Monday 30 September 2019

KARANTA TAKAITACCEN TARIHI DR ISAH ALI IBRAHIM PANTAMI

Tura Wannan Zuwa Ga
An haifi Maigirma Ministan Sadarwa a Nigeria Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami a ranar 20 ga watan Oktobar 1972 a unguwar Pantami dake Gombe, jihar dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Dr. Isa Ali Pantami

Marubuci: Datti Assalafy

Isa Pantami ya kasance ‘da ga Mallam Ali Ibrahim Pantami, mahaifiyarshi kuwa itace Malama Amina Umar Aliyu.

Ya fara karatun Al-Qur’ani a makarantar Allo kafin daga bisani ya shiga makarantar Firamare ta ‘Pantami Primary School’ inda a nan ne ya samu shaidar kammala karatun firamare, ya kammala karatun sakandire a makarantar Sakandire ta Kimiyya ta ‘Government Science Secondary School, Gombe.

Daga nan ne ya samu shigar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake jihar Bauchi, inda a nan ne ya samu damar kammala karatun Digiri a fannin Fasahar Kwafuta a shekarar 2003 tare da samun Digiri na 2 duk a fannin, a shekarar 2008.

Pantami ya kammala karatun Digirin-digirgir a jami’ar Robert Gordon dake Aberdeen a kasar Sukotlan.

Dr. Isa Ali Pantami

Ya fara aiki a jami’ar ATBU, inda yake koyar da ‘Information Technology’ kafin daga bisani ya koma Jami’ar Musulunci dake Madinah a matsayin shugaban Rubutun Fasaha a shekarar 2014.

DUBA WADANNAN:

Karanta Takaitaccen Tarihin Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN SHEIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI

A shekarar 2016, Pantami ya ajiye koyarwa, inda a nan ne shugaba Muhammad Buhari ya nada shi ya zama shugaban hukumar ‘NITDA’ a ranar 26 ga watan Satumbar 2016.

Ya kasance babban malamin addinin Musulunci na sama da shekaru 20, ya kasance limamin sallah Juma’a a Najeriya da kasar Birtaniya. - Jaridar Punch Newspapers

Yaa Allah Ka karawa rayuwarsa albarka, Ka gafarta wa iyayensa, Ka hada fuskokin su da nashi da namu a cikin Aljannah Madaukakiya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user