa ƙera kayan gona to zai fi kyau ya zauna inda manoma za su riƙa ganin abinda yake yi, don wani wucewa kawai zai yi in ya ga abinda yake so zai tsaya ya saya, ko in zai dawo ya riƙo kudi, zan ba da misali ɗaya, wani bawan Allah ya wallafa wani littafi da yake koyarwa game da mutuwa, tun daga rashin lafiya, da yadda ake jinya zuwa fitar rai, wankan gawa, ginin ƙabari da zaman makoki, littafi ne mai matuƙar mahimmanci.

Zai yi kyau musulmi ya mallake shi ya yi nazari don sanin yadda zai suturta waninsa, sai dai ya yi wa littafin suna "MUTUWA" ga gawanan cikin likkafani an ɗora ta a kan anna'ashi, na ce wa mai sayarwan da za ku canja sunan littafin da hoton da aka saka a bangonsa da littafin ya fi shiga, misali a sanya fure a maimakon gawa, sunan kuma a ce "Tafiyar da ba makawa" ya ce ai komai ya yi dai-dai, ko ba a gaya wa mutum ba ya san cewa maganar mutuwa ake yi da abinda ya shafe ta.

A taƙaice dai wallahi littafin nan ƙwara ɗaya sai da ya gama cin dukar rana ya ƙoƙe ba wanda ya saya, kuskuren wajen nuna wa mutane abinda ba sa son gani ne, duk wanda ya kalli bangon littafin zai yi wahala ya yi sha'awar siyan sa, akwai wata yarinya da take tallar abinci, wallahi abincin ta akwai daɗi ga arha, komai kake so akwai, amma yanayin kayan da take sakawa, da wurin da take zama, da nau'in abincin da mutanen wurin suke buƙata ya sa sam-sam ba a sayen abincinta, ga masu abincin nan a wurin ko kusan nata bai kai ba amma suna samun ciniki ba kaɗan ba.

Sun gyara shagon, ga kujeru da teburi, fanka na kaɗawa, a gefe ga firinji, na ci abincin wata sau ɗaya ban ƙara ba, wancan ta farkon da za ta riƙa ragewa a hankali ta kwaikwayi waɗannan, ta tsare daɗin abincinta kar ta canja, tabbas sai ta ƙwace komai, akwai kuma lokacin da aka zo ɗaukar malamai aiki, ana neman malamin Turanci, an sami wani Bayerbe komai ake so yana da shi har da ƙari, amma yana da ƙasumba, ga shi ya zo da jallabiya da wando rabin ƙwabri da takalmi silifas.

Wanan kawai suka kalla suka manta da duk sifofin da yake da su, wai da na tambaye su dalili sai suka ce ba addini zai riƙa koyarwa ba, wannan ya sa ban yi mamaki ba da na ga takardar wata da take neman aiki a wani gidan talabijin ta rubuta cewa ita fara ce kyakkyawa, na tabbata da gidan Radiyo ne ƙila sai ta ƙara da cewa tana da daddaɗar murya, wannan ma abin nema ne, duk abinda za ka yi ka dubi buƙatun jama'a da kuma yadda za su kalle ka.

An yi wani zamani a ƙauyem mu lokacin da fulani suka rabu biyu, akwai masu sayar da nono a kwano da masu sayarwa a kwarya, masu sayarwar a kwano sukan ci ado ka gan su tsab-tsab koda yaushe amma fa suna da tsada, na ƙwaryar ne da arha, na tabbata shigar masu sayarwan a kwanon da yarda da kai da yadda suka ƙawata sana'ar suke ganin abinda ya dace a yi kenan, domin duk da tsadarsu da komai wasu sun fi natsuwa da su, ba su sayen nono sai a wurin su, ko lauyoyi da likitoci gami da manyan ma'aikata ba wani abu ya sa kake ganinsu tsab-tsab ba sai inganta ayyukan su, ana ƙimanta mutum wani sa'in da irin shigar da ya yi ne.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (4) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (5) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (7) Cikin Sauki

Ka lura da kyau ka gani, ko tsayuwa ka yi wurin wanda ya fito tsab za ka ga shi ake girmamawa, na taɓa yin tafiya wani lokaci da mai gidan mu, akwai kuma ma'aikatan mu, cikin su akwai wani Bakatsine da ya sha shakwara da Jamfa, duk inda muka shiga sai ka ga an tsallake mu an fuskance shi, ba wani abu ya fi mu ba illa irin shigar da ya yi, ana ganin shi ne ogan gaba ɗaya, zaben wurin aiki, shigar ma'aikacin, nau'in irin aikin duk abin dubawa ne, mu tara a gaba kan wannan batun.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user