Saturday 29 February 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (16) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
SABON KARATU

Ba wanda zai ci nasara sai ya gaya maka irin wahalhalun da ya sha, da irin gulaben da ya tsallake kafin ya kai ga biyan buƙata, a lokacin da ka ɗauko kayan sayarwa ya yi kwantai saboda rashin kasuwa ko abubuwa suka runcaɓe a wurin aiki, ko ka yi aure amma kullum cikin tashin hankali a maimakon a sami kwanciyar rai, ko ka fara neman auren sau uku ana gaya maka cewa an ɗaura da wani, duka dai abubuwa ne munana, kar mutum ya taɓa zaton cewa shi kenan duniya ta ƙare daga wannan lokacin, koda mace ce ta yi aure mijin ya musguna mata ya cutar da ita iya cutarwa wannan bai nufin duk maza haka suke, akwai namijin da yake ji kamar ya haɗiye matar, duk motsinta sai ya ji shi a zuciyarsa.

Ka koyi darasi dangane da rashin nasarar Ka...


MarubuciBaban Manar Alkasim

Abinda ya dace ta yi anan shi ne ta sami wani sabon karatu na yadda za ta tafi da sabon mijinta mai zuwa, akwai wani ɗan kasuwa da ya yi babban shago yana kai ƙudinsa banki, wata rana ya tara kuɗin makwanni da dama don ya kai banki sai aka yi wuta cikin dare, ta cinye shagon da abinda yake ciki, mutumin ya yi kamar zai zautu, daganan durƙushewarsa kenan ta har abada, amma fa akwai maƙwabtansa Allah kaɗai ya san asarar da suka yi su ma, in ma sun faɗi to ni ban sani ba, dukansu sun dawo suka gyara shagunansu suka faro daga farko kamar yadda suka yi a baya, Allah ya taimake su ga shi komai ya koma tarihi.

Akwai wata mata da maigidan ya rasu ta ƙi aure tana faɗin ita sai mijinta na farko, tana ganin in ta sake aure to fa a aljanna mijin baya ɗin nan da shi za ta rayu, don haka ta ce ba za ta sake aure ba, an yi da ita har aka gaji ta ce ita kam ba ta ba aure, amma a ƙarshe bayan shekaru da dama ta yi auren, kai da ganinta ka san akwai bambanci, ta yi kyau ta ƙara haske, irin faɗace-faɗacen da aka san ta da shi duk ta daina, ga alama ta sami natsuwar zuci, wata kuwa cewa ta yi ba za ta yi auren ba a dalilin abinda ta gani a tsakanin mahaifanta uwa da uba, duk waɗannan in mun haɗa su karatu ne, kai daga lokacin za ka fara tsara naka, don kauce wa abinda ya faru a baya.

Na ga wani mutum da aka shiga shagonsa aka yi masa satar kuɗi dubbai kuwa, shi kansa ba ya son faɗin adadin don kar a ce dama yana da wannan kuɗin? Bai ce shikenan ya daina sana'ar ba, sai ya sa aka yi masa waldar ƙarafuna a gaban shagon yadda ba za a iya shiga a saci wani abu ba nan gaba, wani shima ya sa aka yi masa irin yadda ɓarayi ba za su iya buɗe kwanon shagon su shiga su yi masa ɓarna ba, duk lokacin da mutum ya sha wahala haƙiƙa wani sabon karatu ne yadda zai kiyayi gaba, ba wai ya takura kansa ya yi ta tunanin irin asarar da ya yi a baya ba, wanda in bai yi sa'a ba ma ya kai shi ga hawan jini.

In ta sama ɓarayi suka shiga maka shago kai ma yi walda kawai, in wuta ce ta shigo ta ƙone maka kaya yi nazarin ɓarakar da aka samu sauran ka bar wa Allah, in muguwar mace ka aura a dalilin rashin binciken tarbiyarta ba cewa za ka yi ba ka sake aure ba, gano sakacin da ka yi kawai, nan gaba kar ka nemi auren sai ka bincika don kauce wa abinda ya faru a baya, in gwari ka saya ka yi muguwar faɗuwa, yanzu ka canja salon sayen ko salon ajiyewar, da binciken kasuwa da yadda za a tafiyar da ita, amma ba shakka dawowa a naɗe hannu ana tunanin irin asarar da aka yi ba abinda zai haifar sai cutar damuwa da hawan jini.

Sake miƙewa kawai ka kuma gwada, wanda ya ba ka a baya yananan in ka roƙe shi zai kuma ba ka, ba abinda yake so kamar a roƙe shi, to tsaya cikin dare ka sha mamaki, ana maganar shugaban ƙasar Nigeria na yanzu, wato Janar Buhari, ya shiga siyasa ya sha ƙasa, ya kuma komawa bai samu ba, na ji wani na cewa in har bai samu ba a wannan karon shikenan ya haƙura kawai ba shi ba mulkin Nigeria har abada, aka yi zaɓen kuma bai samun ba, a karo na gaba sai ga shi Allah ya tabbatar masa, ina ganin duk faɗuwar da aka yi ba a rasa karatun da za a yi don dai a ci ribar gaba, ƙarshe sai da aka haɗa jam'iyyun haɗaka, cikin ikon Allah yau dai shi ne shugaba, da ya yi la'akari da irin asarar da ya yi a baya ya watsar da maganar siyasa da zaɓe ƙila da bai sake tsayuwa takarar ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (13) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (14) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (15) Cikin Sauki

To a yau ka tsaya takarar ma ya aka ƙare bare ba ka nuna kana so ba? Dole sai ka shigo sannan a yi da kai, shi ɗin ma za a hana ido barci, a kashe kuɗi a yi kamar ba za a mutu ba, na sami labarai da dama masu alaƙa da wannan batun, akwai wata mata sai da ta yi aure shida kafin ta sami inda ranta ya natsu, ko unguwa ba ta fita bare yaji ko ta bar gidan gaba ɗaya, zama ya yi daɗi kenan, dama haka ake so, za a haɗu da rashin jin daɗi amma a jure a ci gaba, haske yana gaba da izinin Allah.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user