Tuesday 19 November 2019

Karanta Cikakken Tarhin Samuwar Takutaha da Dalilin da Yasa ake Yinta Harzuwa Yanzu

Tura Wannan Zuwa Ga
Asali,  kusan shekaru dubu da suka gabata, Kano ba gari bane,  Shirayi ne kawai,  kamar yadda marubucin wakar Bagauda ta Kano ya bayyana.

Zagayen Takutaha


Marubuci: Fatuhu Mustapha

Birnin Kano a wannan lokaci ya shahara ne a matsayin wurin bauta,  dake cike da addinai kalakala.  Wadanda suka hada da ; masu bautar ruwa, wadanda ke zaune a Bakin Ruwa,  kuma asalinsu sun taso daga kasar Gaya ne.  Wadannan suke ke bautar ruwan jakara.  Kuma sun amince shine yake tsaresu daga dukkan wani balai da zai taso musu,  ko kuma ya taso ma garinsu.

Akwai masu bautar farji,  wadanda ke zaune a Dutsen Bompai,  wadanda aka fi sani da Gwandarawa,  sukan yi wa azzakarin limaminsu,  farjin limamiyarsu sujada (ba lallai irin ta musulunci ba). Kuma addinin nasu cike yake da raye-raye da kade-kade.  Shine asalin ake kiransu da Gwandarawa wato: Gwanda-rawa-da-sallah.

Wani nau'in addinin shine Adzna ko Arna.  Wadanda ke Gwabron Dutse.  Su wadannan sune masu bautar Ubangiji.  Wato wani Allahnsu ne da suke bautawa,  Wanda a zatonsu yana ko ina.  Haka kuma suna da gumaka da suke bautawa a matsayin wakilan Shi wannan ubangiji.  Ita wannan kalma,  ita ce malaman musulunci suka amsheta,  suka nuna cewa ba Wanda ya cancanci wannan siffa ta ubangiji in banda Allah (domin shine yake ko ina,  ilminsa ya game komai).

Addinin da yafi kowanne karfi da shahara,  kuma manyan sarakunan kasar Kano dake da helikwata a Santolo suke bi,  shine addinin maguzanci.  Wanda babban wurin bautarsu ke kan Dutsen Dala.  Masu bin wannan addini su ake kira  Maguzawa,  Farfesa Murray Last a kasidarsa maitaken : Historical Metaphor in the history of Kano ya bayyana cewa asalin sunan,  ya samo ne daga "Majus " wato majusawa.  Wadannan bayin Allah na bautar iskokai ne,  wato aljannu.  Musamman wata aljanna da ake kira Tsumburbura,  ko kuma Danko. Malam Adamu na Maaji ya bayyana a littafinsa I'lan bi Tarikh Kano cewa,  asalin wannan aljan ana bauta mata tun zamanin  Annabi Nuhu,  inda ya tabbatar da cewa ita ce 'Yaquqa ' da aka fada a alqurani,  cikin suratul Nuh.

Akwai kuma masu bautar Bishiya da aka fi sani da Gazargawa,  wanda sheikh AbdurRahman Zagaiti ya sha fama da su.  Sune ke zaune a Shirawa,  akwai cikakken bayani akan wannan rigima a kundin nan maisuna: Waraqa makatuba,  fiha asl al wangariyun ".

Akwai sauran addinai da dama wanda Malam Nasiru Kabara ya yi dogon bayani akan su,  a wani kaset na waazinsa da ya Maida martani ga malaman Izala akan gudunmowar sufaye a wurin yada addinin musulunci a Kasar Kano.  (Abin bakin ciki na nemi kaset din na rasa).

