Monday 30 September 2019

SHIN KO KASAN ZA KA IYA SABAWA ALLAH AMMA DA SHARUDA GUDA BIYAR?

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani saurayi ya je wajen Ibrahim dan Adhama, (daya daga cikin magabata), sai ya ce masa zuciya ta tana tunkuda ni zuwa sabo, ka yi min wa'azi.


Wajen Ibada Mafi Daraja

Sai ya ce masa :

Idan ta kiraka zuwa sabawa Allah to ka saba masa amma da sharuda guda biyar.

Sai saurayin ya ce fadi mu ji :

1. Idan za ka sabawa Allah, to ka boye a wurin da ba zai ganka ba.

Sai saurayin ya ce:

Tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za'a yi na boye masa, alhalin babu abin da yake buya gare shi.

Sai ya ce : yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kuma yana ganin ka.

2. Idan za ka sabawa Allah to kar ka saba masa cikin kasar sa.

Sai saurayin ya ce :

Tsarki ya tabbata ga Allah, ina zan je, alhali duka duniya ta sa ce, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kana zaune a saman kasarsa.

3. Idan za ka sabawa Allah to ka daina cin arzikinsa.

Sai saurayin ya ce :

Tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni'imomi daga gare shi su ke, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali yana ciyar da kai kuma yana shayar da kai, yana ba ka karfi.

4. Idan ka sabawa Allah, to idan mala'iku suka zo tafiya da kai wuta, ka ce ba za ka tafi ba aljanna za ka.

Sai saurayin ya ce :

Tsarki ya tabbata ga Allah ai sun fi karfina, kora ni za su yi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar alkiyama ka ce :

ba kai ka aikata su ba.

Sai saurayin ya ce :

tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala'iku masu kiyayewa, sai ya fashe da kuka ya tafi yana maimaita wannan Kalmar ta karshe.

DUBA WADANNAN:

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

KARANTA KADAN DAGA CIKIN MUNANAN HALAYEN DA SUKE CUTAR DA AL'UMMA GABA DAYA CIKIN GAGGAWA

KARANTA LAIFIN ME MALAM DR ISA ALI PANTAMI YAYI WA 'YAN KWANKWASIYYA SUKE KOKARIN HALLAKA SHI?

KARANTA YADDA RAYUWAR AURE TA LALACE A WANNAN ZAMANIN DA MUKE CIKI

SHIN KANA TUNA WADANNAN IDAN ZA KA AIKATA ZUNUBAI ?

ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA KUMA IMANI AMIN.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user