Wednesday 1 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (1) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
MECE CE NASARA?

In aka ce nasara ana nufin isa ga biyan buƙata, ko samun abinda ake so, in mutum ya ci nasara to ya iya rinjayar ƙalubalen dake gabansa kenan, kalmar nasara ba ta zuwa ba tare da mutum ya tsallake wani tarnaƙi dake gabansa ba.

Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

MarubuciBaban Manar Alkasim

Kenan maganar da Bahaushe yake cewa "Kowa ya ci zomo ya ci gudu." ta zama gaskiya, wani malamim mu Ustaz Ya'qub yake cewa ba abinda ake samunsa a ɓagas, in ka ga mutum ya ba ka abu ba tare da neman wani abu ba, kar ka yi zaton ahaha ne ka ci baki bude, ka jira abinda zai biyo baya.

In ka ba Bature kyauta zai karɓa ya ajiye sannan ya tambaye ka "Me kake so na yi maka?" Hatta almajirai masu bara ba a jefa musu kuɗi haka arha, sai sun yi busa ko rawa da za su ja hankalin mutane, sannan a biya su, kenan samun nasara a rayuwa in muka dubi abubuwan da suka gabata za mu fahimci cewa yana nufin bayyanar mutum ne a kan abinda yake haƙilo tuntuni, kamar mallakar gida na kai, yin tafiye-tafiye, ko samun sabbin abubuwa na more rayuwa, kodai mutum ya ga ya wayi gari kuma ga kuɗi a banki bai da buƙatar sai ya fita kafin ya sami na rufin asiri.

Ko ya kasance yaransa suna karatu a manyan makarantun da ake buƙata, ko kuma a ce kowa na sha'awarsa yana fatan ya zama kamarsa, ko samun wani shugabanci na gwamnati ko na al'umma, ko ya riƙa ganin dandazon mutane suna zuwa wurin wata sana'a da ya fara, koda kuwa ƙarama ce wace ba ta taka kara ta karya ba, idan ya kalli jama'ar kuma ya ga don wannan abinda ya yi ne lallai zai san cewa ya ci nasara a ruwarsa.

Bai tsayanan ba, mutum ya rabu da damuwa ma wani abu ne, to bare a ce ba ya tsoron wani abinda zai bijiro masa a rayuwa, kamar a ce ma'aikacin gwamnati ne amma yana da wata sana'a a gefe da take yi masa komai, in yau ya rabu da aikin gwamnatin ba abinda zai dame shi, shi kansa zai ga mutane na girmama shi, in ya yi magana ana sauraronsa ba don ya fi sauran 'yan unguwar ilimi ko girman shekaru ba tabbas wannan ma zai iya zama cin nasara a rayuwarsa.

Babban abinda ke damun mutane a yau shi ne rashin tabbacin wurin aiki, ma'ana kullum mutum yana ƙoƙari ne ya kawo abinda zai tabbatar da shi a inda yake aiki, yana kuma tsoron abinda zai yi ya zama sanadiyyar da za a ce ya kama gabansa, to in ya sami nasa duk tsoronsa ya ƙare, bare kuma a ce zai iya daukar nauyin wasu mutane wadanda a ƙarƙashinsa suke, abincinsu na samuwa ne daga wani abu da ya ƙirƙira, kodai su ɗauka su je su sayar, ko kuma su taimake shi aiki, ya yanka musu albashi, wannan duk ci gaba ne ( Takbeerut Tafkeer na David p9).

Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

NASARA CE ASALIN JIN DAƊI

Da yawanmu ba su fahimtar nasara da irin wannan bayanin da muka yi domin tunaninsu kawai abinda za su ci ko su rufa asiransu su da iyalinsu, wani ma zai ce maka "In ka sami abida za ka ci ka sha ka yi zumunci ya ishe ka" ma'ana mutum bai da wani abu a rayuwa sai dai wannan, ya manta cewa maganar zumuncin da kuɗi ake yi, sannan zai yi tattalin abinda yake da shi a yanzu, ta yadda za a same shi a kullum, ko a ƙara yawansa tunda ana haihuwa iyali na ƙaruwa.

Da irin wannan ne za ka ga mutum ya rayu kullum cikin tsoron rasa abinda yake hannunsa na kuɗi ko na aiki ko muƙami, kullum hankalinsa yana kan dan kadan din da yake hannunsa, a zahiri duk wanda ya saka a ransa cewa ba zai iya zama wani abu ba da wahala ka ga ya zama din, don ba zai taba yin abinda zai kai shi wurin ba, ko mace da take ganin ita wata ce kar ka zaci tana da abinda wata ba ta da shi ne, ta ɗauki kanta ne ta kai wani matsayi shi ya sa take jin tabbas tana matsayin.

Mutum ya tabbatar wa kansa cewa tabbas zai iya yin kaza, shi zai sa ya fara laluben hanyoyin da zai cimma burinsa, to ko bai sami abinda yake so duka ba za ka ga ya sami wani abin, misali saurayin da yake ganin zai iya riƙe mata, sai ya yi aure har wanda ya fi shi albashi ya riƙa cin abinci a gidansa, abokin ya kasa saboda tsoro ya koma kuma yana cin abincin wanda ko kusa bai kai shi ba, irin wannan tsoron shi ne yake damun mafi yawan matasa, ko wani abu na kansu ba sa iyawa sai zaman banza ko na kashe wando ya yawaita.

Za mu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user