Sunday 1 March 2020

ZAN IYA DORA RIBA IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU?

Tura Wannan Zuwa
Tambaya:

Assalamu Alaikum Mallam, dan Allah ina da tambaya, kaman misalin mutum yana baka kuɗi ka sayo mishi abu, wataran ya baka kuɗin ka sayo, wataran kuma sai ka sayo ka kai zai baka kuɗin, shin koya halasta inci riba a wanda yaban kuɗin shi in sayo mai, ko kuwa a wanda na sayo da kuɗina ne kawai zan iyacin riba, banda Wanda ya bada kuɗin shi? Nagode Allah ya ƙara basira.

Zan Iya Ɗora Riba Idan aka Wakilta Ni..


MarubuciDr. Jamilu Zarewa

Amsa:

Allah ya amsa addu'arki ƴar uwa, idan mutum ya wakilta ki, ya baki kuɗi ki sayo masa wani abu, bai halatta ki ci riba da shi ba, sai da izininsa, saboda hadisin Urwatu Al-ja'ady lokacin da Annabi (S.A.W) ya ba shi dinare (1) don ya sayo masa dabbar layya, sai ya sayo akuyoyi guda biyu, ya sayar da ɗaya akan dinare ɗaya, ya zo ma da Annabi (S.A.W) da akuya ɗaya da kuma dinaran da ya aike shi, sai Manzon Allah ya amshe ya yi masa addu'a, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 3642.

Kasancewar Annabi (S.A.W) ya tabbatar da shi akan aikinsa, sai ya nuna hakan shi ne shari'a, don haka idan wakili ya samu ragi ko ya ci riba a cinikayyar da aka wakilta shi ya wajaba ya dawo da ita zuwa wanda ya aike shi.

Idan ya wakilta bai bayar da kuɗi ba, to mutuƙar kuna kasuwanci a tsakaninku ya halatta a ɗora riba, amma in ba kwa yin kasuwanci ba za ki ɗora riba ba, za ki kawo masa abin a kuɗin da ake siyarwa a kasuwa, saidai in ya bada iznin cin riba, saboda wakili amintacce ne a shari'a, wasu malaman suna ganin za ki iya ɗora gwargwadon wahalarki, in bai bada kuɗi ba.

Don neman ƙarin bayani duba Al-mugni na Ibnu khudaamah 5\86.

Allah ne mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user