Thursday 30 January 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (11) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
KARATU

Duk wani mai son cin nasara a rayuwa dole ya yi karatu, kodai ya yi na takarda da biro ko kuma ya yi na rayuwa, wanda duk ka ji ya ce "Ba dole sai mutum ya yi karatun boko zai zama wani abu ba" maganarsa haka take, amma wanne irin karatu ne ya zarce na zaman duniya? Ai ita duniya gaba ɗayanta makaranta ce, jami'a ce da take da sassa daban-daban, duk sashin da mutum yake son ya shiga zai samu, da za ka ɗauki mutane guda biyu; wani ya bi layin boko, wato furamare har zuwa jami'a a ƙarshe ya sami abin kansa, za ka taras wani ya fara da ƙaramar sana'a ne, ya bari ya koma wata, ko kuma ya ƙawata ta, za ka ji ya sha wahalhalu iri kaza kafin ya isa wuri kaza, duk waɗannan da kake gani karatu ne bambancin hanya ne kawai.

Ilimi Maɓuɗin Nasara a Rayuwa..

MarubuciBaban Manar Alkasim

Mu a zamanance muna ɗaukar wanda ake ganin kamar ya dan fi sauƙi ne, wato shiga a ji, shi ɗin ma ana ƙoƙarin goge ƙwaƙwalwar yaro ne tun yaranta yadda zai iya hararo abubuwan da za su amfane shi a rayuwa, babban dalilin da ya sa aka ƙirƙiro darussan dake buƙatar tunani kenan a azuzuwan yara ƙanana, akan koyar da yaro a ba shi aiki don ya wasa ƙwaƙwalwarsa wajen nemo irin amsar da ake buƙata a rayuwa.

Idan za a tura yaro wurin sana'a shi ma karatu zai yi, sai dai wannan ya fi karkata ne ga aiki, wato karatu ne amma a aikace, zai san kayan aikin gaba ɗaya da yadda ake sarrafa su, muna da injiniyoyi irin su kanikawa, kafintoci, maƙera da magina, waɗannan manya-manyan Injiniyoyi ne amma ba su san haka ba, saɓanin waɗanda suka je makaranta, sau da yawa za ka taras waɗanda suka yi karatun boko ba su kai waɗanda suka yi a aikace ba, amma da ka ce Injiniya sun san da su kake yi ba waɗancan ba, sun yarda da kansu sosai koda kuwa ba abin a ƙasa, sai su fara bin hanyoyin da za su cimma burinsu, cikin ikon Allah sai ka ga sun sami biyan buƙata a dan ƙaramin lokaci.

Waɗanda suka faro ta sana'a sukan ɗauka cewa na abinci kawai suke nema, wato abinda za su ci da iyali, duk kuwa da cewa bakanike karar abin hawanka kawai zai ji ya ce maka kaza ya lalace, in ya hau ya ce maka sai ka canza kaza, in ya buɗe ya ce maka ba za ka jima ba za ka canza kaza, wannan in ba karatu ba meye? Sai dai babu tsari ne na mataki, babu wata takarda da za ta ba da shedar cewa tabbas mutum ya ƙetare mataki na kaza don haka ya zama cikakken Injiniya, sai ya ɗauki kansa a kan cewa shi ba injiniyan ba ne, ko ka ce injiniya in ba an saba kiransa ne ba ba zai waiga ba, da wahala ka ga ya faɗaɗa tunaninsa a kan fannin da yake ciki har ya fara saka wa a ransa zai iya ƙera jirgin sama.

Galibin waɗanda suka fara sana'a a aikace sun ta'allaƙa ne da motsa jikinsu wajen koyon abinda za su riƙe rayuwarsu da iyalinsu kawai, akwai ƙarancin tunani wurin hararo sabbin abubuwa waɗanda za su bunƙasa sana'ar, ko ƙirƙiro wasu sabbin na'urori da kansu waɗanda za su sauƙaƙe musu ita, shi ya sa nake ganin wanda ya kama sana'a kuma ya shiga makarantar ya fi kowa sanin kanta, kamar yaron da ya girma a cikin bariki ne daga bisani ya shiga soja.

Yanzu kai da ka fara kasuwanci a gaban babanka ko kantinsa dole ka san irin kayan da mutane suka fi so, ka san nau'in da suke buƙata, da lokutan da suka fi zuwa sayayya, a ɗaya hannun dole ka iya lissafi irin na rayuwa, wato ka riƙa gamsar da su ta wurin cinikayyarsu, misali mata masu ciniki, kayan da ake sayarwa a Naira 15 sai ka bar shi 13.5 ɗan abinda ka rage 1.5 ne kawai, akan ɗan wannan ragin mace za ta iya takawa daga wuri mai nisa ta zo wurinka, to bare ƙaramin yaron da aka aika, sai ka sayar da guda 10 wanda ya ƙi rage nasa bai sayar da 4 ba, in ka duba sai ka ga ka mai da kuɗin ka har ka sami ribar da shi bai samu ba.

Kawo irin kayan da mutane ke buƙata kowa na yi, amma lissafin sauƙaƙe kaya don jawo mutane da yawa wani abu ne da yake buƙatar lissafi bayan dogon tunani, galibi waɗanda suka hau sana'a a sama ba su cika irin wannan lissafin ba, in aka yi rashin da ce da mai sayar da kayan gwari sai ka ga ya ruɓe an zubar, a maimakon a sauke kuɗin ya ƙare a sake kawo wani ya ƙare a ɗauko wani nan da nan, ta kowani ɓangare ka bi karatu na ba da gudummuwa gwaggwaɓa wajen cin nasara a rayuwa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (9) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (10) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (12) Cikin Sauki

Ba ƙoƙari muke mu ce wanda bai yi karatu ba ba ya cin nasara, manufar ita ce in aka haɗa ɓangarorin guda biyu an fi samun sauƙi wajen isa ga buƙatun mutum na cin nasara a rayuwa, nakan ga uwaye da dama sukan sa yaransu a makaranta, kuma suna tilasta su tsayuwa a wuraren aikin hannu don su sami sana'a, wani zai gaya maka cewa tun yana sakandare shi ya ɗauki nauyin karatunsa, na ga wani ɗan bumburutu kwanannan da yake gaya min cewa yana karatu ne a jami'a, yana karanta Biochemistry, yanzu yana tara kuɗin makaranta ne, irin wannan da wahala ka ga ya sadaukar da karatunsa a banza, ya fi kowa sanin irin wahalar da ya sha.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user