Friday 20 March 2020

Karanta Tarihin Asalin Yaduwar Cutar Coronavirus a Duniya

Tura Wannan Zuwa Ga
Yanzu dai sunan Kwarona Bairos bai zama baƙo ba kasancewar ana ta yayata al'amarinta a kafafen yaɗa labarai. Wasu na ganin cewar a wannan karon ne kaɗai aka samu irin wannan cutar, sai dai a binciken da na yi an jima da sanin ta a duniya. 

Covid-19

MarubuciDanladi Haruna

Ita wannan cutar tun  jimawa an san da ita kan cewar tana shaƙe numfashi da haddasa zazzafan zazzaɓi da mura da tari da kuma lalata huhu da hanjin mutum ko dabba. Duk lokacin da aka samu ɓullar cutar sai a yi mata wani laƙabi daban, ta kwanan nan dai ana kiranta Covid-19.

A 2005  wasu ƙwararun likitoci suka yi bincike a ƙarƙashin Dakta Kahn Jeffery. Sun bayyana  a wata mujallar likitoci mai suna, 'The Pediatric Infectious Disease Journal' cewar,  an fara gano cutar Coronavirus a cikin shekarar 1965. Ita wannan an yi mata laƙabi da B814. Daga nan aka yi ta samun ɓullar cutar daga lokaci zuwa lokaci.

Likitocin suka ce daga shekarar 2003 zuwa 2005 an samu ɓullar cutar har sau biyar. Coronavirus ta farko an raɗa mata sunan SARS wadda ta ɓulla a China cikin 2003 kuma ta halaka mutane 22 - 24. Ta biyu an yi mata laƙabi fa NL63 a cikin shekarar 2004 inda ta ɓulla a Netherlands kuma ta kashe mutane 32. Ta uku ma a ƙasar Netherlands ɗin ta bayyana inda ta kashe mutane 33 duk a 2004. Ta huɗu kuma a yankin New Haven ta bayyana cikin 2005 inda ta kashe mutane 34. Ana mata laƙabi da HCoV-NH. Sai ta biyar da ta bayyana a Hong Kong ta halaka mutane 35. Ita ana mata laƙabi da HKU-1.

Haka kuma a tsakanin 2008 zuwa 2019 an samu ɓullar wasu irin Coronaviruses da ake wa laƙabi iri - iri kamar, OC43, 229R,  COVid - 12 da sauransu. Babbar coronovirus daga cikinsu ana kiran ta MERS-CoV watau 'Middle East respiratory syndrome - Coronavirus'.

Likitan ƙasar Masar,  Dakta Ali Mohamed Zaki ya bayyana cewar ana iya samun cutar a jikin raƙuma da aladu da kuma Jemagu. Ya kuma ƙara da cewar ƙwayar halittar wannan cuta yana da girma fiye da sauran ƙwayoyin cuta.

Sai dai da alama Covid-19 ta fi  tsanani kuma ta fi girgiza al'ummar duniya ganin yadda take yaɗuwa da sauri kuma take halaka mutane cikin hanzari. Da alama kuma a wannan karon cutar ta bayyana da ƙarfinta fiye da baya. Kuma da alama kamar ba a yi tanadin taron ta ba.

Wasu al'umma suna ganin da gangan aka ƙirƙiri wannan cutar tun zamanin yaƙin duniya na biyu, sannan aka cigaba da wanzar da ita a lokacin yaƙin cacar baki. Shugabannin duniya suna sane da makami mai guba da Amerika da Rasha suka mallaka, ba abin mamaki ba ne a ce tun asali an ƙirƙiro cutar ne a ɗakin gwaje-gwaje. Haka kuma ba zai zama abin mamaki ba idan mutane da dama sun san da sunanta a baya kafin yanzu da sunan ya zama ruwan dare.

Kuma ba zai zama abin mamaki ba idan an samu wasu marubuta a baya sun yi hasashen afkuwar cutar a shekaru masu yawa. Wannan baiwa ce ta marubuci kamar dai littattafai irin su 1984, GodfatherClass 1999 da sauransu.

Mu dai anan ba abin da za mu ce sai mu roƙi Allah ya kare mu da irin kariyarsa. Ya inganta lafiyarmu ya duba raunin shugabanninmu yadda cutar za ta wuce mu ba tare da kawo mana wafta ba Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user