Showing posts with label Kissoshin Annabawa da Salihan Bayin Allah Nagari. Show all posts
Showing posts with label Kissoshin Annabawa da Salihan Bayin Allah Nagari. Show all posts

Monday, 23 March 2020

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Ku Sani Dangane da Cutar Coronavirus

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Ku Sani Dangane da Cutar Coronavirus

Babban Malamin addinin musuluncin nan, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo (Allah Ya kara masa lafiya da albarka) ya ja hankulan al'ummar musulmi dangane da cutar nan ta sarƙewar numfashi (Covid 19) da ta addabi duniya a halin yanzu.

Tataccen Bayani Akan Cutar Sarƙewar Numfashi (CORONAVIRUS) A Mahangar Musulunci

Babban Malamin ya gabatar da wannan Jawabi ne a Majalisin sa da ya saba gabatar da karatu a dukkan ranakun Laraba, a Masallacin Cibiyar Imamul Bukhari dake Unguwar Rijiyar Zaki a cikin birnin Kano.

Ga bayanin da Babban Malamin ya gabatar a taƙaice:

Zan yi amfani da wannan dama kafin mu fara karatu domin tunatar da 'yan uwa musulmai a kan yanayin da duniya take ciki a halin yanzu na afkowar cutar nan da ake kira da (Corona Virus).

Mu duba mu gani yadda wannan 'Yar ƙaramar ƙwayar halitta ta cuta, wacce ko da abin hangen nesa (Microscope) sai an ƙura ido sosai ake iya ganin ta, amma gashi ta mayar da kowa gida, ta tayar da hankalin duniya, har ƙasashe masu tinƙaho da ƙarfin kimiyya da karfin tattalin arziki, da cigaba, hankulansu ya tashi! Lissafinsu ya birkice, duk wani abu da suke tunƙaho dashi bai iya amfanar dasu komai ba. Wanda wannan lallai shi zai nuna maka ƙarfin Ikon Allah, zai nuna maka babu wani wanda ya isa gaba ga Allah.

Mu al'ummar musulmi ga matsayar da ya kamata mu ɗauka dangane da wannan cuta:

1. Kallon da musulmi ya kamata su yi wa wannan cuta daban yake da na kafirai, haka a cikin musulmai ɗin ma, mai karanta Alkur'ani da Sunnar Annabi (S.A.W) kallon da zai yi mata daban yake da na wanda ba ya karantasu. Mu musulmi mun yi imani da Ƙaddara, duk wani abu da ya faru to dama can Allah Ya san da shi, kuma bai faru ba sai da ganin damar Allah, saboda babu abinda ke gudana a cikin Mulkin Allah sai da izininsa sai da saninsa. (Malamin ya ambaci ayoyin Alkur'ani mai girma a kan haka).

2. Mu musulmi mun sani cewa ba wannan ne farau ba, ba yanzu aka fara samun irin wannan annoba ba, Allah Ya sha aiko da azabarsa ga al'ummomi da suka gabace mu, saboda sun kangarewa tafarkinSa, sai Allah Ya aika musu da annoba iri daban-daban, misali: mutanen Fir'auna Allah Ya aika musu da annoba iri-iri, kamar annobar ambaliyar ruwa, annobar jini, duk abinda suka buɗe sai suga ya zama jini, annobar fãra da kwarkwata. A ƙarshe kuma Allah Ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Nuhu kafinsu, Allah Ya aiko musu ambaliya ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Lud Allah Ya kifar dasu suka halaka baki ɗaya.

3. Duk da cewa ita wannan al'umma ta Annabi (S.A.W) Allah Yayi alƙawarin ba zai tumɓuketa Ya halakar da ita baki ɗaya ba, idan da Allah Ya so haka ɗin tabbas zai iya, irin waɗannan musibu sun isa shaida a kan haka, to amma Allah sai ya aiko da irin wannan annoba domin jan kunne da kashedi ga bayi. Yayin da annobar tazo kuma bata banbance salihi nagari da na banza, kowa haɗawa take dashi, sai dai tana zama Rahama ga Salihai, azaba kuma ga fanɗararru.

4. Daga cikin darasin da ya kamata musulmi ya lura dashi a kan sha'anin wannan cuta, mu duba mu gani, a lokacin da Ɗan Adam yake tutiya, yake tunƙaho cewa ya mallaki ilimi, ya mallaki ƙarfin tattalin arziki, wasu har suna ganin Allah ma baya yi musu komai, su sun isa, su sune!!! Kwatsam sai ga wata 'yar ƙaramar halitta daga halittun Allah, wacce ido ma baya iya ganinta saboda tsabar ƙanƙantar ta, sai gashi ta baza duniya, ta bazama manyan ƙasashe, tattalin arziki yana ta rushewa, kowa ya firgita. Lalle wannan ya isa wa'azi! Wannan ya isa shaida akan girman Allah da ƙarfin mulkinSa.

