Thursday 19 December 2019

KARANTA HANYOYIN SAMUN RAYUWA MAI DADI CIKIN SAUKI

Tura Wannan Zuwa Ga
Karka tsani kowa, duk girman rashin fahimtar ka da yayi.

Hanyoyin Jin Dadin Rayuwa

Ka rayu cikin sauƙin kai duk da yawan dukiyar da Allah ya baka.

Ka yi tunanin mai kyau, ka dogara ga Allah duk da ƙuncin rayuwa da kake ciki.

Ka bayar da yawa kar ka matse hannu duk da ƙarancin abinda kake samu.

Ci gaba da kulawa da Sallama ga waɗanda suka manta da kai, sannan kayi yafiya ga waɗanda suka ɓata maka, wata rana sai labari.

Karka tsaida addu'ar alkairi ga waɗanda suke sonka don ka sani kullum kana ran su.


Hanyoyin Jin Dadin Rayuwa

Baka sanin dadin lafiya sai idan ciwo ya same ka, hakanan baka sanin dadin zaman lafiya sai tashin hankali ya ziyarce Ka.

Wanda yafi kowa girma shine wanda baya ganin girman kansa, wanda yafi kowa ɗaukaka shine wanda yake amfanar mutane.

Ana sanin daɗin haɗuwa ne idan an rabu, godewa ni'imomin Allah wanda ka sani da wanda ma baka sani ba.

Shin kana sada zumunci kuma kana kyautatawa makocin Ka?

Ka sani idan kafi karfin mutane baka fi karfin Allah ba, kuma yana nan a madakata zaka zo ka same Shi.

Zunubin da yasaka yin danasani da komawa ga Allah yafi ibadar data saka girmar kai da ɗagawa!

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

ME CE CE KUNYA KUMA TA YA YA AKE GANE MUTUM YANA DA KUNYA ??

KARANTA ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI

Idan farce yayi tsawo shi muke yankewa ba yatsan ba. Haka ne idan mukayi saɓani, kawar dashi ya kamata muyi ta hanyar sulhu bata hanyar yanke alaƙa dake tsakani ba.

Ya Allah ya sa Muyi kyakkyawan karshe Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user