Sunday 1 March 2020

Shin Mene ne Dalilin da Yasa duk Abinda Na Nema Bana Samu?

Tura Wannan Zuwa Ga
Yana daga cikin abinda bazai taɓa yiwuwa ba, shine kaga waninka ya tafi da rabon da Allah yarubuta zai sameka.

Rabon Ka Naka Ne...

Idan har kaga baka samu abinda kake da muradi ba, to ka tabbata haka Allah yarubuta cewa ba rabonka bane, kuma duk hanyar da zaka bi bazaka taɓa iya samun abinda Allah bai rubuta zaka same shi ba.

Hanyar da kabi ta Haram har kasamu abinda kakeso, da ace ka yi Haƙuri ka bi hanyar Halala zaka same shi saboda rabonka ne Allah yarubuta zaka sameshi.

Ka nutsu kuma kayarda da Allah saboda rabon kwaɗo baya hawa sama, saboda ko ya hau sai Allah ya sauko da shi.

Imam Shafi'ey yana cewa : Ni na san wanina bazai taɓa tafiya da rabona ba, shiyasa na nutsu (ba na tayar da hankali na akan abinda ba nawa bane saboda na san ba rabona bane.) "

HIKIMAR ANAN ITACE

Duk abinda kaga ka samu, to Allah ne yarubuta zaka sameshi, waninka bazai taɓa hanaka abinda Allah yabaka ba, kuma duk abinda kaga baka samu ba, to haka Allah yarubuta bazaka sameshi ba, waninka bazai taɓa baka abinda Allah bai rubuta zaka sameshi ba.

Ya Allah ka azurta zukatanmu da yarda da abinda karaba kabamu ,  Kuma kaƙara tsare mana Imaninmu sannan kasa mucika da kyau da Imani Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user