Wednesday 11 December 2019

ME CE CE KUNYA KUMA TA YA YA AKE GANE MUTUM YANA DA KUNYA ??

Tura Wannan Zuwa Ga
Kunya wata ɗabi'a ce daga cikin dabi'un musulunci wanda ake kwadaitar da musulmi na gari ya siffantu da ita.

Ma'anar Kunya...

Marubuciya: Faridah Bintu Salis

MATSAYIN KUNYA A MUSULUNCI

Kunya a addinin musulunci ɗabi'a ce dake sanya mutum aikata kyawawan ayyuka ababan so ga ma'abocin ta, ta kuma hana shi aikata munanan ayyuka.

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “KUNYA wani rassa ko yanki ne daga cikin Imani.” [Sahihun Nasa'i 5020]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Kunya bata zuwa da komai sai alkhairi.” wani wajen kuma yace: “Kunya dukkanta alkhairi ce.” [Sahihaini]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yace: “Lallai ALLAH mai yawan Kunyane kuma mai son suturtawa ne, yana son suturtawa da kunya.”. [Abu-dawud da Nasa'i]

Manzon ALLAH (ﷺ) Yana cewa: “Yana daga abunda mutane suka riska daga cikin kalaman Annabawan farko, idan baka jin kunya to ka aikata abunda kaga dama.” [Bukhari]

Manzon ALLAH  (ﷺ) Yace: “Lallai kowa ne addini yana da wani hali mai kyau, halin Musulunci shine kunya.” [Muwadda Malik da Sunan Ibn majah]

Ibn Sa'adiy (Rahimahullah) Yana cewa: "Da Kunya ake samun rayuwar imani, wato imani yana rayuwa ne idan akwai kunya acikinsa, da kunya ne bawa yake barin dukkan abunda zai janyo masa zubar da mutumci da matsayi, da kunya ne aka tabbatar da dukkan halaye masu kyau, domin kunya itace tushen dukkan hali mai kyau abun yabo, kuma ita ke korar da dukkan hali mummuna abun zargi.” [Attaudihu wal bayan: 95]

Ibn Uthaymeen (Rahimahullah) Yace: “Kunya wani sifface ko dabi'ace da take sanya mutum ya aikata dukkan abunda zai sanya masa yabo da daukaka da mutunci da matsayi, kuma take hanasa aikata abunda zai zubar masa da matsayi da kima da daraja.” [Sharh Riyadus-saliheen 4/42]

Abu-Tamaam Yace: “Wallahi babu wani alkhairi acikin rayuwa, har ma acikin duniyar baki daya idan kunya ya gushe! Idan har baka tsoron abunda zai je ya dawo, matukar baka da kunya, ka aikata duk abunda kaga dama.”

Ma'anar Kunya...

Wani Magabaci yake cewa: “Duk Wanda kunyarsa tayi Karanci, Toh takatsantsan dinsa zai yi kadan...”

Kunya na da matukar amfani da muhimman ci ga rayuwar dan adam mace ko namiji.

Haƙiƙa mata sune wadanda akafi siffantawa da ɗabi'ar kunya. Sai dai abun takaici ayanzu suna nema su saki wannan ɗabi'a ta kubuce musu a wannan rayuwa badan komai ba sai dan bin rudin duniya da mai halakarwa wato  shaidan.

Ayau mun wayi gari dayawa daga matayen cikinmu da mazajen mu basa jin kunyar Ubangijinsu wajen aikata saɓo kowanne iri ne amma abin takaici zaka samu yana tsoron mutane akan wani aibi nasa.

Hakika rashin kunya alamace ta raunin imani ga ma'abocinta.

Wani daga cikin magabata yana cewa: “imani tsirara yake tufafin sa shine tsoron ALLAH adonsa kuwa shine kunya”

Wani kuma yana cewa: “duk wanda ya mai da tufafin sawarsa ya zamo kunya to mutane baza su ga aibin sa ba.”

Wannan magana tana nusar damu cewa kunya da imani tafiyarsu daya.

IRE-IREN KUNYA: a taƙaice Kunya ta kasu kashi hudu:

1. JIN KUNYAR UBANGIJI: wannan nau'in kunyar shike hana bawa sabawa ubangijinsa. Aduk lokacin da bawa zai aikata mummunan aiki matukar akwai kunya atare dashi to lallai zaiyi gaggawar tuna cewa ALLAH yana ganinsa aduk inda yakasan ce kuma zai tambayeshi akan abunda ya aikata.

2. JIN KUNYAR MALA'IKU: ALLAH (SWT) Yana cewa: “lallai akan ku akwai matsara masu daraja marubuta suna sanin abunda kuke aikatawa.” Ansamu daga sahabbai wani na cewa lallai atare daku akwai wadanda basa rabuwa daku saboda haka kuji kunyar su ku girmama su.

3. JIN KUNYAR MUTANE: Huzaifa bin yaman (RA) yana cewa:  “Babu alkairi ga wanda baiji kunyar mutane ba. Ashe yan uwa kunya alkairi ce.”

MAKALOLI MASU ALAKA:

SHIN KO KASAN ZA KA IYA SABAWA ALLAH AMMA DA SHARUDA GUDA BIYAR?

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

CIKIN WADANNAN MUTANE WANNE IRIN ABOKI NE DA KAI ?

4. JIN KUNYAR KAI: aduk lokacin da mutum zai aikata mummunan aiki dazarar yatuna Ubangijinsa kuma yaji kunyar kansa to lallai zuciyar sa zata nutsu kuma ta tsoraci ALLAH ta hana shi aikata mummuna tayi masa umarni da kyakkyawan aiki.

ALLAH Yasa mu kasance cikin salihan bayi ma'abota jin kunya a duk inda addinin ALLAH yayi mana iyaka (Ameen).

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user