Sunday 7 July 2019

Karanta Ka Ji Dalilin ta: Zan bar Harkar Film din India Saboda Yana Barazana ga Tsarin Addinin Musulinci - Jaruma Zaira Wasim

Tura Wannan Zuwa
Jarumar Fina-Finan Indiya (Bollywood) Zaira Wasim mai shekara 18 a duniya ta bayyana cewa za ta yi adabo da harkar fim saboda abin da ta kira ‘barazanar’ da sana’ar fim din ke haifarwa ga sha’anin addini.                                    
Zaira Wasim


                                                                                  An ruwaito jarumar tana cewa: “Tafiya ce mai matukar wuyar sha’ani; da na share lokaci mai tsawo ina yakar ruhina.” Kamar yadda ta rubuta a wani rubutu mai tsawon gaske a shafinta na Facebook, a ranar Lahadin da ta gabata.
Indiyawa sun yi ta mayar da martani game da  labarin nata; inda da dama suka yi ta sukar dalilin nata na barin harkar fina-finan.

Misis Wasim dai tauraronta a harkar fina-finan na Bollywood ya fara haskawa ne a shekarar 2016- lokacin da ta fito a wani fim mai suna Dangal, daya daga cikin fina-finan Indiya da suka yi tashe a baya-bayan nan.
Jarumar-wacce ’yar yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi ne; a shafinta na Facebook, ta yi karin haske game da yadda ta sha gwagwarmaya a masana’antar fina-finan, da kuma yadda hakan ya shafi dangantakarta da addininta na Musulunci.

Abin da ta wallafa a shafin sada zumuntar, tuni ya yadu inda ya yi ta samun dubban sharhi da nuna so.
“A lokacin da na fara fahimta tare da yin nazarin abin da na sadaukar da lokacina a kai; tunani da hankalina sun nuna min cewa, lokaci ya yi da zan bude wani sabon babin rayuwa; kawai sai na ji cewa, eh lallai na dace sosai da masana’antar; amma dai ba wurin zamana ba ne,” kamar dai yadda ta wallafa.
Ta kara da cewa: “Sana’ar fim, ta gadar min da soyayya da kauna da goyon bayan jama’a da ma yarda daga jama’ar; sai dai a daya bangaren ta kuma dulmiyar da ni zuwa ga jahiltar addini, ta yadda sannu a hankali ba tare da na farga ba; ta nesanta ni da addinin Musulunci. A lokacin da na ci gaba da kasancewa cikin sana’ar da a kullum take yin katsalanda a harkar addinina; to kuma lallai hakan zai yi ta yin barzana ga addinin.”
Ta ci gaba da cewa, a kullum sana’ar na jefa ta cikin ‘raunin imani.’ “Abu ne mai saukin gaske, kullum in tsinci kaina a yanayin da zai bata mini kwanciyar hankali da imanina da ma dangantakata da Mahaliccina.”
Matakin da jarumar ta dauka, ya haifar da zazzafar muhawara a shafin Twitter, inda mutane da dama suka  kalubalanci dalilin ‘addini’ a matsayin hujjar yin adabo da harkar fim da ta yi.
Sai dai kuma, akwai wadansu da suka yi ta kare matakin nata, ciki har da Omar Abdullah, tsohon Ministan Lardin Jammu da Kashmir.
Fim dinta da zai fito nan gaba, shi ne ‘The Sky Is Pink’ zai kasance fim dinta na karshe. A cikin fim din, jarumar nan Priyanka ta fito; kuma an tsara fitowarsa wani lokaci cikin shekarar nan.

MUKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Takaitaccen Tarihin Mawakiyar India Falguni Pathak

KALLI HOTUNA DA TARIHIN WANDA YA FARA FITOWA A MATSAYIN JARUMA MACE KAFIN MATA SU SHIGA FILM A TARIHIN INDIA

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN JARUMI RAM CHARAN

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







Source: Aminiya
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user