Saturday 11 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (5) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
GUJI YAWAN KAWO HANZARI

Wasu za su iya yin duk abinda ake buƙata, kuma su ɗin ma ya dace a ce sun yi ɗin, amma yawan koke-koke shi zai ruguza su ya ɓata tafiyar gaba ɗaya, wani kana tuntuɓarsa a kan wani abu mai matuƙar mahimmanci a rayuwarsa sai ya ce maka mu yanzu ai mun girma ya za a yi mu iya? Hanzarin dai shi ne yawan shekaru, akwai kuma wanda zai ce gaskiya ba zai iya ba saboda ƙarancin wayewa, ko ilimi, ko kuɗi, ko shekarun, ko dai wani abin na daban, matuƙar mutum ya ce ba zai iya ba saboda wani dalili da ya ambata koda a wurin kowa ba dalili ba ne da shi zai dogara kuma shi ɗin dai zai hana shi cin nasara.

Hanyoyin samun nasara a rayuwa

MarubuciBaban Manar Alkasim

Lokacin da muka shiga JSAIE (Junior Secondary School for Arabic and Islamic Education) ba mu san komai ba, gaskiya ni ko baƙaƙen da Larabci ban iya ba, mun dai yi karatun allo kuma mun sauke, mun haddace wurare da dama amma sunan Nahawu ma lokacin na fara ji, don haka muka nemi wani malami da zai taimaka mana, shi ya koyar da mu littafai da yawa, a dalilinsa muka fara sanin inda aka dosa, mun ga sa'o'inmu a ajin, da ƙannin mu da ma waɗanda suka haife mu ba yayyim mu ba.

Mun yi shekara ɗaya cur tare da malam muna ƙaruwa, tsakani da Allah ba abinda muka sani shi ya riƙa dora mu a kan hanya, a shekara ta biyu ya ce mana shi fa iyakar sa kenan sai dai mu nemo wani malamin, hankalin mu ya yi matuƙar tashi, haka dai muka yi ta bundun-bundun mu faɗa nan mu tashi can, cikin ikon Allah muka shekara shida muka kammala karatun, muka wuce kwalejin share fagen jami'a muka samo kwalin diploma, muka dawo gidan da muka zauna muna tuna baya, cikin ikon Allah a ranar sai ga malamin namu ya yi sallama ya shigo.

Abin mamaki sai ya sami wuri a ƙasa ya zauna ba yan mu muna kan kujeru a zaune, sai ya ce "Wai ya zo neman sani ne". Haka dukkanin mu ukun muka yi ƙasa, ya ce wallahi shi tun daga shekara ta biyu ya rabke ya kasa ci gaba, yana ganin ya girma ga kuma ƙarancin abubuwan masarufi, mu ga shi Allah ya taimake mu har mun kai ga Diploma, tsakani da Allah ba don neman sani ba da ba zai zo ba, saboda haka mu koma kan kujerar mu in ta so in mun ba shi amsa ma sauko ƙasa, muka ce masa wallahi in dai yana ƙasa ba wanda zai hau kujera.

Hanyoyin samun nasara a rayuwa

Da dai ya ga da gaske muke sai ya hau ɗin kuma ya umurce mu da mu hau, da farko mun ƙi, amma da muka ga zai shiga wani hali muka hau, sai bayan mun gama sai ya yi mana nasiha da cewa "Kar mu taɓa samun raunin gwiwa a kan karatu". Da ma duk abinda muka shiga, na san dai yana yin wata sana'ar da tun farko muka san shi da ita, mu kam yanzu muke tasowa amma a ɗalibansa wasu sun  zama marubuta, wasu malaman jami'a wasu manyan 'yan siyasa, wasu 'yan kasuwa da malaman musulunci, a sa'o'inmu ni na san waɗanda suka zama manyan sojoji, 'yan sanda, alƙalai, lauyoyi, malamai a jami'u da sauransu, akwai waɗanda suka koma suna koyarwa a zaurukan gidajen su ana ba su sadakar Laraba.

Wasu tabbas sun sami karayar zuciya ne a dalilin ƙarancin kuɗi, wasu za su ce maka ba sa ganewa, akwai wanda muna karatun ya arce abinsa wai shi aure yake so, ya yi auren amma ya kasa dawowa fagen da yake ciki har abokan tafiyar nasa suka yi masa nisa, sai ya gan su ya yi ta sha'awa, akwai wanda ya ƙi karatun wai za a maida shi ɗan Izala, a dai-dai lokacin mu kammu muna kukan cewa Dariƙar ake koya mana, don littafan tauhidin sam ba sa taimakon 'yan Izalan a aƙidun su, amma duk da haka muka yi haƙuri muka dage har muka gama, kuma ba abinda ya shafi aƙidum mu, shi kuma har yanzu yana nan yau kamar jiya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (3) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (4) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (6) Cikin Sauki

Akwai kuma wani bawan Allah da muka zauna wuri guda, yana HND a ɓangaren kimiyyar noma da tsire-tsire, muna koyarwa wuri guda, ya ba ni shekaru da dama kuma ya fi ni wayewa da sanin kan rayuwa ta ko'ina, a haka na je na yo digirina na farko a waje, na dawo na ba shi shawarar ya canja layi kawai ya dawo ɓangaren koyarwar tunda yana da sha'awa, na yi dace ya manta da shekarunsa da wayewarsa ya koma makarantar, cikin 'yan shekaru ya samo kwalin Digirin shi ma, ya ɗora digiri na biyu, a maganan nan da muke yi shi ke jagorantar wani babban kwaleji.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user