Thursday 30 August 2018

DOWNLOAD SABUWAR WAKAR RARARA MAI ZAFI AKAN ATIKU DA BUHARI LATEST RARARA SONG

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙar Siyasa.

Rarara da Atiku Abubakar

Fitaccen Mawaƙin Siyasar ƙasar Nigeria Musamman akan abin da ya shafi Jam'iyyar APC , haƙiƙa babu kamar Dauda Adamu Kahutu Rarara a Nigeria.

A kwanakin baya ne dai ma'abota bibiyar wannan shafi na Muryar Hausa24 mai Albarka suke aiko mana da saƙonni daban-daban akan Cewa"Shin da gaske ne rarara yayiwa Abubakar Turakin Adamawa waƙa?, tare da wasu tambayoyi makamantan hakan".

Taken Wakar "ATIKU ABUBAKAR TURAKI BANGO MAJINGINAR 'YAN NIGERIA".

Muryar Hausa24: Magana ta gaskiya Rarara yayi ma Abubakar Turaki waƙa, amma yayi masa lokacin da yake jigo a jam'iyyar APC.

Ga taken waƙar kamar haka:

Kuban kiɗan ƙashin gwiwar duniya...

Amshi: Turaki

Hasken Arewa kai kahaɗe nahiya...

Amshi: Turaki

Ƙashi bugun ƙashi taku ka iya...

Amshi: Turaki

Bango majinginar 'yan Nigeria ...

Amshi: Turaki

Namijin maza kadan garkin duniya ...

Amshi: Turaki

Farin ciki uban ɗakin fariya...

Amshi: Turaki

Ga ɗan kahutu rarara mai kabiya...

Amshi: Turaki

Atiku Abubakar taku lafiya...

Amshi: Turaki

Nigeria ka kafaf kai ne maliya...

Amshi: Turaki

Don kazamo madubin  Nigeria...

Amshi: Turaki

Domin ko kai kasan sirrin tin jiya...

Amshi: Turaki

Kune ku ke tuwo kune am miya...

Amshi: Turaki

A cikin africa kaf kai ne jan wuya...

Amshi: Turaki

Atiku Abubakar Namijin Duniya...

Amshi: Turaki

In kataho ina wani mai tambaya...

Amshi: Turaki

Burin ka taimako baka fariya...

Amshi: Turaki

Wallahi sai da ku za'ai gwamnati..

Amshi: Turaki

Aikin da babu ku baya kwaliti...

Amshi: Turaki

Atiku Abubakar Turaki da kai muke kwatance bango majinginar 'Yan Nijeriyar mu kenan...

Waƙar tasha sauti mai inganci kuma Dauda Kahutu Rarara ya zuba basira a cikin waƙar sosai.

Ku sauke waƙar anan...


Ayi sauraro Lafiya.

Wannan waƙar ce kaɗai zata fayyace maka matsayin Atiku Abubakar a jam'iyar APC mai Mulki a Nijeriya kafin yayi hijira zuwa jam'iyar PDP mai adawa a Nigeria.

A halin yanzu dai kowa yasan Atiku Abubakar Turaki baya tare da Jam'iyyar APC ya koma Jam'iyyar Adawa ta PDP.

Masoyan Atiku Abubakar sun fara sakin hotunan takarar Atiku Abubakar a matsayin Shugaban ƙasar Nijeriya a 2019 sun fara sakin hotunan a social media .

Hotan Takarar Shugaban ƙasa a 2019

Wannan shine hotan da Muryar Hausa24 ta samu ɗaya daga cikin hotunan.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user