5. Mu musulmi mu sani cewa babu abinda zai yaye mana wannan annoba illa kaɗai mu koma ga Allah, mu guji dukkan abubuwanda ke janyo Allah Yayi haka ga al'umma, kamar manyan laifuka, Zinace-Zinace, Zalunci, Ɓarna a bayan ƙasa.

6. Mu sani cewa komawa ga Allah shine matakin farko domin magance wannan annoba, duk wani abu da ba wannan ba ciko ne, amma komawa ga Allah shi ne Jigo. Mu koma ga Allah da yin addu'o'i da yin istigfari.

7. Mu sani cewa lalle babu wata musiba da wuce a jarrabeka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe masallatai, ana hana fitowa sallar Jam'i, har sallar juma'a da yawa daga ƙasashe sun bayarda sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta. Lalle wannan abun tsoro ne! Kamar Allah Yayi fushi da mutane ne yace: Ku fita ku bar min ɗakuna na (Masallatai) tunda ɓarnar ku a bayan ƙasa tayi yawa. Babbar musiba ce a rabaka da ɗakin Allah, a ce babu Umarah, babu Ɗawafi, babu sallar Jam'i, lalle babu musibar da tafi musiba a cikin addini. Tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba ga Allah.

8. Musulunci ya yarda da tsarin killace marasu lafiya, da kuma tsarin kare kai daga cututtuka, musulunci shi ya fara zuwa da irin wannan tsari. (Malamin ya ambaci Hadisi a kan haka) amma kuma a musulunci munyi imani da cewa zama da mai cuta ba shi ke janyo kamuwa da cuta ba har sai idan Allah Ya hukunta haka, cuta a karan-kanta bata da ikon shiga tayi tasiri a cikin mutum sai da ganin damar Allah. ita cutar sababi ce, sababi kuwa baya aiki a karan-kansa sai idan Allah Ya ƙaddara, mu duba mu gani, wuta a al'adarta tana ƙona mutum, amma Annabi Ibrahim da aka jefa shi a wuta sai Allah Ya sa wutar taƙi ƙona shi, mu duba ruwa yana dulmiyar da mutum, amma sai Allah Ya sa Annabi Musa da mutanensa suka taka saman ruwa suka wuce ba tare da sun dulmiya ba, saboda haka ko da abu sababi ne, Allah Yana iya zare sababiyyar yaƙi yin aiki. A musulunci mun sani cewa duk abinda ya sameka ba zai kuɓuce maka ba, duk kuma abinda ya kuɓuce maka ba mai samunka bane. Kamar yadda Annabi (S.A.W) Ya faɗawa Abdullahi Ɗan Abbas.

9. Irin wannan annobar an sha yinta a baya, a lokacin Sahabbai an samu annoba da tayi sanadiyyar rasuwar wasu daga cikin Sahabbai, kamar: Mu'az bin Jabal, da Abu Ubaida bin Aljarrah da sauran su, wannan ya faru a shekara ta (18) bayan Hijra.

Haka nan akwai annobar da aka taɓayi inda tayi sanadiyyar mutuwar 'ya'yan Anas bin Malik kusan mutum saba'in (70), da Ƴaƴan sahabi Abu Bakrata kusan Mutum arba'in (40).

10. Na daga cikin abinda zai magance irin wannan annoba, gujewa aikata Zalunci, danne haƙƙin mai haƙƙi, wajibi ne shugabanni su riƙi yin adalci su guji yin zalunci, domin zalunci sababi ne afkawa irin wannan masifa.

A ƙarshe Malamin yayi addu'a mai ratsa zukata, inda Ya roƙi Allah da Ya yaye mana wannan masifa ba don halinmu ba, Allah Ya dube mu da Rahamarsa da Ludufinsa ya kawo mana agaji.

Waɗannan bayanai an tattaro su ne a taƙaice daga jawabin babban Malamin, mai buƙatar cikakken jawabin sai ya nemi karatun littafin (Alwabilussayyib) darasi na 149.

Marubuci:
Musa Muhammad Dankwano.
Secretary, Dr. Muhd Sani Umar R/lemo Academic Forum.

