Friday 31 August 2018

Karanta Takaitaccen Tarihi akan Tushen Harshen Hausa da Al'ummar Hausawa

Tura Wannan Zuwa Ga
A duk ranar 26 ga watan Agusta, ranan ne da akaware saboda Hausa a Duniya. Rana da marubuta suke tunawa da al'adun malam Bauhaushe da tasirin su a Duniya.

Ranar Hausa ta Duniya


MarubuciMahmud Isa Yola

Hausa daya ne daga cikin manyan tsoffin yaren Afirka guda goma wadanda ake kira a turance da "Afro-Asiatic Speaking Groups". A kalla masu magana da yaren Hausa a matsayin yare na farko sun haura miliyan 70, a kiyasin Jaridar 'The Guardian' ta kasar Amurka. Sannan a kalla sama da miliyan 50 a matsayin yare na biyu.

Masu sadarwa da yaren Hausa a duniya ba sun tsaya a Afirka ta yamma ba, duk da cewa Afirka ta yamma za'a iya cewa ita ce cibiyar Hausa, saboda manyan garuruwan Hausawa a nan suke.

Alkaluman shafin tattara bayanai na Wikipedia sun bayyana kasashe 14 da suke dauke da dimbin mutane masu jin yaren hausa kuma suna magana da Hausa a matsayin yare na farko ko na biyu.

Kashen sun hada da:

Nigeria 30, 211, 000
Niger 10, 238, 000
Benin 1, 058, 000
Saudi Arabia 1, 000, 000
Ivory Coast 385, 000
Cameroon 357, 000
Ghana 275, 000
Chad 274, 000
Togo 20, 000
Gabon 12, 000
Algeria 11, 000
Congo 9, 400
Burkina Faso 2, 700.

Yaren Hausa yayi tasiri sosai a duniya, kasancewar shi yare na farko da kafafen yada labarai na turai suka fara dauka don isar da sako a Afirka. Baya ga tasirin yaren Hausa a bangaren kafafen sadarwa, Yaren Hausa ya shiga kasashen turawa da na larabawa musamman a lokacin kasuwancin bayi wadanda ake safarar su daga kasashen Afirka zuwa Turai ko yankunan larabawa.

Rubuce rubuce akan Hausawa da kuma shirye shiryen a kafafen sadarwa ya taimakawa yaren Hausa ratsa duniya ta fannoni daban daban. Wannan ya janyo kafafen sadarwa irin su BBC, VOA, Deutsche Welle, Radio Moscow, Radio Beijing, RFI France, IRIB Iran da sauran su, suka zabi Harshen Hausa a matsayin daya daga cikin yaren da suke amfani da shi wajen isar da sako ga Al'ummar Afirka.

Banagaren Kasuwanci da raya tattalin arziki kuma, Hausawa sun shahara ta fannoni daban daban. Idan muka dauki noma, wanda kusan shine cibiyan tattalin arzikin malam Bahaushe, zamu ga tun kafin bayyanar turawan mulkin mallaka Hausawa suke da karfin tattalin arziki. Tun daga kasuwancin dillancin goro tsakanin kasashen Hausa da na larabawa a shekarun 1700 har dalar gyada, zamu fahimci yanda Hausawa suka dauki noma tushen arziki.
Al'adun Malam Bauhaushe, tun daga sutura: riga malum-malum, sulke, jabba, alkyabba, rawani, wando bante, har zuwa huluna daban daban, ginin gidan malam Bahaushe da abincin da yake ci zamu fahimci tasirin al'adar sa.


Hakika, Hausa yana cikin sahun mayan yaruka na duniya lura da yawan masu magana da yaren, da kayatattun al'adu da Hausa ke dauke da su.

Bazamu iya ambatan nasarorin siyasar Nijeriya ba ba tare da kawo sunayen shahararrun 'yan siyasa Hausawa ba. Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa da Alh Ahmadu Bello sune shugabannin farko na Nijeriya, wadanda gudunmawar da suka bayar ya daukaka darajar Nijeriya a duniya baki daya.

Daga tarihi zamu fahimci tasirin Hausa a duniyar da da na yanzu, da kuma shaharar yaren. Haka kuma zamu fahinci yanda al'adun malan Bahaushe ya zama abun sha'awa ga masu nazarin tarihi da al'adu.Halin Hausawa na tarban baki, da saukin kai da riko da tarbiyya, kamar yanda shafin 'Historyarchive' ya wallafa, ya sanya Hausawa samun saukin shigar da al'adun su ga wadanda suka bakunce su.

A yayin da muke bikin ranar Hausawa ta duniya, mu tuna da sadaukarwar shugabanni da jagororin Hausawa, da tarbiyya da halayen su da mu'amalar su da al'adun su wadanda ko shakka babu, ababen koyi ne gare mu duka.

Za'a iya samun Marubuci a:

+2348106792663 (Text only)

isamahmud77@gmail.com


Karanta Kaji: Takaitaccen Tarihin Yaren Harshen Hausa 


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user