Tuesday 28 August 2018

Yanzu - Yanzu: Karanta Manya-Manyan Ayyukan da Shugaba Buhari ya rabawa 'Yan Nigeria

Tura Wannan Zuwa Ga
A cikin kasa da sati guda, mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rabawa 'yan social media aikin yi, inda kowanne 6angare ya dage tukuru wajen gudanar da nasa aikin ba tare da algus ba.


Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja

Wani aikin shi da kansa ya raba, wani kuwa, masoya, 'yan adawa, mahassada da makiya ne suka raba mana....

1. Ranar Sallah bayan an sakko daga Sallar Idi yayi tafiya a kasa, mai nisan zangon mita 800, domin ya gaisa da jama'ar gundumarsa, kuma yayi musu barka da sallah.

Hakan ce tasa masoyansa yaba masa, inda makiya da mahassada tare da 'yan adawa kuma suka kama cewa yayi tafiyar ne dan ya nuna koshin lafiyarsa, wanda hakan har ta jawo shugaban ya mayar da martani.

2. Wannan bata gama gushewa ba, sai wasu jarida sun bada labarin cewa: "Shugaban zai bude kamfanin sarrafa giya a jihar Ogun, wanda kuma shine zai kasance kamfanin giya mafi girma a nahiyar Afrika.
Nan ma 'yan kuci ku bamu, masu baki da kunu tare da 'ya yada jita-jita suka dauki wannan zancen, ya zame musu abin wallafawa a shafukansu na dandalin sada zumunta.

Inda a 6angare guda kuma wasu masu yiwa shugaban makauniyar soyayya suka fara kareshi.

Har aka yi wannan zance aka gama bance uffan ba akai, dan kuwa babban abinda na duba shine, ita wannan sanarwa ba daga fadar gwamnatin ta fito ba, kuma babu sa hannun daya daga cikin mataimaka na musamman ga shugaban kasar akan sha'anin yada labarai.

Inda a karshe na yanke shawarar cewa: "kawai na jira ranar da aka ce za'a kaddamar da wancan kamfani, idan ta tabbata (wanda ba haka nake fata ba), shugaban yasha suka daga gareni.
Idan kuwa karyane, to Allah ya kunyata wadancan kenan, kuma gashi yau ne kwanan watan da aka saka a waccan sanarwa".

Sai dai abin tambayar shine, an fasa ne?
Ko kuwa an daga ne zuwa wata ranar anan gaba?
Ko kuma dai dama shifcin gizo ne?.

3. Waccan kuma bata gama lafawa ba, sai gashi an kara yada wani labarin a jiya, inda ake cewa: " Wai shugaban kasar Amurika Donald Trumph ya soki shugaba Buharin da munanan kalamai".

Nan ma dai 'yan social media din suka fara soma halin nasu na yin murna, tare da nuna jin dadinsu akan wannan kalamai.

Hahaha....! Ni wallahi sai aka bani dariya ma, kwata-kwata wannan labari bai bani mamaki ba, dan kuwa shi wancan dan tahaliki ba yau ya fara kato6ara ba, hasalima ya tsani duk wani shugaban kasa musulmi, da kuma kasashen musulmai, kuma a kullum baya iya rike irin kiyayyar da yake musu a cikin ransa, kullum kokarinsa bai wuce ya fito fili ya nunawa duniya irin wannan muguwar al'ada tasa ba.

Kuma ko ba komai wallahi nasan bazai ta6a kaunar kasar Najeriya ba, koda kuwa ba Buhari bane akan mulki, domin Najeriya tana daya daga cikin kasashen da suka ki goyon bayan mayar da ofishin jakadancin Amurika na Isra'ila zuwa birnin Gaza, inda har suka goyi bayan cewa suma wadancan musulmi a basu 'yancin kansu. Sa6anin zamanin mulkin shugaba Jonathan, inda aka bukaci jakadiyar Najeriya da ta fice daga dakin taron, dai-dai loton da ake daf da kada waccan kuri'a.

A wani 6angaren kuma sai na kalli Shugaban Amurikan a matsayin "Zulwajahaini" (mai fuska biyu).

Dan kuwa shine dai ya yabawa Shugaba Buharin, a lokacin da Buharin yakai wata ziyara kasar Amurikan kwanakin baya, yau kuma yazo yana sukarsa, to da wanne zancen zamu yarda kenan?

Wancan da ya yabawa Shugaba Buharin ko kuma wannan da ya soki Shugaban?
.
Hahaha.....! Allah ya kara lafiya da nisan kwana mai girma Shugaban Najeriya Mallam Muhammadu Buhari, lalle ka zama rana mai rabawa kowa aiki, kowa ya ajiye aikinsa ya kama naka.

'Yan social media suna zancenka, makiya zancenka, yan adawa zancenka, mahassada zancenka, magoya baya zancenka, jaridu zancenka, kafafen yada labarai zancenka, Shugaban kasashen duniya zancenka......

Sai kayi 8 da izinin Allah, haushi ya kashe makiyanka....

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user