Tuesday 14 January 2020

Shin Ko Kasan Zagin Shuwagabanni da Malaman Addini tamkar zubar da jini Ne ?

Tura Wannan Zuwa
Sheikh Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, yayi kira ga musulmai da su guji zagi da cin mutuncin 'yan uwansu musulmai da shuwagabanni musamman a kafafen sadarwa.

Shin Ko Kasan Zagin Shuwagabanni da Malaman Addini tamkar zubar da jini Ne...

Malam ya fara da cewa:
“Wannan lamari yana ba ni tsoro…!"

Yau an wayi gari mutuncin Mutane ya zama abin banza. Kowa bai wuce a keta masa mutunci a ci zarafinsa a fito a zazzage shi a bainar jama’a ba.

Musamman a waɗannan kafafe na sada zumunta Facebook, Tweeter, Instagram da makamantansu.

A yau babu wani shugaba da yake da kwarjini da ake jin tsoron zaginsa.

Babu wani Sarki da yake da martabar da za ta sa a kiyaye matsayinsa.

Babu wani Malami da yake da alfarmar da za ta sa a kiyaye darajarsa.

Babu wani shugaban al’umma da yake da matsayin da zai sa a kare masa mutuncinsa.

Cin mutuncin Musulmi da Zubar da kimarsa dai-dai yake da zubar da jininsa.

A yau kowa ya fito yana ta kururuwa a kan zubar da jinane da suke faruwa a sasssa daban-daban na ƙasar mu, amma a lokacin da yake wannan kururuwa, a lokacin ne yake cin mutunci da zubar da ƙimar Musulmi.

A bisa haƙiƙa, kai da kake cin mutuncin Musulmi a Facebook, dai-dai kake da wanda yake zubar da jini a Jihar Zamfara.

Annabi (saw) a ranar Hajjin ban kwana ya ce:

«فإن دماءكم وأموالكم وأعراضكم عليكم حرام، كحرمة يومكم هذا، في بلدكم هذا، في شهركم هذا»
صحيح البخاري (2/ 176) صحيح مسلم (3/ 1306)

“Lallai jinanen ku, da dukiyoyin ku, da MUTUNCINKU, HARAMUN NE A KANKU, kamar haramcin wannar ranar taku, a wannan gari naku (Makka), a wannan wata naku”.

Imamu Nawawiy ya ce:

معناه متأكدة التحريم شديدته، وفي هذا دليل لضرب الأمثال وإلحاق النظير بالنظير قياسا
شرح النووي على مسلم (8/ 182)

A wani Hadisin kuma:

«بحسب امرئ من الشر أن يحقر أخاه المسلم، كل المسلم على المسلم حرام، دمه، وماله، وعرضه»
صحيح مسلم (4/ 1986)

“Ya ishi mutum samun sharri ya WULAKANTA ƊAN UWAN SA MUSULMI, kowanne Musulmi haramun ne a kansa ya zubar da jinin Musulmi, ko ya ci dukiyarsa, ko ya ci mutuncinsa”.

Malamai suka ce: Mutunci shi ne muhallin yabo ko zargin mutum, sawa’un a kansa ko a danginsa.

Haba Jama’a, wannan fa Musulmi kawai aka ce, ina kuma ga Jagororin Musulmai?

1. Shugabannin Gwamnati.
2. Sarakunan Musulmai.
3. Malaman Addini.
4. Shugabannin Al’umma.

Rashin Tarbiyya ne da rashin riƙo da Addini ka mayar da dandalin Facebook da ire-irensa ya zama dandalin cin mutuncin Ɗan uwanka Musulmi, balle kuma shugabanni a cikin su.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

Karanta Wasiyyar Wani Uba Mai Hikima Ga Dan Sa a Zamanin Internet

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (1) Cikin Sauki

Shin al’ummar nan za ta ɗore kuwa, idan aka ci mutuncin kowa, aka rasa mutunta shugabanni?!

Yanzu kenan zamu wayi gari babu mai mutuncin faɗa aji kenan a cikin mu?!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user