Monday 6 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (3) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
KAR KA BAR JAKI KA KOMA DUKAR TAIKI

Wato dai kar mutumin da yake haƙilon cin nasara a rayuwarsa ya bar abinda ya dace a ce ya yi ya koma wanda bai da alaƙa da abinda yake nema kuma ya nace, ba yadda za a yi mai son zuwa Gabas ya kama hanyar Yamma kuma ya zaci inda yake so zai je, mun ɗan yi tsokaci a kan wannan a baya, Allah ne ke ba da arziƙi kuma bai ɓoye hanyar da za a bi don isa gare shi ba, duk masu kuɗin nan da kake gani ba roƙon Allah suka yi da suka buɗe ɗaki suka sami kuɗin a zube ba, ka tambayi kowa a cikin su in zai gaya maka yadda ya tara su za ka taras ya ci baƙar wahala kafin ya kai matakin da yake a yau.

Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

MarubuciBaban Manar Alkasim

Na san shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi shugabanci ba ɗaya ba ba biyu ba ana liƙa shi da ƙasa, amma da yake yana da abin a zuciyar sa ƙarshe Allah ya taimake shi ya kai ga manufarsa, muna da manyan malamai a ƙasar nan, in ka sami wani a cikin su ka tambaye shi yadda aka yi ya kai ga matakin da yake a yanzu, za ka taras wasu matsaloli ne ya tsallake waɗanda ba sa ƙirguwa, wasu tabbas ya yi dariya a ƙarshe, wasu kuma ya yi kuka da hawayen sa, ba wani ɗan adam ɗin da ya kai ga cin nasara ba tare da ya ji jiki ba, Bahaushe ya daɗe da sanin wannan, shi ne ma ya sa ya ce wai Allah ya ce "Tashi na taimake ka!" Na san ba maganar Allah ba ce amma manufar a wurin Bahaushe a fili take.

YARDA DA KAI

Ƙa'idar kamar yadda muka gani a baya ita ce: Duk wanda ya sanya wa zuciyarsa ba zai iya yin abinda yake so ba to ba fa zai iya ɗin ba, rashin yarda da kai matsala ne mai zaman kansa, ko na ce cuta ne dake damun mutane da dama, kuma shi ke hana su isa ga burin su, amincewa da kai wani abu ne dake tasowa daga cikin mutum, ƙwaƙwalwa, zuciya da ma gangar jiki gaba ɗaya, duk su suke taimakawa wurin ganin mutum ya ci nasara a rayuwarsa, mu ɗauki masu wasan dambe a matsayin misali, kalli dai yadda kowa yake dagewa sai ya yi nasara ta wurin rinjayen abokin faɗansa, a ƙarshe mai rabo ya ɗauka, amma akan ji jiki.

Ba a Samun Nasara Haka Kawai.. 

In Allah ya taimake ka kana burin sai ka ci nasara, ka tsaya wurin yin aikin da ya kamata, ka inganta aikin kuma, ba shakka ka taka matakin farko na cin nasara a rayuwa, saɓanin kallon abinda za a samu a maimakon ingancin aikin, ko kallon yawan mabuƙatan aikin a maimakon masu yabon ingancin nasa, in ka raina abinda kake samu tun farko ƙila ka gaya wa zuciyar ka cewa ba za ka iya ba, matakin farko kenan kuwa na karayar zuciya, wato rashin samun ƙarfin gwiwa, sai abin ya fara fita daga ranka kaɗan-kaɗan sai ma ka bar shi gaba ɗaya, a duk lokacin da ka bar abu don ka raina shi wani zai ɗauka ya ririta shi, in ba ka yi sa'a ba sai ka koma yi masa aiki yana biyan ka.

KWATANCIN BURI DA ISA GARE SHI

Wannan labarin wani mutum ne da ya girma a gaban kakarsa saboda mahaifinsa ya rasu tun yana jariri, da yake uban mai kuɗin ƙauye ne yaron sa ya yi ta amfani da gadon da aka bar masa ta wurin biyan kuɗin makaranta na karatun da ba a maida hankali ba, ko kuma yanayin karatun ƙauye, yadda yaro bai samun tagomashi a gida, makarantar ma ba sa ba da abinda ya dace, haka har ya gama sakandare ba tare da ya san abinda yake yi ba.

Ganin haka da ya girma ya sake maimaita sakandare da kuɗin sa, tunda a lokacin ya mallaki hankalinsa, inda ya fara ƙwadago wato noma a gonakin jama'a yana samun na makaranta, wani sa'in kuma ya koma wanki da guga, musamman idan rani ya yi, yana kammala sakandare na 2 ya wuce kwalejin share fagen jami'a ya yi shekara 2 da kwalin Diploma, Allah ya taimaka ya sami karatu a waje, tun daga can ya fara aiki a fagen da jama'a za su san shi, a taƙaice maganannan tamu malami ne a ɗayan jami'o'in nan na Nigeria.

Juriya da Jajircewa... 

Binciken da na yi shi ne, burin mutumin nan tun yana yaro shi ne karatu, babban dalilin da ya sa yaƙi yin auren ƙauye kenan da wuri kamar yadda sauran abokai suka yi, burin sa shi ne a ce yau ya zama malami yana koyarwa, an ce tun yana ƙarami yake da burin koyarwar a makarantu da ɗai-ɗai kun mutane har Allah ya kai shi wannan matsayin, kuma a yanzu haka wai yana so ne a ce yana da makaranta tasa ta kansa wacce yake jagoranci, a tarihin sa bai taɓa nisa da burin sa na zama malami ba, duk mutanen da ya san su a fagen suka haɗu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (2) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (3) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (4) Cikin Sauki

Iya bincike na game da shi bai da wata gata ko ƙwara ɗaya wacce za ta sa ya kai matsayin da yake a yau, hatta aikin da yake yi a yanzu, ya sami taimakon Allah ne kawai, sannan jajircewar sa da ƙoƙarin kaiwa ga wannan matsayin shi ma ya taimaka, shi ya sa makarantu ke sanya wa yara rigunan lauyoyi, injiniyoyi, sojoji, likitoci da ƙarfafa musu gwiwar cewa za su kai ga cimma burin su, na san wanda duk maganarsa soja yake so, kuma a yanzu haka Captain ne ma, wani ɗan sanda yake so, shi ma an ce DPO ne, amma fa sun tsaya ne sosai kafin Allah (S.W.T) ya kai su ga cin nasara.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user