Dokar kasar Kano a wannan lokaci shine: tunda kasa ce mai tsarki ta gamayyar addinan Hausawa,  da suke aikin hajji duk shekara acikinta,  kuma malamnsu da limamansu duk na ciki,  to baa yadda kayi  noma acikinta ba, ba kuma a yadda kayi farauta acikinta ba. Duk yayi wannan to zaiyi fuskantar fushin  Allolinsu ko kuma ya fuskanci yaki daga Sarakan Kasar dake zaune a Santolo (wato Tsakuwa kenan dake karamar hukumar Dawakin Kudu  a yau). Wannan dalilin ne ya sanya Shi kansa limaminsu mafi shahara (Barbushe), yake tafiyar wuni domin ya farauto nama.  Saboda ba damar yin farauta a garin  Kano da kewaye.  Hakan ta sanya kqbilar Doma suka bar gari saboda mafarauta ne, suka koma Kazaure,  karkashin jagorancin shugabansu maisuna Kazaure.

Yunkurin Bagaudawa;

Farkon Wanda suka fara yunkurin rusa wannan addinai sune Abagayawa,  asalinsu makera ne da manoma, sukan kuma taba farauta.  A wannan lokaci saboda bukatar sabon wurin noma da kuma neman karfe domin  kara fadada  sanaarsu,  ta sanya dole su fara neman sabon wuri,  inda zasu  samu  kasa mai yalwa,  da kuma isasshen  karfe.  Ba kuma inda yake da wannan abubuwa in ba Kano ba. Gashi kuma baa noma a kasar Kano,  kuma baa farauta,  ba kuma dama a haki maadaninta.  To amma fa,  dan wuya ba zaa bar dadi ba.

Zuwa Bagauda Kano ya tabbatar da shi fa yaga,  domin yaga akwai karfe  a kasa,  ga kuma kasar noma mai albarka,  sannan ga dabbobi kala kala.  Don haka ya yanke shawarar Shi fa, sai dai ayi wacce zaayi,  amma dole  a barsu,  su cigaba da rayuwa a kasar Kano.  Kuma dole su noma kasa, dole su hako karfe,  dole kuma a barsu suyi  farauta,  don ba zasu bar nama a banza  ba.

Wannan yunkuri  na Bagauda da mutanensa,  ya jawo  musu tsangwama  daga sarakunan Santolo da kuma tofin  Allah tsine  daga manyan limaman Kano.  Koda  yake da farko  Bagauda ya keta  doka yayi yanda  yake  so,  amma baa jima Santolo ta zo da runduna  mai karfi ta fatattake  shi,  inda ya sha da kyar,  ya tattara  yanasa-yanasa  ya koma Shema  a kasar Kazaure,  acan ya mutu!

Sai dai  wannan fatattaka  da akayi  masa ya bar  baya da kura,  domin ya haifar  da gadajjiyar  gaba tsakanin  Bagaudawa  da manyan  addinan  Kano,  inda suka sha alwashin  ko bajima,  ko badade,  sai  sunga bayan  wadannan addinai.  Sun  shafe kusan  shekara  100 da doriya suna mulki  a kasar Kazaure,  kafin  daga  baya dama ta samu  a zamanin Gajimasu su dawo su kafa  garin  kano.

Bawata cikakkiyar  bayani,  akan ko ya akai  suka dawo,  cikin  Kano,  domin kundin  Tarikh  Arbab  bai bada wani bayani  cikakke ba akan yadda sukayi nasarar  dawowa  cikin garin  Kano,  da maido  da masarautarsu,  amma alamu  na nuna  cewa,  a wannan lokaci  karfin  Santolo  yayi rauni  ainun! Kila  ko saboda yake  yake  da ya addabe su,  musamman da daulolin  Tumbi  da kuma Washa,  ko kuma da Zazzau.  Kila hakan  ne  ya sanya  aka bar shirayin  Kano ba wani tsayyayen  tsaro  da zai kareta,  daga mamayar  Bagaudawa.

