Tuesday 10 December 2019

CIKIN WADANNAN MUTANE WANNE IRIN ABOKI NE DA KAI ?

Tura Wannan Zuwa Ga
Dan adam a rayuwar sa yakan yi abokai da masoya iri-iri, haka kuma zai iya samun Makiya nau'i  daban-daban.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai...

Marubuci: Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa

1. Akwai wanda zai yi da'awar Shi Masoyinka ne, amma ba zai tashi Matsowa jikinka ko kuma nuna maka soyayya ba, sai lokacin da yaga wata nasara ko ni'ima ta samu gareka.

Amma da zaran ka samu matsala a rayuwa ba zaka sake ganin sa a kusa da kai ba.

2. Akwai wanda yana nan tare da kai ko yaushe, amma duk abinda kasa a gaba sai ya tayaka kuyi. Ba ya yi maka musu, ko gyara a cikin lamarinka ko da ya ganka akan kuskure haka zai tayaka kuyi.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

To wannan masoyi ne amma yana da rauni, kayi hattara dashi don zai jefa ka in da ba zaka iya fita ba a duniya da lahira.

3. Akwai wanda yana tare da kai ko yaushe amma idan yaga abin alkhairi tare dakai sai ya binne labarin. Idan kuma yaga mummunan abu tare dakai sai ya watsa ma duniya. Ta wajensa ake samun Miyagun labarai game dakai.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

Wannan Makiri ne, Mahassadi ne. Ka nisanceshi.

4. Akwai masoyin da ko yaushe yana tare da kai a zuciyarsa haka a fili. Duk lokacin da ya ganka akan alkhairi sai yaji dadi har ya taimakeka kuyi. Idan kuma ya ganka akan kuskure Sai ya gyara maka Koda ranka bayaso. Wannan shine masoyi na gaskiya.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

Ka riƙeshi da kyau domin Irinsa suna da wahalar samu.

'Yan uwa mu sani a ranar alƙiyamah abokai zasu zamo suna gudun gamuwa da junan su saboda tsoron hisabi kan haƙƙin jikan su.

Haƙiƙa akwai abokai masu alaƙa don kwaɗayi da son abin duniya masu halakarwa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Shin Zan Iya Zama Sanadin Shiriyar Abokina?

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

KARANTA ABU BIYU NE KAWAI ZAKA IYA YI IDAN KA HADU DA WANDA YAFI KARFIN KA

Kuma akwai abokai na kwarai masu alaƙa don Allah.

Kuma sune masu samun shiga inuwar al'arshin Allah, waɗanda suka gina kauna da abotarsu bisa gaskiya da riƙon amanar juna sune zasu rabauta.

Cikin Waɗannan Abokai Wanne iri ne da Kai..

Kuma su zama Sanadiyyar Samun rahama ga junansu.

Allah ka bamu dacewa duniya da lahira ka haɗamu da abokai na kwarai, amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user