Thursday 30 January 2020

MARYAM SANDA SHARI’AR ALLAH TA’ALA KO CONSTITUTION??

Tura Wannan Zuwa Ga
Babu buƙatar nayi dogon sharhi akan lamarin saboda lamarin ba ɓoyayyen al’amari bane ba. Dalilin rubutun kawai shi ne mu rarrabe aya daga tsakuwa akan masu danganta hukuncin da aka yankewa Maryam a jiya da shari’ar musulunci, da kuma masu ganin tausaya mata ma laifi ne.

Maryam Sanda Tayi Kururuwa Lokacin da aka yanke mata Hukuncin Kisa..

Marubuci: Mujahid Ahmad Muktar

Da farko Ina son mutane su fahimci cewa shari’ar Maryam babu abunda ya shafi musulunci da ita, tun daga farkonta kuwa har zuwa ƙarshenta.

Maganar gaskiya ma ita ce babu wata kotun Shari’ar Musulunci a Nigeria da take da hurumin sauraren shari’ar gaba ɗaya ma.

Laifin da ake tuhumar Maryam da shi Capital offence ne, capital offence a dokar ƙasa shi ne duk wani laifin da hukuncin da shari’a ta tanadar masa a ƙarshen sa hukuncin kisa ne Idan kotu ta tabbatar da laifin mutum. Kotunan jahohi (High  Courts) da kuma kotun jaha ta tarayyah (FCT High Court) sai kuma wasu keɓaɓɓun lokutan (Federal High Court) kaɗai suke da cikakken hurumin sauraren ƙara makamanciyar wannan.

Gwamnatin Jaha ko ta Tarayyah kuwa kaɗai ke da ikon shigar da ƙara ƙarƙashin ikon Attorney General na Ƙasa ko na Jaha. Idan anyi hukunci kuwa Gwamnatin dai kaɗai ke da ikon daukaka ƙara, ba ko ‘yan uwan wanda aka kashe ba. Saboda laifin a Gwamnati aka yiwa shi ba ‘yan uwa ko iyayen mamacin ba kaɗai.

Dokar ƙasa tafi tsanani a abunda ya shafi kisan Kai  fiye da Shari’ar Allah TA’ALA, ba kamar abunda ya shafi zina bane ba, da a wasu ɓangarorin ƙasar ba’a shaida shi a matsayin laifi ba ma, ballantana a tanadar masa da hukunci.

Abunda Mu musulmai nake son mu gane shi ne, da ace shari’ar musulunci akayi amfani da ita akan Maryam Wallahi da ta daɗe a gida tana abunda zai fishsheta, tunda ‘yan uwan mamacin sun yafe mata tuni.

A shari’ar Musulunci ‘yan uwan wanda aka kashe idan shari’a ta tabbatar da laifin wanda yayi kisan suna da zaɓuka guda 3 ;

1. Zasu iya yafewa wanda yayi kisan kwata-kwata babu diyyah akansa, sakinsa  kawai za’ayi.

2. Zasu iya neman diyyah Idan dangin sa sun biya a sake shi.

3. Zasu iya neman a tabbatar masa da hukuncin shari’ar Allah TA’ALA kawai akansa (kisa) babu yafiya, babu kuma karɓar diyyah.

Haƙƙin Allah TA’ALA na azumin kaffara 60 kuwa baya sauka akan mai laifin a cikin kowane irin zaɓi da ‘yan uwan mamacin suka ɗauka.

Sannan ina son masu kiraye ga Maryam akan kar ta ɗaukaka ƙara kuwa su sani, Allah TA’ALA da Maryam Sanda su kaɗai suka fi mu sanin gaskiya a Cikin lamarin, ita ta kashe shi, ba ita ta kashe shi ba, sai Allah sai kuma ita.

Shari’a kawai zatayi amfani da abunda yaje mata gabantane a matsayin shaida ta yanke hukunci da shi, Ana kuma iya samun akasi saɓanin tunanin mu ba ita ta kashe shi ɗin ba kamar yadda muke tabbatar mata da laifin.

Sannan ina son mutane su san da cewa ƙalubalantar aikata laifi ya sha bamban da ƙalubalantar hukunci.

A. Bani na aikata laifin ba, idan an hukuntani an zalunceni (ƙalubalantar aikata laifi).

B. Hukuncin nan yayi tsanani da yawa, babu adalchi ga wanda ya sanya shi (ƙalubalantar hukunci). (Ni bana ƙalubalantar kowane a cikinsu, amma Ina tausaya mata akan jarrabawar da Allah (S.W.T) yayi mata).

MAKALOLI MASU ALAKA:

Wallahi Zan Auri Maryam Sanda Idan Har aka Yafe Mata Laifin Ta - Abdulwahab Haladu Zarma Hina

KARANTA DALILAI 6 DAKE SA MATA KASHE MAZAJEN SU

KARANTA SHAWARA ZUWA GA MA'AURATA DA MASU NIYYAR YIN AURE

Sannan a yanzu ko Maryam ta ɗaukaka ƙara ba hukuncin Allah TA’ALA take ƙalubalanta ba, kamar yadda na faɗa, babu ruwan musulunci da hukuncin da aka yanke mata, hukuncin da dokar ƙasa ta tanadar take ƙalubalanta, dokar ƙasar ce kuma ta bata zaɓin ƙalubalantar Idan tana ganin akwai kuskure a hukuncin da aka yanke mata.

A shari’ar Allah TA’ALA da ma constitution ɗin da a hukunta mutum 1 bisa kuskure akan laifin da bai aikata ba, gwamma a saki masu laifi da aka tabbatar da laifin su mutum 10. ( a duba wasiƙar Sayyidina Umar zuwa ga Abu ayubal Ansari lokacin da ya naɗa shi Gwamna a Khufa. Wanda constitution ɗin ma kan sa anan ya kwaikwaya).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user