Thursday 16 January 2020

Karanta Hirar Masoya Tsakanin Saurayi da Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga
Budurwa: Baby kana sona kuwa?

Saurayi: Kwarai kuwa baby duk duniya ba wacce nake so kamar ke.

Hirar Masoya Tsakanin Saurayi da Budurwa

Marubuci: Jabir M. Hassan

Budurwa: Koda zan wanka maka mari mai zafi?

Saurayi: Ai ko abinda yafi hakama ba zan damu ba.

Budurwa: Idan na mari ƙanwarka a gabanka fa ko yayanka?"

Saurayi: Idan kika mari ƙanwata haƙuri zan bata, ai ke yayarta ce dole tayi haƙuri, idan kika mari yayana haƙuri zan bashi, saboda ke ƙanwarsace ai, kuma akwai ƙuruciya a tattare dake, ko kuma na tsaya ya dakeni a maimakon ke ɗin.

Budurwa: To idan na mari mamarka fa?

Saurayi: Tasss! Tasss!! Tasss!!! ya wanketa da mari har sau uku.

Budurwa: Kan batasi! Ni zaka mara har sau uku daga na tambayeka?

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ZAFAFAN SAKONNIN SOYAYYA GUDA 32 MASU RATSA ZUKATAN MASOYA MAZA DA MATA NA ZAMANI

Karanta Labarin Wata Kyakkyawar Budurwa da Samari Guda Biyu

KARANTA ALAMOMI 10 DAZAKA FAHIMCI MACE TANA SON KA

Saurayi a fusace  An mareki, ki ɗauki mataki dan ubanki, mari na farko danayi miki don kinyi tunanin zaki mari mamata ne, mari na biyu kuma don kin faɗa ne, na uku kuma gargaɗi ne don idan ma kikayi tunanin marin mamata sai na kakkaryaki wallahi, banza 'yar rainin hankali.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user