Tuesday 18 February 2020

Karanta Irin Abokin da Yakamata Kayi Rayuwar Ka da Shi

Tura Wannan Zuwa Ga
Annabi (S.A.W) yana cewa "Mutum yana tafiya ne akan ɗabi'ar abokin sa. Don haka kowa a cikinku ya duba yaga da wa ya kamata yayi abota".

Aboki Nagari

Sayyadina Umar Allah ya ƙara masa yarda yana cewa "Babu wata ni'ima bayan ni'imar musulunci data wuce abaka aboki nagari. Don haka duk wanda ya dace da aboki nagari a cikin ku yayi riƙo dashi ƙam".

Imamul-shafi'I Allah ya jiƙan sa da rahama yana cewa"In Allah ya azurta ka da aboki nagari to ka riƙe shi gam da hannunka, Domin samun Aboki nagari abune me wahalar gaske, kuma rasashi abu ne mai sauƙin gaske".

Imam Hasanul Basari yana cewa "Muna son abokan mu nagari fiye da yanda muke son Iyalanmu da 'ya'yan mu".

Domin iyalan mu da 'ya'yan mu suna tuna mana Duniya.

Shi kuma Aboki Nagari yana tuna mana Lahira ne, yace "yana daga Siffar Aboki nagari ya fifita buƙatarka akan tasa buƙatar".

Luƙmanul Hakim yake cewa da ɗansa "Ya kai Ɗana, farkon abunda zaka tsururuta arayuwar ka bayan imani da Allah shi ne Aboki nagari."

Domin aboki nagari tamkar bishiya ce, in ka zauna aƙasanta, sai inuwarta ta lulluɓeka gabarin rana. In ka tsinki ɗan itacenta ta ƙosar dakai daga yunwa.

In har bata anfanar da kai
ba kuma bazata taɓa cutar da kai ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Shin Zan iya Sanin Hakikanin Masoyi na ta Hanyar yi Min Dariya ko Murmushi?

ABOKAI IRI UKU NE A DUNIYA

Shin Ko Abokina Zai Iya Canza Min Halayena Bansani Ba?

Duk aboki nagari zai so wannan saƙo ya isa zuwa ga abokinsa, don ya samu falalar abin da zai zama alkhairi agareshi da sauran al'ummar musulmai baki ɗaya.

GODIYA GA ABOKAINA NAGARI!!!

Ya ALLAH ka haɗamu da Abokai Nagari waɗanda zasu ƙaunacemu saboda Kai, su kuma ƙimu saboda Kai, kasanya su zama sanadiyyar shigar mu Aljanna Fiddausi, kada su zama sanadiyyar Shigar mu Wuta, Ya Allah ka bani Aboki Nagari, kasa in zama nagari da kuma sauran al'ummar musulmai bakiɗaya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user