Tuesday 19 November 2019

KALLI WASU DAGA CIKIN FINA-FINAN ALGAITA DUBSTUDIO DA SUKA DAU LOKACI MAI TSAWO KAFIN SU FITO

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar yadda kuka sani akwai wasu daga cikin fina-finan Algaita da idan aka fito da tallarsu kafin su fito kasuwa suna daukan lokaci mai tsawo, hakan ce ke saka masoya Algaita tunanin cewar laifin Kamfanin Algaita Dubstudio amma sam! ba haka bane.

Ahalin Dambe


Marubuci: Nasiri Bin Muhammad

Laifin yan kasuwa ne, domin su ake sayarwa da faya-fayan amma kuma sai suke ƙin sakarsa saboda wani dalili nasu.

Nan muna dauke da Jadawali na fina-finan.

1. "SARKIN ASKA"

Wannan shiri ya dauki fiye da shekaru uku da yin tallarsa amma bai fito ba. Anyi tallan wannan fassara ne a wata tsohuwar fassarar Algaita mai suna ‘Tsohuwar Gaba’, daga nan ba'a ƙara tallan Sarkin Aska ba. Kawai kwatsam! aka ga shirin ya fito kasuwa.

2. "CHAKWAKIYA"

Wannan shiri shima yaja dogon lokaci kafin a sake shi don inaga yakai kusan shekara ana tallarsa, idan ma baku manta tare ake tallarsu da tare da AshiQui na fassarar Algaita, amma kuma sai aka samu nasara ya fito ya bar AshiQui inda har yanzu kusan shekara biyar kenan da fitowarsa.

Ahalin Dambe

3. "AHALIN DAMBE"

Eh shine ma zance shirin da ya tara dumbin masoya da suka ƙagu da ya fito, don a lokacin da aka fara tallansa saida mutane da yawa suka rinƙa neman shirin amma sai a ce musu bai fito ba. Sai daga baya wurin wata shida da tallansa ya fito, sannan kuma babu wanda bai kalli fassarar ba yace bata yi masa ba. Don wasu ma cewa suke Algaita bata taba fassara film kamarsa ba.

4. "JAMI'IN SIRRI"

Shirin Jarumi Saif Ali Khan da Kareena Kapoor wanda shima akayi tallansa, daga baya bayan lokaci mai tsawo shirin ya fito.

5. "ƘAUNAR ZUCIYA"

Shiri ne wanda tallarsa take da tsuma zukatan masoya, shiri ne na soyayya mai cike da sarƙaƙiya da matsaloli. Wannan shiri saida ya shafe kusan shekara Uku da rabi kafin ya fito, lokacin ma data fito sai aka chanja masa suna aka saka masa ‘Bakin Rijiya’.

6. "MACHASKALI"

Shiri mai dauke da barkwanci, Soyayya da kuma Suburbuda. Tun daga kan tallan shirin za ka gane cewa wannan shiri na musamman ne, domin a iya tallar ma sai ka tsinci barkwanci da duk wani abu daya ƙunsa. Wannan shiri shima yaja lokaci mai tsawo sannan fito duk da wasu kamfanin sun yaudari masoya suka fassara shi suna saka mai irin sunan da Algaita ta saka masa.

7. "FARMAKIN ADALCI"

Shima dai shirin Jarumi Saif Ali Khan ne amma kuma wannan karon da jaruma Katrina Kaif ce a shirin. Wannan shiri tun daga kan tallarsa yaja hankalin mutane da yawa saboda yadda aka tsara tallansa, shiri mai launin suburbuda sai da yaja lokaci mai tsawo kafin a sake shi. Wani abun ma kusan tare aka fara tallarsu da Jami'in Sirri sannan kuma kusan tare suka fito.

8. "JAHADI"

Wannan shiri sau daya aka yi tallansa shika kamar Sarkin Aska, a cikin tallarma ba'a magana kawai Rigin-Riginmu ake nunawa. Sai da ya dade sannan shima ya fito.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KALLI HOTUNA DA TARIHIN WANDA YA FARA FITOWA A MATSAYIN JARUMA MACE KAFIN MATA SU SHIGA FILM A TARIHIN INDIA

Zan bar Harkar Film din India Saboda Yana Barazana ga Tsarin Addinin Musulinci - Jaruma Zaira Wasim

KARANTA SUNAYEN WASU JARUMAN BOLLYWOOD DA SUKA AURI MATAN DA SUKA GIRMESU

SHIN KUNA SON SANIN FINA-FINAN ALGAITA DA A RINƘA SUKAR SU CEWAR BASU YI KYAU BA?

SHIN KUNA SON SANI FINA-FINAN ALGAITA DA AKA DADE ANA TALLANSU KUMA HAR YANZU BASU FITO BA?

SHIN KUNA SON SANIN WANNE DALILI NE YASA FINA-FINAN ALGAITA SUKE KARANCI?

Domin samun wadannan amsoshi sai mu tara a wani lokacin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user