Thursday 30 January 2020

Karanta Hadaddun Kalaman Soyayya Daga Saurayi Zuwa Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga
DAGA ZUCIYA ZUWA GA ZUCIYA

Salam ya ke muradina,
Da safe na antayo ƙauna,
Na bayyana sirrikan raina,
Gare ki ina makwancina,
Zo amsa min cikin son rai.

Rayuwar Masoya

Marubuci: Ibrahim Garba Nayaya

Abar sona abar sona,
Abar ƙauna abar ƙauna,
Abar marari a rayina,
Yau ga ni da so cikar ƙauna,
Cikar buri cikar komai.

Gare ki masoyiya tawa,
Ki ji ni da zantukan baiwa,
Na ƙaunar nan da ba tsaiwa,
Cikin mararin cikar sowa,
Na bayyana baitukan so dai.

Idan na gane ki don ƙauna,
Na manta abin da ke raina,
Cikar buri ki zo guna,
Ki amshi buƙatuna,
Ki share min duhun komai.

Ranar wanka Bahaushe de,
Ya ce cibi waje buɗe,
Nufinsa a wangame buɗe,
Kowa ya gano ido buɗe,
A san shi a san kalar komai.

Kin san so ba a mai yarfe,
Ba a ƙyamar tuwon safe,
Zoben so ba a sa ƙarfe,
Burina na tattaro lefe,
Na kai ki garin da ba kome.

Kin san so ba a mai kulle,
Gararinsa yawa na 'yan talle,
Shuhurarsa a zuciya zille,
A ganta a fuska ba kyalle,
A san ya zarce duk komai.

Idan na taho a motata,
Cikin tafiya ta ƙasaita,
Idan na gane ki 'yar auta,
Kina tafiya ta ƙasaita,
Na manta batu na tukin dai.

Kalarki daban a mataye,
Sunanki daban na 'yar yaye,
Sautinki daban a Karaye,
A soyayya ana maye,
A sonki ko za na yo komai.

Naman da ake kira soye,
A cakuɗa kafi zabaye,
A sa naman a sa maye,
A sa gishiri a yo soye,
A so haka duk ake komai.

Maimaita aji fa sai dolo,
A so kam ba a son gwalo,
Ba a kome cikin salo,
Jifa kam sai da ɗan kwallo,
A so ba a barin komai.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA KALAMAN BADA HAKURI A SOYAYYA 

KARANTA KALAMAN SOYAYYA MASU DADIN GASKE DA RATSA JIKI

KARANTA TSANTSAR KALAMAN SOYAYYA 

Baitin ƙarshe na ce santsi,
Ya ɗebi mutum ya yo watsi,
Ya farfasa kai ya yo rotsi,
A soyayya a bar kutsi,
Aure a gare ki ne komai.

Ni Nayaya na ce ki dube ni,
Ki min kallon da ba raini,
Da zai mai she ni ɗan birni,
Na sa kaya na sa rawani,
Na so domin na zam komai.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user