Monday 15 July 2019

KARANTA MAGANIN BASIR KO WANE IRINE DA YARDAR ALLAH

Tura Wannan Zuwa
Hakika wannan ciwo yajima yana haifar da matsaloli ga ma'aurata, wasu har takankai ga rabuwama gaba daya.

Maganin Basir da Yardar Allah



Wannan dalili yasa mukaga ya kamata shafin "TAFARKIN TSIRA" yayi rubutu akan wannan mas'ala.

ME YAKE KAWO BASUR ???

Da yawan mutane suna kasa banbancewa meye basir da yawa mutum daga yaji cikinsa yana kugi ko yana ciwo sai yace basir yana damunsa, amma da yawa wasu cututtu suna kama da basir, kuma yana cutarwa da yawa.

Yakan sa sha'awar mutum ta bangaren jima'I ta dauke, ya kansa ciwon ulcer domin yana hana cin abinci, yana kuma kawo wata cuta wadda ake ce wa (sha'awatul-kaziba), shine mutum daya fara cin abinci sai yaji ya koshi.

Kowa da kowa zai iya samun wannan matsala ta Basir, maza da mata.

Amma ba acika ganinsa ga yara ba, anfi ganinsa ga manya, Kuma kowa zai iya samunsa a kalla sau daya a. rayuwarsa.

A manyan ma sai masu nauyi sosai, kamar mutane masu kiba.

A mata kuma za a ga basir ya fi yawa a lokacin da mace ta samu juna biyu, saboda nauyin da takara yayin daukar ciki, Idan ta haihu kuma ya baje.

A likitance basir shine ciwon jijiyoyi ko magudanan jini na dubura, na can ciki ko na waje-waje, wadanda suke kumbura su kuma yi ta ciwo.

Wasu abubuwan da ake gani suke kawo wannan ciwo sun hada da.

Yawan zama wuri daya na tsawon lokaci, yawan bayan gida mai tauri shi ma kansa jijiyoyi ko magudanan jinin dubura su kumbura su rika ciwo.

A dukkan wadannan yanayi, magudanan jinin suna kumbura, suja ruwa, wani lokaci su fashe.

Shiyasa mai basir wani lokaci yakanji zafi ko ciwo a dubura, wani lokacinma har da zubar jini.

GIDA NAWA BASIR YAKASU ???

Basir Ya kasu kashi uku.

Akwai na cikin dubura da kuma na kasa, akwai kuma mai tsuro wanda akan jishi yana saukowa, har sai an mayar da shi.

ILLOLI GUDA 20 DA BASIR KAN HAIFARWA DAN ADAM.

Basir ko kuma ince Dan kanoma wanda a Turance ake kira da "DYSENTERY" yana haddasa illoli da dama kamar haka :

1.TSUWAR HANJI (INTESTINAL DISTURBANCE).

Zaka rinka jin hanjin cikinka na yawan tsuwa akowane lokaci.

2.KUMBURIN CIKI :Cikinka zai kumbure saboda toshewar hanji a sanadin dattin ciki da yawaitar girman kwayoyin cuta da rashin samun damar abinci ya yi saurin narkewa.

3.YAWAN TUSA (FREQUENT FLATUELENCE) : Zaka rinka yawan fitarda iska akai akai, wani iskan sai ka ce wanda ya ci mushe.

4.ZAFIN JIKI DA CIWON KAI : Jikinka zai rinka zafi ga kuma yawaitar ciwon kai wanda baya jin magani kamarsu analgesic.

5.RASHIN CIN ABINCI KA KOSHI : Basir na haddasa maka kaji baka iya cin komai,kusan komai kaci sai kaji ba dadi.Take ka koshi.

6.YAWAN ZUWA TOILET: Basir kansa kayi ta yawon zuwa toilet,idan kaje kuma kayi ta faman yunkuri da nishi sai zafin musiba da fitar majina ko jini dan tsirit.