المنتدى العلمي للدكتور محمد الثاني عمر

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 28 February 2020

Karanta Kissar Wani Mutum da Ya Saba ma Allah Tsawon Shekaru Arba'in

Karanta Kissar Wani Mutum da Ya Saba ma Allah Tsawon Shekaru Arba'in

An ruwaito cewa zamanin Annabi Musa, Alaihis salam, fari (rashin ruwan sama) ya samu Bani Isra'ila, sai suka taru su dubu saba'in ko fiye da haka suka je wurin Annabi Musa, suka ce: "Ya wanda Allah ya yi magana da shi, ka roƙa mana Allah Ya shayar damu ruwan sama". Sai Annabi Musa ya tashi ya fita tare da su zuwa filin dake wajen gari.


Mu tuba zuwa ga Allah


Marubuci: Isah Ade

Daga nan Annabi Musa Alaihis salaam, ya ce: "Ya Ubangiji ka shayar damu ruwan sama, ka yaɗa RahamarKa a gare mu, ka tausaya mana saboda dabbobi da ƙananan yara da suke cikin mu da dabbobi da tsofaffi".

Annabi Musa Alaihis salaam ya ci gaba da cewa" Yaa Allah kar ka haramta alherin da ke wurin Ka, saboda laifinmu".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa a cikin ku akwai wani bawa shekara arba'in yana saɓa mun, ku umurce shi ya fita daga cikin ku, domin sabida shi na hana ku ruwa".

Sai Annabi Musa ya ce: "Yaa Allah ni mutum ne mai rauni, kuma muryata ba zata isa ba saboda yawan su ya kai dubu saba'in ko fiye da haka. Sai Allah ya ce da shi kai dai ka yi kira ni ne mai ikon isarwa".

Sai Annabi Musa (A.S) ya juya yana kira cikin mutane yana cewa: Ya kai wanda ka yi Shekaru arba'in kana saɓa ma Allah, ka fita daga cikin mu, domin saboda kai aka hana mu ruwan sama.

Lokacin da wannan bawa ya duba hagu da daman shi bai ga wanda ya fita ba sai ya fahimci lallai shi ake nufi, sai ya faɗi a cikin zuciyar shi "Idan na fita a cikin waɗannan mutane shi kenan asirina ya tonu, kuma idan na zauna za a hana su ruwan sama. Sai ya shigar da kansa cikin rigar shi yana mai nadama akan munanan ayyukansa yana cewa, Yaa Allah na saɓa maka tsahon shekara arba'in amma ka yi mun jinkiri baka kama ni ba, to yanzu gani na zo maka a matsayin mai ɗa'a don haka Yaa Allah ka karɓe ni".

Wannan bawan Allah bai gama magana ba sai ga sama ta haɗa hadari kuma Allah Ta'ala Ya saukar da ruwa.

Sai Annabi Musa Alaihis salaam ya ce: "Yaa Allah ga shi Ka shayar damu alhalin babu wanda ya fita daga cikinmu".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Yaa Musa na shayar da ku ne saboda bawan da ya hana ni in shayar da ku, domin ya tuba ya dawo gare ni.

Sai Annabi Musa ya ce:" Yaa Allah ka nuna mun wannan bawa mai ɗa'a kuma mai tuba?".

Sai Allah Ta'ala Ya ce: "Ban tozarta shi ba alhalin yana saɓa mun sai yanzu da ya tuba zan tozarta shi?".

Domin ganin inda aka ciro kissar za a iya duba littafin قصص التائبين na فضيلة الشيخ محمود المصري.

Allah Ta'ala Ya bamu ikon tuba daga zunuban mu kuma Ya gafarta mana Amin .

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


Monday, 25 November 2019

Shin Zan Iya Zama Sanadin Shiriyar Abokina?

Shin Zan Iya Zama Sanadin Shiriyar Abokina?

Lallai kai ba ka isa ka shiryar da wani ba, sai dai kayi iya ƙoƙarinka wajen tunatarwa da jan hankali ga 'Yan uwa musulmai domin tunatarwa yana amfanar wa.

Allah ne yake Shiryar da Wanda Ya So

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Sau da dama wasu daga cikin ma'abota da'awa wajen da'awarsu ga bayin ALLAH su kan sanyawa kansu ƙunci har ma wasu sukan kauracewa da'awar a dalilin sunyi kira ba amsa ba, Toh kada kayi bakin ciki ka roka musu shiriya awajen ALLAH (SWT) domin ka sani baka isa ka shiryar da wani bawa zuwa ga hanya madaidaiciya ba face sai idan ALLAH ne ya shiryar dashi.

Domin lallai ALLAH (SWT) shi yake shiryar da wanda ya nufe shi da falalarsa kuma yake batar da Wanda ya riske shi da adalcinsa.

