Friday 3 January 2020

ABOKAI IRI UKU NE A DUNIYA

Tura Wannan Zuwa
Abokai iri uku ne a duniya:

1. Abokin tayi daɗi, abinda ya kawo shi abota da kai domin ya amfana da kai, ranar da yaga babu amfanin zai kama gabansa.

Abokai Iri Uku Ne a Duniya

Marubuci: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

2. Abokin aiki, wannan abota da shi, iya wajan aiki ne da zarar an gama aiki shi kenan sai kowa ya kama gaban sa.

Abokin Aiki

3. Abokin mai daraja mutunci, wanda zai kasance tare da kai, a dukkan mawayacin hali, ko kana da shi ko babu, shi yana kaunar ka saboda Allah kawai, ba domin wani abu na duniya ba.

Aboki Nagari Mai Daraja Mutunci

Wannan irin abokin yana da wahalar samu, idan ka samu irin sa ka riƙe shi da kyau.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA HANYOYIN SAMUN ABOKI NAGARI CIKIN SAUKI

Shin Zan iya Sanin Hakikanin Masoyi na ta Hanyar yi Min Dariya ko Murmushi?

Shin Zan Iya Zama Sanadin Shiriyar Abokina?

Idan za kayi abota kayi da masu hankali domin:

idan baka nan zasu kare mutunci ka.

Idan  basu ganka ba zasu nemeka.

Idan ka samu zasu tayaka murna.

Idan kayi kuskure zasu gyara maka.

Idan za suyi addu'a ba zasu  manta da kai ba.

Idan baka da lafiya zasu duba ka suyi maka addu'a.

Idan ka shiga wani hali zasu nuna damuwa da alhini.

Idan sun ganka suna murna.

Idan kayi kuskure za su yi maka gyara, cikin hikima.

Idan za a cuce ka zasu taimake ka.

Idan ka mutu zasu yi maka addua, kuma su taimaki iyalanka a bayanka.

Wanda ya rasa abokai na gari yayi asara.

Shin muna da irin waɗannan abokan?

Allah ka bamu abokai nagari Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user