Friday 17 January 2020

SHIN KO KASAN ZABI BIYU KAKE DA SHI A RAYUWA?

Tura Wannan Zuwa Ga
A rayuwar nan kana da zaɓi guda biyu idan wani ya tafka maka kuskure ko laifi ko ya zalunce ka.

Yin Haƙuri shi yafi Muhimmanci a Rayuwa..

Marubuciya: Fatima Zahra

Inma kace "Allah ka shaida na yafewa wane duk abin daya min na zalunci"

Wannan kalmar ba rashin wayo bane, ba kuma rashin dabara bane, ana sa ran ta wannan hanyar ka samu Alkhairi guda uku.

1. Gafarar Ubangiji: domin niyyarka.

2. Sauƙin Hisabi: domin baza ku tsaya ɓata lokaci dakai dashi a gaban Allah ba tunda ka yafe.

3. Maye maka gurbinsa da abu me kyau mafi Alkhairi  daga Ubangiji.

Ka sani karkace indai abu kaza ne baza ka yafe ba, a'a koma menene yi ƙoƙari ka danne ka yafe, ka sani akwai laifi masu girma masu yawa kaima da kake so Allah ya yafe maka.

Shin ko baka So kaima Allah (S.W.T) ya yafe maka?

Inma kace"Allah ya isa ban yafe ba, Allah Kabi min haƙƙina"

Allah me Adalci ne, zai bi maka Haƙƙi ranar gobe ƙiyama, zaka tsaya dakai dashi ayi muku shari'a abawa me Haƙƙi haƙƙinsa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa

Karanta Abu Biyu Kawai Zaka Iya yi Idan Ka Hadu da Wanda Yafi Karfin Ka

Karanta Hanyoyin Samun Rayuwa Mai Dadi Cikin Sauki

Amma ka sani ana sa ran ka rasa waɗancan tarun alkhairan, idan ka rama kuma kayi balance, shikenan.

Abin me sauƙi ne ko wacce ƙwarya da abokin gurminta.

Allah ya bamu zuciya Me Yafiya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user