Kuma ALLAH (SWT) Ya fada acikin Alkur'ani Maigirma cewa: "Lallai kai ba ka shiryar da wanda kake so, sai dai ALLAH ne yake shiryar da wanda yake so." [Suratul Kasas aya ta 56]

Kuma ALLAH (SWT) ya fada acikin Alkur'ani Maigirma cewa: "Sannan Wanda ALLAH Yayi nufin shiryar dashi sai ya buda kirjinsa ga musulunci, kuma wanda yayi nufin ya batar dashi sai ya sanya kirjinsa ya zama mai kunci matsatstse, kamar yana takawa zuwa sama, kamar haka ne ALLAH yake sanya kazanta ga wadanda basa yin imani." [Suratul An'am aya ta 125]

Wannan Ayoyin suna kara tabbatar mana da cewa lallai ALLAH (SWT) shine mai shiryarwa ga Wanda yaso.

Hakanan Annabi (ﷺ) Yace: "Wanda ALLAH Ya shiryar dashi babu mai batar dashi, kuma wanda ya batar babu mai shiryar dashi."

Mutum Bai Isa Ya
Yahiryar da Wanda yake So ba

Don haka duk sonka da kaunarka ga wani naka ko dan'uwanka musulmi yabi hanyar shiriya bazai taba bi ba face sai idan ALLAH ne yaso, domin daga cikin Annabawan ALLAH akwai wanda mahaifinsa akwai wanda matarsa ne akwai wanda dansa ne amma basu bi wannan hanya ta shiriya ba saboda ALLAH (SWT) bai tabbatar da hakan ba.

Haka kuma mafificin Halitta Annabi (ﷺ) Ya sowa Bappansa Abu-dalib ya cika da wannan shiriya ta addinin ALLAH yayin mutuwarsa amma ALLAH (SWT) bai bashi sa'ar amsawa ba.

Kamar yadda yazo acikin ingantaccen Hadisi daga Musayyab daga Babansa yace: "Lokacin da mutuwa tazo wa Abu-dalib sai Manzon ALLAH (ﷺ) yazo masa kuma awajen akwai Abdullah Dan Abu-umayyah da Abu-jahl, sai yace masa: "Ya Bappana kace LA'ILAHA ILLALLAH, Kalma ce wacce zanyi maka hujja da ita a gaban ALLAH." Sai suka ce masa: yanzu ka bar addinin Abdul-mudallib?. Sai Annabi (ﷺ) ya maimaita masa, su ma suka maimaita masa, karshen abunda ya fada shine: yana kan addinin Abdul-Mudallib, yaki cewa La'ilaha illallah. Sai Annabi (ﷺ) Yace:

"Wallahi zan roka maka gafara matukar ba a hana ni ba."

Sai ALLAH Mai girma da buwaya ya saukar da ayar da take cewa: "Ba ya kasancewa ga Annabi da wadanda suka yi imani su nemar wa mushirkai gafara." [Taubah aya ta 113]

Kuma ya saukar game da Abu-Dalib ayar da take cewa: "Lallai kai ba ka shiryar da wanda kake so, sai dai ALLAH ne yake shiryar da wanda yake so." [Suratul Kasas aya ta 56] [Bukhari 1360 da Muslim 24 suka ruwaito]

Tarihi ya bayyana mana irin kulawar da Abu-Dalib yayi ga Annabin ALLAH da gudumawarsa ga musulunci amma ALLAH (SWT) bai bashi ikon furta wannan kalma ta "La'ilaha illallah" ba.

Da wannan ya kamata duk mai kira zuwa ga Shiriya zuwa ga hanyar ALLAH ya sani cewa ALLAH ne yake shiryar da wanda yaso kuma Ya sani shima ba wayonsa bane haka kuma ba dabararsa bace ALLAH Ya shiryar dashi ya batar da waninsa ba, sai dai hakki ne akansa yayi kira zuwa ga shiriyar ALLAH kuma ya tunatar kuma yayi addu'a ya roki ALLAH Ya dawwamar dashi akan shiryar, kuma ya shiryar da wadanda suka karkace daga hanyar ALLAH, kada kayi fushi kuma kada kayi bakin ciki, Lallai ALLAH ya kasance mafi sani  ga abunda yafi dacewa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Muhimman Abubuwan da Yakamata Ku sani Kafin ku Fara yin Taimako

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

KARANTA INGANTACCIYAR HANYAR YIN MU'AMALA DA MUTANE

Ya ALLAH ka shirya damu cikin wadanda ka Shiryar bisa hanya madaidaiciya, kuma ka buda kirjinmu ga Musulunci, kuma kada ka sanya mu daga cikin wadanda zuciyarsu tayi kunci kuma ta Matse. (Ameen).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode