Thursday 23 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (9) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
BANDA YIN SAƁANI

In makaranta kake da ita uwayen yara suka kawo kuka kan cewar ba kwa ba da aikin gida yin hakan kuskure ne, yi ƙoƙari ka duba maganar da aka yi, sannan ka nuna jin daɗin Ka ga gyaran da suke nema, ka maida musu da magana mai daɗi, kar ka yi ƙoƙarin kau da maganarsu tare da kare kanku da wasu hujjoji marasa kan gado waɗanda a ƙarshe kuma su fahimci cewa girman kai ne zai hana Ka ka karɓi gyarar, dalilin mutum guda sai ku fuskanci matsala a nan gaba.

Lafazi mai Daɗi yayin Mu'amala..

MarubuciBaban Manar Alkasim

Banda wannan ma in mutum ɗan kasuwa ne, ya haɗu da wani mai sayen kaya wanda ya ce masa "Sikelin da kake auna nama (ko lemo) da shi ba ya cika da kyau"  bai dace ya yi gardama da shi ba bare wani ya ankara ya fahimci me suke tattaunawa, don in gardama ta yi nisa yanzu za ka ga mutane sun fara taruwa musu don jin ƙwaƙwab, tun farko kar ya mayar masa da baƙa misali ya ce "Wa'azi ka zo ne ko sayen nama?" Ya yi masa godiya kawai ya ce zai gyara, ya kashe maganar kenan, daganan sai ya yi maza ya bincika don ɗaukar mataki, in ma wancan ya riga ya gaya wa wani a ƙarshe aka sami cewa ba haka ba ne za a ƙaryata shi ne, in kuma shi ne ya dawo zai taras an gyara.

7. Banda saɓani: Masu sana'annan yadda sunayen mu suke daban-daban haka fahimtarmu da rayuwa da ma aƙidun mu na siyasa da na addini suke, wasu 'yan ƙwallo ne sun saba jayayya a kan gaibu, masu ƙwallan na wata nahiya ta Duniya su kuma sunanan suna kallo a talabijin suna tabka muhawara a kan rayuwarsu ko wasansu ko ma abinda suke samu, gardaman takan yi nisa ta yi tsanani yadda mutanen dake son zuwa wurinka in suka ji hayaniya sai su canja layi su wuce, kar kabari a riƙa yi maka wannan gardamar a ofis ko shago ko wurin sana'a, tana ruguza al'amura ta hana mutum samun wasu damammaki.

Haka saɓanin aƙida ta siyasa da 'yan takaran, kar ka yarda wannan hayaniyar ta hana ka hurɗa da wasu nau'in mutane, kai mai sana'a ne kowa kuma naka ne, babban abinda ya kawo ka wurin shi ne nema, kenan mai ba ka ko wanda za ka ƙaru da shi shi ne naka, wasu gardandami ko maida magana wanda zai kora maka abokan hurɗa ba naka ba ne, yi ƙoƙari ka gaya wa kowa abinda yake son ji, sai dai in sana'ar asali ta siyasa ce to wannan kuwa, an zo kamfe ne, ko kuma kana sayar da wasu kaya na addini kana da damar ka tallata abinka yadda ba za ka kori abokan hurɗanka da kanka ba, wasu sam-sam ba sa son yin jayayya a kan abinda ya shafi addini.

8. Ya zaka yi: Wani sa'in akan yi wa mutum tayin banza a wurin sana, ko raina kayansa ko sana'ar da yake yi da gangan, in haka ya faru ya za ka yi? Kwana huɗu kenan da suka gabata na je wurin abokina a makaranta sai na iske wani yana son shiga, kuɗin karatun gaba ɗaya ₦60,000 ne, sai na ji yana cewa "Shi fa ₦30,000 ne kawai zai iya biya". Kuma fa karatun nan gaba yake da digiri, sai abokina ya yi murmushi ya ce "To ko makarantun furamare masu zaman kansu wasu sun wuce hakan." haka dai ya miƙe ya yi tafiyarsa, kawai mai sana'a ya riƙa ƙimanta mutane da yadda suke kawai ya sa haquri a cikin lamarinsa, ba sai ya yi faɗa da abokan hurɗa ba.

9. Mata: Wasu matan kan yi lalle su sha ado na fitan hankali kamar za su gidan biki, alhali iyakarsu Ƙasuwa, suna gama abinda suke so gida za su dawo, wasunsu suna da manufa, mai sana'a in ya ga wannan kwalliyar ga murmushi da daɗin murya shikenan an saye shi an biya, ya kalli kudinsa kenan, kar ka yarda a ja ka da magana ka shiga wata sabgar, tsaya a matsayinka, ba abinda yake gaban ka sai sana'arka, ba ado ba ko me mace za ta yi saurare ta kawai ka ba ta irin amsar da ta dace, duka dai magana ce kan lura da abinda za a furta, da yadda za a furta shi.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (7) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (8) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (10) Cikin Sauki

10. Banda ɗaga Murya: Wani sa'in za ka taras da mutum ba fushi ya yi ba ba kuma gardama yake yi da wani ba, amma muryan nan tasa sama, ka yi ƙoƙari ta dawo dai-dai da yadda masu mu'amalla da kai suke buƙata, in mata ke gabanka kar ka riƙa ƙoƙarin jansu da hira ko kusantar su, in har za ka yi za su gane, ba dole ne gobe su dawo wurin ka ba, in maza ne kar ka riƙa tambayar su kan sana'o'insu ko harkar da ba ta shafe ka ba, kowa ka yi mu'amalla da shi kawai kan abinda ya zo da shi da kuma abinda yake nema, ka yi iya ƙoƙarinka yadda zai dawo gobe da kansa saboda jin daɗin yadda ka yi mu'amalla da shi, ban hana ka neman budurwa ba amma komai da mahallinsa.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user