Friday 28 February 2020

Karanta Kissar Wani Mutum da Ya Saba ma Allah Tsawon Shekaru Arba'in

Tura Wannan Zuwa Ga
An ruwaito cewa zamanin Annabi Musa, Alaihis salam, fari (rashin ruwan sama) ya samu Bani Isra'ila, sai suka taru su dubu saba'in ko fiye da haka suka je wurin Annabi Musa, suka ce: "Ya wanda Allah ya yi magana da shi, ka roƙa mana Allah Ya shayar damu ruwan sama". Sai Annabi Musa ya tashi ya fita tare da su zuwa filin dake wajen gari.


Mu tuba zuwa ga Allah


Marubuci: Isah Ade

Daga nan Annabi Musa Alaihis salaam, ya ce: "Ya Ubangiji ka shayar damu ruwan sama, ka yaɗa RahamarKa a gare mu, ka tausaya mana saboda dabbobi da ƙananan yara da suke cikin mu da dabbobi da tsofaffi".

Annabi Musa Alaihis salaam ya ci gaba da cewa" Yaa Allah kar ka haramta alherin da ke wurin Ka, saboda laifinmu".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa a cikin ku akwai wani bawa shekara arba'in yana saɓa mun, ku umurce shi ya fita daga cikin ku, domin sabida shi na hana ku ruwa".

Sai Annabi Musa ya ce: "Yaa Allah ni mutum ne mai rauni, kuma muryata ba zata isa ba saboda yawan su ya kai dubu saba'in ko fiye da haka. Sai Allah ya ce da shi kai dai ka yi kira ni ne mai ikon isarwa".

Sai Annabi Musa (A.S) ya juya yana kira cikin mutane yana cewa: Ya kai wanda ka yi Shekaru arba'in kana saɓa ma Allah, ka fita daga cikin mu, domin saboda kai aka hana mu ruwan sama.

Lokacin da wannan bawa ya duba hagu da daman shi bai ga wanda ya fita ba sai ya fahimci lallai shi ake nufi, sai ya faɗi a cikin zuciyar shi "Idan na fita a cikin waɗannan mutane shi kenan asirina ya tonu, kuma idan na zauna za a hana su ruwan sama. Sai ya shigar da kansa cikin rigar shi yana mai nadama akan munanan ayyukansa yana cewa, Yaa Allah na saɓa maka tsahon shekara arba'in amma ka yi mun jinkiri baka kama ni ba, to yanzu gani na zo maka a matsayin mai ɗa'a don haka Yaa Allah ka karɓe ni".

Wannan bawan Allah bai gama magana ba sai ga sama ta haɗa hadari kuma Allah Ta'ala Ya saukar da ruwa.

Sai Annabi Musa Alaihis salaam ya ce: "Yaa Allah ga shi Ka shayar damu alhalin babu wanda ya fita daga cikinmu".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa na shayar da ku ne saboda bawan da ya hana ni in shayar da ku, domin ya tuba ya dawo gare ni.

Sai Annabi Musa ya ce:" Yaa Allah ka nuna mun wannan bawa mai ɗa'a kuma mai tuba?".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Ban tozarta shi ba alhalin yana saɓa mun sai yanzu da ya tuba zan tozarta shi?".

Domin ganin inda aka ciro kissar za a iya duba littafin قصص التائبين na فضيلة الشيخ محمود المصري.

Allah Ta'ala Ya bamu ikon tuba daga zunuban mu kuma Ya gafarta mana Amin .

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user