Wednesday 1 January 2020

Shin Zan iya Sanin Hakikanin Masoyi na ta Hanyar yi Min Dariya ko Murmushi?

Tura Wannan Zuwa
Idan da ace zaka iya jin abinda wasu suke faɗi a bayan idon ka dangane da Kai, to da wasu ma idan kun haɗu da su ko gaisuwa da kallon mutunci ba zakayi musu ba.

Sanin Mutum Sai Allah Dariya ba So ba Ce

Marubuci: Idris M. Rismawy

Ba kowacce dariya ce da wasu zasuyi maka take zama dariyar soyayya gare ka ba, wasu kam iya karta fuska, amma abinda suka ɓoye na nuna maka ƙiyayya cikin zuciyar su shine yafi girma.

Ba lallaine sai ka mallake zukatan dukkanin mutane ba, koda kuwa ka yunƙura ba lallaine ka iya ba, idan kuwa kace sai ka da ge ka yi, to lallai kam baku da bambanci da Mahaukaci.

Kai dai kawai katurawa kowa aniyarsa, Ka mu'umilanci mutane da kyawawan halayyar da Musulunci ya tarbiyyantar dakai akai.

Kada ka mu'amilancesu da irin munanan Halayyarsu, sai a rasa gane wane ne ba wane ne ba,  domin idan Kare yana maka haushi, kaima idan ka mayar masa da haushin sai arasa gane wane ne ba Kare ba a cikin ku.

Idan an munana maka kai kuma sai ka kyautata musu, idan sun baƙanta maka, sai kai kuma ka faranta musu, idan sun zalunceka sai kai kuma kayi musu Adalci.

MAKALOLI MASU ALAKA:

CIKIN WADANNAN MUTANE WANNE IRIN ABOKI NE DA KAI ?

Shin Zan Iya Zama Sanadin Shiriyar Abokina?

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa Cikin Sauki

Amma kuma karka sake kazubar da mutuncin ka a kokarinka na kyautatawa wani, ko wajan neman yardar wani ba Allah ba.

Ya Allah ka ƙara mana Imani da tabbata akan IMANIN, Ka yayewa zukatan mu hassada da ƙyashin 'yan uwan mu kuma kasa mudace duniya da lahira Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user