Koda yake Bagaudaw sun dawo Kano,  amma kuma sai ga shi basu samu yadda suke so, na murkushe  tsoffin  abokan gabarsu  ba.  Duk  wani yunkuri  da suka yi na tabbatar  da mulkinsu,  abin  yaci tura.  Shi kansa Zamnagawa (usmanu) da yayi yunkurin farko,  bai kare  lafiya ba.

Yunkurin Musulunci

Acikin  wannan hali  ne,  a wata shekara  zamanin sarkin Kano  Yaji  dan  Tsamiya,  wasu malaman Wangarawa  karkashin  jagorancin sheikh AbdurRahman Zaiti  suka zo,  Kano,  baya ga musulunci da kuma kasuwanci,  suna kuma da sabbin  makamai  da dabarun  yaki da baa  san  da su  ba a Kano.  Wannan ya sanya Bagaudawa suka karbi  musulunci,  domin su samu hadin  kan  wadannan baki,  su taimaka musu  su yaki  abokan  gabarsu.  Kwana daya  da zuwansu  Sarkin Kano Yaji ya karbi musulunci,  ya kuma canjawa kansa suna zuwa Ali.  Wanda hakan ke nuna, cewa , shirin yaki zaayi,  domin ana cewa Ali bin  Abu Talib shine sarkin yakin  manzon  Allah (saw).

A farkon watan Rabiul  Awwal  na wannan shekara,  ne Yaji  ya tara dukkan  maguzawa,  ya kuma karanta  musu  dokar-ta-baci.  Inda yace musu

"Ku sani,  daga yau, komai tsakanina  daku,  sai yaki  da tsinin  mashi,  ba yaudara,  bawani  boye boye,  domin  ba mayaudari  sai  matsoraci,  ku  shirya  gani nan zuwa gareku "

Mataki  biyu  suka dauka,  na farko sunyi  kokarin  bada  cin  hanci  ga Sarki  Yaji,  amma yaki  karba,  yace  a maida  musu baya so.  Na biyu,  sai suka koma ga Tsumburbura,  domin neman nasara,  amma ta gaya musu,  cewa wannan yaki ba nasara,  domin lokacin  karshen  addininsu  a kasar Kano yazo.

Acikin  watan  dai,  rundunar  musulmi  suka fuskanci,  rundunar  maguzawa,  a gefen  Dutsen Dala,  inda suka hadu,  aka gwabza.  A wannan lokacin ne,  Jarmai  Bajere  ya samu  nasarar  Kutsa  kai cikin  shigifar  Tsumburbura,  inda ya samu  wani  halitta  na tsaye,  rike  da maciji  a hannunsa,  ya daga mashi  ya bugawa  halittar  nan,  tayi  kuwwa ta fito  a guje.  Nan da nan suka bita,  inda ta nufi  kofar  ruwa,  ta fada cikin ruwan  Dankwai.  Wannan Shi ya kawo karshen  Tsumburbura,  da kuma addinin  maguzawa a garin Kano.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Jerin Sunayen ’Ya’yan Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN ATTAJIRI NA DAYA A AFIRKA  ALHALIKO DANGOTE


Karanta Jerin Abinci Hausawa Kafin Zuwan Shinkafa 'Yar Kasashen Waje


Takutaha

Samuwar  wannan Nasara, ba karamin abu  bane  a wurin  musulman  Kano.  Wanda aka shafe  sama da shekaru  100 ana nema.  A dalilin haka ne,  ya sanya  musulman  kanawa duk  shekara,  sukan taru  su hau Dutsen  Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci.  Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe  addinin kafirai.  Domin kafin  zuwan musulunci,  ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba. Amma zuwan musulunci,  yanzu kowa ma sai ya hau,  ya yi kashi ma aka. Wannan shine dalilin da ya sanya ake  takutaha a duk shekara a Kano,  Wanda wasu da basu san tarihin ba, ke ganin jahilci  ne,  ko kuma abu ne, da ya sabawa musulunci.

Allah ya sa mu dace Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user