Thursday 30 August 2018

Takaitaccen Tarihin Ahmad S. Nuhu: Abubuwa guda 10 Da Yakamata Ku Sani Dangane Da Rayuwar Marigayi Ahmed S. Nuhu

Tura Wannan Zuwa Ga
Marigayi Ahmed S. Nuhu Fitaccen Jarumi ne a masana'anatar Shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood domin rawar da jarumin ya taka a zamanin sa.

Ahmed S. Nuhu

Domin Tunawa da irin rawar da Gwarzon jarumin  ya baiwa masana'antar kannywood Shafin Muryar Hausa24 ta kawo muku wasu muhimman abubuwan da yakamata ku sani guda guda goma da suka shafi rayuwar jarumin kafin Rasuwar sa.

1. Shine kaɗai jarumin da haryanzu ake Alhinin rasuwar sa kuma aka kasa mantawa da shi a masana'antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, domin duk ranar rasuwar sa idan ta zagayo sai an ta sanya hotunan shi ana yi masa kyakykyawan fatan samun rahama hakan yasamo asali ne sanadiyyar Jarumi Ali Nuhu wanda shine ya sunnanta hakan ta hanyar fara wannan al'adar a shafukan sa na sada zumunta da musayan ra'ayi.

2. Rasuwar Jarumin  ce tafi girgiza masana'antar shirya fina-finan Hausa ta kannywood tin bayan rasuwar Jaruma Balaraba Muhammad ba'a kuma samun jarumin da rasuwar shi ta girgiza masana'antar Shirya fina-finan Hausa ba irin rasuwar jarumi Ahmed S. Nuhu, jarumin ya rasu a shekarar dubu biyu da bakwai ɗaya ga watan ɗaya (1/1/2007) a sanadiyyar hatsarin mota akan titin zuwa Maiduguri.

Ahmed S. Nuhu da Hafsat Shehu

3. Marigayi Ahmed S. Nuhu shine jarumi na uku cikin jerin sunayen jaruman da suka auri abokanan Sana'ar su lokacin da tauraruwar su ke tsaka da haskawa a masana'antar kannywood, sai dai shi ya auri jaruma Hafsat Shehu lokacin da tauraruwar ta ke tsaka da haskawa a masana'antar kannywood, jaruman da suka auri abokanan sana'ar su a lokacin da tauraruwar su ke tsaka da haskawa a wancan lokacin sune kamar haka:

Jarumi Shu'aibu Lawal ya auri marigayiya Balaraba Muhammad , Jarumi Sani Musa Mai Iska ya auri Jaruma Fati Muhammad waɗannan sune su auri abokan sana'ar su bayan auran sune Marigayi Ahmed S. Nuhu ya kasance jarumi na uku a cikin jaruman kannywood da ya auri abokiyar sana'ar sa.

4. Kamar yadda majiyar mu ta tabbatarwa da wakilin Shafin Muryar Hausa24 Cewa"Jarumin bai taɓa karɓar kyautar gwarzon jarumi a lokacin sa ba, babu mai yin tantama Ahmed S. Nuhu ya kasance jarumin da yafi kowanne jarumi iya shiga kowanne irin yanayi ake so ya shiga a gaban kyamara, amma duk da haka bai taɓa karɓar gwarzon jarumi ba harya gama lokacin sa, amma wasu na danganta hakan da kasancewar sa ƙarƙashin inuwar jarumi Ali Nuhu, wanda shima yana sharafi a wancan lokacin, kuma shi marigayin ya kasance mutum ne mai kunya da girmama na sama da shi ".

5. Fim ɗin Huznee na hafizu bello shine fim ɗin da ya fara haskaka jarumin  duk da kasancewar fim ɗin an kwaikwayi wasu fina-finan indiya ne kamar irin su Agni Shakshi a shekarar 1996 da kuma fim ɗin Daraar a shekarar 1997, amma fim ɗin ya samu karɓuwa matuka  musamman saboda ganin yadda jarumin  ya nuna kwarewar sa wajen aikin fim ɗin hakan yasa ya samu lashe kyautar mai taimakawa jarumi ( Best Sporting Actor).

Ahmed S. Nuhu

6. A Shekarar dubu biyu da uku (2003) kamfanin layin waya na sadarwa MTN a Nigeria ya bayyana jarumi Ahmed S. Nuhu a matsayin mutum na bakwai da yafi kowa amsa kiran waya a duk faɗin Nigeria a wannan shekarar ta 2003.

7. Dalilin yin fim ɗin sansani anyi shine kacokan akan tarihin rayuwar sa ta zahiri, a wata tattaunawa ta musamman da akai da jarumin a jaridar tauraruwa ya bayyana Cewa"Fim ɗin sansani wanda kamfanin FKD PRODUCTION ta shirya anyi shine saboda akan abinda yafaru da rayuwar sa ta zahiri, an shirya fim ɗin a shekarar dubu biyu da uku (2003) , duk wanda yake san sanin yadda rayuwar marigayi Ahmed S. Nuhu ta kasance sai ya nemi fim ɗin sansani.

8. Marigayi Ahmed S. Nuhu ya shiga harkar fina-finan hausa  ne ta sanadiyyar jarumi Ali Nuhu, a wani labarin ance alaƙar sa da jarumi Ali Nuhu ta samo asali ne lokacin da yake karatu a jami'ar jos saboda ya zauna a gidan kakan marigayi Ahmed S. Nuhu, amma a wata tattaunawa da akai da  Marigayi Ahmed S. Nuhu a jaridar mujallar fim ta shekarar dubu biyu da biyu ga watan yuni (july/2002) a shafi na ashirin da ɗaya (page 21)  ya bayyana Cewa"Jarumi Ali Nuhu amatsayin ƙanin mahaifiyar sa".

Ahmed S. Nuhu

9. Marigayi Ahmed S. Nuhu ya sha gwagwarmayar rayuwa kafin ya samu ɗaukaka, a lokacin da yake sakandire sakamakon rashin lafiyar mahaifinsa yasa bazai iya ci gaba da ɗaukar nauyin karatun sa ba har takai ga sai da Ahmed ya fara direban taxi da kabu-kabu domin ya ɗauki ɗawainiyar karatun nasa har zuwa lokacin da zai kammala, bayan nan kuma sai ya fara bin babbar mota haryazama direban babbar mota mai ɗauko kaya daga onisha zuwa jos.

10. Marigayi Ahmed S. Nuhu da Hawwa Ali Dodo Dukkan jaruman sun rasu ne a ranar 1 ga watan Janairu, amma ba a cikin shekara daya su ka rasu ba.

Ahmed ya rasu a cikin 2007, ita kuma marigayiya Hauwa wadda ake yi wa laƙabi da Biba Problem ta rasu a cikin 2010.

Matar Marigayi Hafsat Shehu

Ɗaukacin Ma'aikatan wannan shafi mai Albarka na Muryar Hausa24  na yiwa jaruman kyakykyawan  fatan samun rahama, Allah yasa mutuwa hutuce ga duk wani ɗan uwa musulmi Amin Summa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user