Sunday 19 January 2020

ABIN DA YA KAMATA KU SANI KAFIN KU FARA SHIGA CIKIN BIRNIN JIHAR KANO

Tura Wannan Zuwa Ga
WASIYYATA GA ABOKINA DA ZAI ZO KANO

Ya Kai abokina, ka sani cewa garin Kano yafi kyau a hoto, hakazalika yafi daɗi a saurare. Domin saukin fahimtar da kai hakan ka saurari jawabin da zan maka a ƙasa.

Wani yanki daga cikin Birnin Kano


Marubuci: Muhammad S. Hassan

DA fari idan ka sauka a tasha, kada ka fiye yawan waige-waige koda kuwa ka ji an kira sunanka ne, domin tun a wannan takin zaka iya rabuwa da abin aljihunka. Ba sai an gama jiki da kai ake iya yasheka ba, yo wannan ma ai tsohon yayi ne.

Akwai cikowwa a garin, ba lallai sai ka kuskure hawa tsakiyar titi bane kaɗai za a zungureka da abin hawa, saboda haka ka kula wajen tafiya a gefen titi ma.

Idan ka fara shiga gari akwai (Keke Napep) wato adaidata sahu kayi amfani da iskar bakinka wajen tsayar dashi ma'ana siiit! Kada ka hau wanda ya ganka ya tambayeka "ina zuwa?"

Ka killace wayarka, ba lallai sai a halin tafiyar ƙafa bane ake ƙwace wayoyin hannu, Masu wannan ta'asa sunfi son mahaya abin hawa; adaidata sahu.

Idan tsautsayi ya ritsa da kai, ana maka tsawa "bamu wayarka" kada kayi takiyya ka miƙa ba ko jinkirin daƙiƙa, na san dai rayuwarka tafi dukiyarka muhimmanci a wajenka.

Duk tuƙin ganganci da akayi da kai da karya dokar kan hanya kayi gum da baka, Kanawan asalin ma basu iya kawo canji ba bare kai da kazo ziyarar 'yan kwanaki. Ka sani mu anan mun fi fahimtar daftarin hukunci sama da na gyara-kayanka, don haka kada kayi katsalandan a aikin da na hukuma ne.

Bayan ka ɗan natsa a gari, kada kayi tuƙi, Ba a ƙwarewa da tuki a Kano bare a gwanance, lura tafi komai muhimmanci, yau da gobe kuwa ita ke taimakawa kullum ana komawa gida ba ko kwarzane.

Idan duhu yayi, ba da hasken waya muke haska gabanmu ba, kayi amfani da Shekarau ya gaza da makamantansa, ko kuma kai ka gaza zuwa gida da wayar hannunka.

Kada ka nuna matuƙar wayewa, kuma kada ka fito a zubin ƙauye, ka zama tsaka-tsaki. Babu abinda bakano yafi ganewa da wuri sama da baƙo mai son ya rikiɗe kamar ɗan gari.

Watakil kayi sha'awar shiga kasuwa, ko domin tarkata na tsaraba yayin komawa gida, addu'ar shiga kasuwa zata fi ƙwatarka sama da duk wata dabara, ka tabbata ka haddace wannan.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Wasiyyar Wani Uba Mai Hikima Ga Dan Sa a Zamanin Internet

Karanta Cikakken Tarhin Samuwar Takutaha da Dalilin da Yasa ake Yinta Harzuwa Yanzu

TAKAITACCEN TARIHIN KAFUWAR BIRNIN KANO A AREWACIN KASAR NIGERIA

Domin a kasuwa ba ɓarawo ne kaɗai yake neman rabaka da kuɗinka ba a ɓagas, hatta wanda kaje siyayya wajensa shima ya nau'antu da hakan.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode




TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user