Saturday 4 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (2) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
Maganar Gaskiya Ita Ce....

Tsananin son mutum ga kaiwa ga nasara ke sanya shi ya fara aiki don kaiwa ga gaci, wanda yake son ya zama soja zai fara kallon sojoji da ganin yadda suke fareti yana riƙe sanda a matsayin bindiga, yana son jin duk abinda yake da alaƙa da su, ya fara tambayar hanyoyin da zai bi, har wani ya ba shi shawara, da haka sai ya isa inda yake so, Allah (S.W.T) bai zubo da sulalla daga sama, sai dai ya yi bayanin hanyoyin da za a bi a samo su.

Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

MarubuciBaban Manar Alkasim

Wanda ya tsaya a kan dugadugan yakan bi manufarsa, kuma yakan isa gare ta ta wurin addu'a, sai kuma jajurcewa har dai Allah ya yi masa albarka a ciki, wannan kawai ya isa komai, a wannan shiri za mu yi qoqari wurin binciko wasu hanyoyi na cin nasara da Allah SW ya shar'anta, da wasu abubuwa wadanda tabbas sun faru ga wadanda suka yi nasara a rayuwarsu, ita nasarar kalma daya ce, kuma abu guda ce, sai dai kowa da hanyar da yake bi don ganin ya kai gare ta, kuma akan yi dace din, domin na ga wani hanshaqin mai kudi da aka ce da wanki da guga ya fara.

Na ga wani ɗan kasuwa da shago sama da ɗaya kowanne maƙare da kaya, ga kuɗi ga kyakkyawar mata, kuma aka ce ya baro gida almajirci ne a ƙarshe ya faɗa wata hanyar har ya zama haka, na haɗu da wani babban malami kuma babban ɗan sanda, muna tattaunawa yake ce min "Shi daga karatun allo ne da yake sun haddace Qur'ani aka ɗauke shi a makarantar sakandare ta Larabci". Sai ga shi har ƙasar waje ya fita ya dawo ya shiga aikin ɗan sanda ya kai wannan matsayin, na ga wani daga gini har ya mallaki gidansa na kansa ya zo ya fara yi wa wasu hanyar samun haya, har ta kai ga shi ma yana da gidaje barkatai.

DA FARKO ME KAKE SO?

Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

Dole sai ka san abinda kake so sannan ka cimmasa a rayuwa, ka zama malami, likita, jami'in tsaro, lauya, babban ɗan kasuwa, mai sarauta ko ma'aikacin gwamnati? I to za a iya samun bambanci saboda yanayin bambancin mutane da abinda suke so, ko bambancin al'ada, da ma mataki na ilimi, sai dai a ƙarshe kowa za ka taras yana da abinda yake so ya cimmasa, akwai wanda za ka ga ko addu'a yake yi ba ya nufin a ba shi abinda ya roƙa, shi ya ambaci wani abu ne amma yana nufin a ba shi abinda ba shi ya roƙa ba.

Misali: Mun yi wani limami da kullum muka zo sallah sai ya roƙi Allah ya sauko mana kaɓukka na abinci kala daban-daban daga sama, tun muna yara yake addu'ar har muka girma muka san ma'anar addu'ar muka tambaye shi "Amma kai baba a yadda kake zaune haka ka ga abinci na saukowa daga sama za ka tsaya?" Ya ce ai ba abincin yake nufi ba arziƙi ne, to ko arziƙin ne Allah ba ya zubo kuɗi haka kawai, tabbas akwai arziƙi kuma ba mai iya yi wa mutum sai Allah, hurumi ne daza a roƙe shi, amma ba ka naɗe hannu Allah ya zubo maka daga sama ba.

Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

Kowa ya ƙudurta a zuciyarsa cewa yana son ya sami kaza, ko ya zama kaza, ko ya isa zuwa wuri kaza, amma kar ya yarda ya sami abubuwa barkatai da za su cunkushe masa ya kasa tabbatar da abu guda da zai fara nema, in dai kana da abinda kake so wanda za ka fara aiki dominsa to roƙi Allah sai ka fara, zan ba da misali, wata 'yar uwata ce ta kusa matuƙa, maraici ya gigitata ko kuma yanayin wurin da ta taso ba wuri ne da zai taimake ta ta cika burinta na zama ma'aikaciyar jinya ba.

Kuma abinda take so kenan a rayuwarta, har ta ce in ba ta yi ba in sha Allah 'yarta za ta yi, ba ta da takarda sai ta Furamare, koda yake ta fara sakandare sai dai ta tuƙe, haka ta yi aure, mijin da yake irin ustazannan ne ya kai ta makarantar Islamiya, ta gama ta shiga sakandare ta Islamiya, Larabci ta iya, sai aka kawo wani shiri ƙarƙashi jama'atu na ba da taimakon farko, ai kuwa ta shiga ta yi wata shida suka yi jarabawa aka tura ta asibiti don sanin makamar aiki, jajurcewarta da iya aikin ya sa asibintin suka yarda da aikinta har suka dauke ta gwargwadon addu'arta da samun natsuwa da hukuncin Allah (S.W.T).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (1) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (2) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (3) Cikin Sauki

Amma mutum ya ƙi karatu ya nade hannu ya ce likita yake so ya zama, ko yana karatun kimiyya ne amma lauya yake so ya zama, ko ka iske wanda yake son ya zama madogara cikin manazarta a harshen Larabci amma baida littafan Larabcin, bai da ɗaliban, a ɗakinsa akwai littafai sama da 500 amma duk na addini ne, kuma ya ƙi natsuwa ya karanci addinin, kullum shi ne a masallatai da makarantun koyar da addini da wahala ka ga ya isa inda yake so sai dai kame-kame, na san wanda tun muna sakandare yake da digirin farko ga shi na kawo inda nake a yau har yanzu bai ƙara ko taƙi ɗaya ba kuma yana fagen.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user