Monday 6 January 2020

Karanta Wasiyyar Wani Uba Mai Hikima Ga Dan Sa a Zamanin Internet

Tura Wannan Zuwa Ga
Wannan wasiyya ta cancanci a rubuta ta da zallan ruwan zinari.

 A cikin wasiyyar yana cewa a cikin ta "Lallai Google da Facebook da Twitter da Whatsapp da dukkan tsare-tsare (Platforms) ɗin sadarwa, rafine mai zurfi, halayen mazaje sun ɓace a cikin sa."

Wasiyyar Wani Uba ga Ɗan Sa..

Marubuci: Bashir Abdullahi

Hankula sun gushe a cikin sa, cikin su akwai matasa da masu furfura, igiyarsa ta tafiyar da kunyar 'yam mata.

Cikin sa akwai, jama'a dadama sun halaka a cikin sa.

Ka kiyayi yawo a cikinsa, kazama tamkar ƙudan zuma a cikin sa, kada ka tsaya a shafi sai mai kyau, domin ka soma amfanar kanka dashi sannan ka amfani wasu.

Yakai ɗana, kada ka zama kamar ƙuda, wanda ke tsayawa akan komai, mai kyau da mara kyau, sai ya ɗauki cuta ba tare da ya sani ba.

Ya kai ɗana, lallai Internet kasuwace mai girma, babu wanda ke bada kayansa kyauta, kowa nason wani abu kafin ya bada kayansa.

A cikin su akwai wanda keson ɓata halaye amadadin kayansa!

A cikin su akwai wanda ke fitar da fikira rikitacciya, cikin su akwai mai neman shahara, a cikin su akwai na kwarai, don haka kada ka siya kaya har sai ka bincika sosai.

Yakai ɗana, ina kashedin ka da kwance ƙulle-ƙulle, domin wasun su tarkone da dabara, kuma sharri ne mai girma, makircine da rusawa.

Ina kashedin Ka da yaɗa labaran bandariya (Jokes) da munanan abubuwa, ka kiyayi Copy and Paste na haramtattun abubuwa, kuma kasani waɗannan abubuwa ana  maka kasuwanci dasu cikin kyawawa ko munanan ayyuka, ka zaɓi abin siyarwar ka kafin fitar dashi kasuwa, domin ba'a shawara da mai sayen kaya.

Ya kai ɗana, kafin kayi comment ko joining, kayi tunanin ko hakan yana yardar da Allah ko yana fusata shi.

Yakai ɗana, kada ka dogara da abotar wanda idanun ka basu ganshi ba.

Kada kai hukunci ga mutane ta hanyar abinda suke rubutawa, domin su masu makirci ne, fuskokinsu masu sassauyawa ne, hankulansu dunƙulallu ne, maganganunsu masu daɗi ne, suna ƙarya da gaskiya, na wane mutane masu addini (a zahiri) amma sune manyan wawaye! Nawane kyakkyawa amma shine mafi munin munana, nawane mai kyauta amma shine mafi rowan marowata, na wane jarumi amma shine mafi tsoron matsorata?? Sai dai wanda Allah yawa rahmah, na wane Allah yawa Rahmah???

Ya kai ɗana, ka guji sunayen aro, domin ma'abotansu basu yarda dasu aran su, kada ka aminta da wanda bai aminta da kai ba cikin ransa.

Na haneka da aron suna, domin Allah yasan abindake fili da na ɓoye.

Yakai ɗana, kada ka soki wanda ya soke ka, domin kai kana nuna kankane shima yana nuna kansa, kai kana wakiltan halayen ka ne ba halayen sa ba, kowace kwarya da ruwanta take ado.

Yakai ɗana,  ka kyautata abinda kake rubutawa, domin kana rubutu ne mala'iku na rubutawa, Allah (S.W.T) na saman kowa yana hisabi kuma yana bibiya.

Yakai ɗana, lallai mafi tsoron abinda nake jiye maka tsoro a rafin Internet mai ban tsoro shine kallon haram, da abokantakar mutan banza da kaucewa hanya, in kasamu kanka cikin wannan najasa, ka amfani kanka da sadarwa da Al'ummar ka, ka bada himma wajen yaɗa addinin ka, in kasamu kanka luntsume cikin haramun, ka gudu daga duniyar internet kamar yadda zaka gudu in kaga kura, domin wuta zata zama makomar ka Ubangijin ka ya zamo abokin khusumarka.

Ya kai ɗana, mafi muhimmancin mashigar shaiɗan itace sakankancewa da sha'awa, kuma sune ginshiƙan internet.

MAKALOLI MASU ALAKA:

ALLAHU AKBAR: TAYI NASIHA MAI RATSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI JIM KADAN TA RASU

KARANTA KADAN DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'UMMA GABA DAYA CIKIN GAGGAWA

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

Ka sani wannan abu ba'a halicce shi don sakankantar dakai ba sai dai don amfaninka, don haka kai amfani dashi kada shi yayi amfani dakai, kayi gini dashi kada kasashi ya rusaka, kasanyashi hujja gare ka ba akanka ba.

Muna roƙon Allah, Shiriya da dacewa, ya kuma kare mu daga sharrikan zukatan Mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user