Friday 17 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (7) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
KA SAN ME ZAI FITA BAKINKA

Abinda babu kokwanto a cikinsa shi ne duk wani mutum a gidansa sarki ne, kowaye kuwa, zan ba ka dan misali a kaina, a matsayina na malamin makaranta, na koyar da wani ɗan sanda, to halin rayuwa sai na sami matsala na katin gidan talabijin wanda wani mutum ya zurma ni ciki, ina zaune aka ce ana gayyata ta a State CID, na tafi, sai na iske wannan mutumin da na sami matsala da shi, aka yi min wasu 'yan tambayoyi na fara ƙoƙarin yin bayani, nan take wani ya daka min tsawa wai na daina ɗaga masa murya, a lokacin na san ogansa ɗalibina ne, in ya zo wurina ka ga yadda yake maƙe-maƙen murya, to kowa a gidan sa sarki ne.

Ka koyi yadda zakai Mu'amala da Mutane...

MarubuciBaban Manar Alkasim

Duk da cewa kowa ka gani a gidansa sarki ne zai yi kyau mu koyi yadda za mu yi magana da abokan hurɗan mu, duk wanda yake da kayan sayarwa so yake ya ƙare, zai yi wahala hakan ta faru sai ya kusanto da abokan hurɗarsa, wanda yake buƙatar taruwar jama'a to ya ririta su yadda ba za su watse ba, na taɓa ganin wani mai sana'a da yake ce wa mai sayen "Kar Allah ya sa ka saya mana! In ka tafi dubunka za su saya kuma zai ƙare" ban san me ya hada su ba amma na tabbata wannan mutumin ba zai sake sayen kayansa ba, ba kuma zai bar wani nasa ya saya ba.

Iya magana da abokin ciniki ko abokan aiki fanni ne mai zaman kansa da ya dace duk mai hurɗa da jama'a ya koya, ana cewa "Shimfiɗar fuska ta fi shimfiɗar tabarma" wani ba magana mai daɗi ba har murmushi zai yi maka, don dai ka sami natsuwa da shi, koda kuwa ka gaya masa maganar da bai ji daɗinta ba, na ji an ce wa wani mai nama "Kamar da ƙura a kai!" Sai ya ce "A kansa aka yi yaƙin Badar, fuskan nan a murtuƙe ba alamar dariya" in zan kawo irin waɗannan misalan suna da yawa, don wata mata da take waina mutane suna son abincinta amma da masifarta take korar su.

Wani Rashin Iya Mu'amala da Mutane Shine Matsalar Sa.. 

Wani a makaranta yake aiki sai wani ya kawo dansa yake tambaya ko gwamnati ta amince da makarantar, da buɗe bakinsa sai ya ce "Ranka ya daɗe in ba za ka iya ba ka tafi wani wurin mana, wannan wacce irin tambaya ce haka, gwamnati ba ta yarda da mu ba kawai haka sai mu zo mu buɗe makaranta?" Haka mutumin ya ce "Allah ya ba ka haƙuri" ya ja yaronsa ya tafi, sai mutumin ya ci gaba da cewa "Irin waɗannan asali ba yaran suka kawo ba, neman magana da tunzura mutane suke yi" bayan shi ya kore shi.

Tabbas wasu rashin iya magana ne da mutane, wasu kuma rashin gwanancewa ne wurin hurɗa da jama'a, wasu tsabar wauta ce da rashin sanin ƙimar mutane, akwai kuma masu ƙarancin hangen nesa, sai dai ko ya mutum yake, iya magana wajibi ne matuƙar za ka yi hurɗa da jama'a, in ba haka ba sai a guje ka a bar ka kai kaɗai, in sana'a ce ka ga tana baya-baya ka rasa gane dalili, ai kai ne babban dalilin, in ma sarauta ce ka kasa iya bakinka sai yawan maganganu a kan abinda ya shafe ka da wanda bai shafe ka ba dole ka sami matsala, Annabi (S.A.W) ya riga ya ba mu mafita "Mutum ya faɗi alkhairi ko ya yi shuru."

Shiyasa ake cewa ba mu iya sana'a ba, ai ba shiga inda ya dace ne ba mu iya ba, ba kuma rashin iya tsara lamura ne ba, har da ci da zuci da kuma rashin iya magana, za ka sami mutum a wurin sana'a amma fuskan nan a murtuƙe ba ko alamar murmushi, wani kuma ya riga ya kafa wa kansa dokar ba zai yi magana sau biyu ba, in ya yi ta farkon nan sai ka yi da gaske kafin ka ji ya ƙara tanka maka, har ka ga wasu masu biɗar kayan sun kama gaban su, kuma za ka ga ko a jikinsa, a ganinsa in ka tafi wani ma zai zo don haka tafiyar ka ba matsala ba ce.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (5) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (6) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (8) Cikin Sauki

Akwai mutanen da in ka zo wajen sana'ar su sai ka ce kai ne sarkin, lallaɓa ka ake yi, komai ka ce kana so yanzu za a yi maka, in ma wurin sayar da kaya ne kana gama cinikin ka za ka ji suna yi maka godiya, in ka ce kayansu da tsada cikin murmushi za su yi maka bayani har ka gane, ka ga an rabu cikin raha da dariya, irin waɗannan don ka koma ko ka kira wani ba matsala ba ne, saboda shimfiɗar fuska ta fi shimfidar tabarma, saɓanin wanda zai gasa maka magana kuma ko a jikin sa, mu koyi magana mai daɗi kodon gyara lamuran mu.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.



MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user