7.RAMEWA : Basir kansa ka rame kamar mai ciwon qanjamau.

8.CIWON GABOBIN JIKI : Basir kan haddasa ciwon jiki da kowace ga6a ta jiki.

9.TASHIN ZUCIYA : Sai kaji kamar kayi amai,kana ta faman zubarda yawu.

10.FITAR BAYA : Duburarka zata fito waje (basir mai tsiro).

11.CIWO A CIKIN DUBURA : Sai kaji matsanancin ciwo ka kasa tsayawa ko zama.

12. DAUKEWAR SHAWA : Namiji yakasance kamar baima balaga ba, ita kuma mace batama san meye biyan bukata ba, duk tabi ta bushe ba ni'ima ba wata gamsarwa.

13. KAIKAYIN DUBURA : Basir kansa dubura ta tsage ga zafi da fesowar kuraje.

14.KURAJE GA MATSE MATSI : Basir kan haddasa irin haka amma mutane da dama suna tinanin kamar sanyi ne, to na sanyi ya sha banban dana basir, dan na sanyi akan ga zubar farin ruwa masu yauqi da wari kamar danyen kifi.

15. YANA MURDE HANJI : Ta yanda zai haifarda ru6ewar hanji da sauran cutukan ciki.

16. BAYAN GIDA MAI TAURI : Yana haddasa bayan gida mai tauri kamar duwatsu,kamar kashin dabbobi.

17.Basir na kawo ciwon baya.

18.Basir na haifarda (LIVER ABCESS)

19.Basir na haifarda Brain abcep,sai yakasance kamar kai hauka, kai yana ma haukata Dan-adam.

20.Yana hude hanji (intestinal ulceration, ga zafin ciki kamar mai ulcer).

HANYOYI KARIYA.

Hanyoyin sun hada da yawan motsa jiki da yawan hada ganyayyaki a cikin abinci da yawan cin ’ya’yan itatuwa, Wadanda duka sukan sa bayan gida laushi.

MAGANI DA YARDAR ALLAH.

Idan ciwon basir ya hanaka gamsar da iyalinka wato ya kashe maka jijiyoyin azzakari basuda karfi ka jarraba hada wannan maganin.

Kanemi sassaken dinya da saiwar tsada da saiwar sabara, amma yakamata sassaken dinyar yafi yawa sosai, sai a dakasu sai a gauraya waje guda.

Kullum arinka dibar cokali daya a dafa da ruwa kofi daya sannan a tache asha har zuwa mako daya (1week).

Idan kuma basir din yana tsirowa to sassaken dinyar za a samu a dafashi tun yana danyensa Sannan a surka ruwan daidai misalin yadda baza a chutu dashi ba.
Sannan a juye acikin bahon wanka, sai a rinka zama aciki wannan yana kone basir mai tsiro cikin gaggawa.

A bangaren maganin islamic kuma asamu Garin Habbatus Sauda kamar cokali 3 sai a hada da Garin sassaken Dinyar shi kuma cokali 1 a saka garin citta cokali daya sai a samu zuma kamar copy karami a zuba agauraya akarinqa shan cokali2 safe da rana da yamma wato sau uku a rana.

Idan tsirowa basir din yakeyi za a iya samun garin Hulba da bagaruwa da kuma garin sassaken dinya ka rinka dafawa ana zama acikin ruwan zafin wadannan magungunan dukkansu sun inganta domin mun dade da jarrabasu.


MUKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Kadan Daga Cikin Illolin Shan Taba Sigari Ga Lafiyar Dan Adam

Karanta Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Amfanin Dabino ga Lafiyar Ɗan Adam Cikakken Bayani da Yadda za'ai amfani da Shi

KARANTA KO ME YASA MATA KE NEMAN 'YAN UWAN SU MATA DOMIN YIN MADIGO???

KAƊAN DAGA CIKIN ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MAZA DA KUMA SANYIN GABA

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: Tafarkin Tsira
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user