Thursday 9 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (4) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
SAƘAR ZUCI

A wani Hadisi Annabi (S.A.W) ya ce "A cikin jiki akwai wata tsoka in ta gyaru to mutum ya gyaru, in ta ɓaci shi ma ya ɓaci gaba ɗayan sa". A ƙarshe ya nuna cewa zuciya ce, kenan zuciyar nan yadda za ta iya taimakon mutum ya ci nasara a rayuwa za ta iya wargaza shi gaba ɗaya, mun dai sani cewa ita ce za ta taimaka masa wajen gano sabbin abubuwan da za su taimake shi a rayuwar sa, kuma ita ce dai take taskance masa hanyoyin da wasu suka bi kafin a ƙarshe suka isa matakin da suke a yau.

Rayuwa tana buƙatar Nazari..

MarubuciBaban Manar Alkasim

Misali; na ga wani bawan Allah da mahaifinsa ya bar masa gadon miliyoyin kuɗi.

Nan da nan ya sami sabbin abokai, wasu ma ba sa'o'insa ba ne su ma binsa suke yi sau da ƙafa, ya bar gida ma ya koma hotel, sai abinda yake so zai ci, sai wanda yake so zai gani, a irin kuɗin da ya samu ɗin nan zai iya gina irin wannan hotel ɗin a wani wuri, ya zuba duk abinda ke ciki, amma haka ya yi ta kashe musu kuɗin, ogan wurin ma girmama shi yake yi bare sauran ma'aikata, kuɗin da ya samu raguwa suke yi tsakanin abinda zai ci, inda zai kwana, suturar jikin sa, tafiye-tafiyen da yake yi, ɗaukar nauyin masu taka masa baya, da kuma 'yam matan da yake nema, ma'ana kuɗin ba ya ƙaruwa sai raguwa kullum, a ƙarshe dai ya dawo kamar sauran jama'a, shi ma dole ya nema tunda wanda aka taskace an yi masa illa.

Zuciyarsa ba ta taimaka masa da tunani mai kyau ba kokaɗan, saɓanin wanda ya taso maraya ya sami jarin galam ɗin kalanzi ya fara sayarwa, ta kai ga yana ɗaukar jarka, a hankali ya shiga ɗaukar durom, sai ga shi yana da tankuna ma ba tanki ba, a maganannan yana da gidajen mai a ƙarƙashinsa kamar ba shi ne wancan ba, tabbas Allah ya shige masa gaba, sannan zuciyarsa ta riƙa bugawa ga abubuwan da za su yi masa amfani, akwai kansiloli da suka samu kuɗi tun lokacin ba a bincike, wasu sun yi abinda suka ga dama da kuɗin, wasu kuma sun tunano irin halin da suka shiga kafin su taka wannan matsayin, sai suka fara tunanin yadda rayuwar za ta kasance bayan sun sauka don duk daɗewar su ba za su wuce shekaru huɗu ba.

Duk mutumin da ka ga yana taka tsan-tsan wurin kashe kuɗi ko yana cire su kamar yana yankar naman jikin sa, kar ka taɓa tsammanin bai son jin daɗi kamar yadda kake ji ne, tunanin ku ne ya sha bamban, shi yana tuna yadda ya tara su ne, kai kuma kana tuna yadda za ka kashe ne, duk wanda ka ji yana cewa "Kuɗi Allah ke ba da su a kashe su kawai". To ka duba yadda yake kashe su, shin ta yadda Allan yake so ne? In ba haka ba ne ai bai da sakankancewar in sun ƙare za a sake ba shi wasu, Allah (S.W.T) ya yi maganar zakka ne sai sadaka da sauran wuraren ibada, in ba haka ba kuma to da walakin wai goro a miya.

Inganta Tunanin Ƙwaƙwalwa mai Kyau..

Za ka sami mutum yana burin kama sana'a, bai shiga ba amma ya fara tunanin in kuma kayan suka yi kwantai ko aka ƙi siya ya zai yi? Ko yana son ya shiga soja amma kuma ya ce "In aka tura ni Bama ko Sambisa ko Zamfara fa?" Ko zai gina makarantar Furamare a Kaduna ya ce "In kuma EL-Rufa'i ya ci gaba da inganta makarantun gwamnati ai ba zan sami ɗalibai ba, dame zan biya malamai albashin su? Ya za a yi makarantar ta ɗore? Ba wanda zai kawo wannan tunanin zuciyar sa sai ka ga jikin sa ya yi sanyi, in ba a yi sa'a ba komai daganan zai tsaya, ba wani abu ya ja masa ba sai irin tunanin da ya saƙo cikin zuciyar sa kafin ya fara.

Da yawa za ka taras ana son a yi wata harka ta haɗaka amma wasu suna dan jajja da baya, ka ga kamar ba sa so ne, ko kuma wani abu na rashin natsuwa yana musu ƙaiƙayi a zuciya, gaskiya ba komai ne ba sai irin saƙe-saƙen da suke yi a zukatan su na yuwuwar rashin nasarar tafiyar, in sauran abokan za su zama haka to an gama, ba abin alkhairi da za a iya tsinanawa, har a koma zargin juna cewa wane ne ya ja, shi kuma ya fara ƙoƙarin kare kansa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (3) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (4) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (5) Cikin Sauki

Mu ɗauki addinin musulunci a matsayin misali, mahaddata Qur'ani a lokacin su ne sojojin muslunci kuma su ne malamai, su ɗin ne dai suka riƙa fita jihadi, ba su ce in aka kashe su ya za a yi Qur'ani ya zo gare mu ba, haka suka riƙa fita ko a mutu ko a yi rai, Allah ya kalli zuciyar su ya ba su kariya ga shi muna amfani da ƙoƙarin su, haka a yau mutum zai narka miliyoyin kuɗi ya gina makaranta, ko kamfani ko wata ma'aikata, ba tare da ya yi tunanin in kuma bai dawo da kufin ba fa? A koda yaushe yana tunanin cin nasara ne, tabbas zai ci ɗin da izinin Allah, kowa da ka gani a cikim mu ya san da cin nasara ko faɗuwa, amma masu cin nasarar kau da kansu suke yi ba sa tunanin faduwar kokaɗan.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user