Sunday 21 March 2021

POS: Tarihin Sa Da Hukuncin Amfani Da Shi Wajen Kasuwanci Da Fitar Da Kudade Da Tura Su A Addinin Musulunci

Tura Wannan Zuwa

Bismillahir Rahmanir Rahim Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata ga Annanbinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa bakiɗaya.


Hukuncin Amfani Da POS Da Tarihin Sa


Marubuci: Ahmad Murtala Mansur


Bayan haka, a yau Laraba 23 Jumada Ula, 1442 H.-06 Janairu, 2021 M., na samu tambaya ta fuskoki da yawa har sai da aka rubuto cewa: “Malam ana cikin buƙatuwar yin cikakken bayani a dangane da POS. Wasu malaman sun haramta, wasu kuma sun halatta, Mun gode”. Wannan ita ce tambayar. Amma jin akwai wannan saɓani na malamai a nan ƙasar, ya sa na yi kamar ba zan bada amsa ba. Saboda ban cika son shiga irin mas’alolin da aka samu karakaina ba, ba tare da na  ji ko na karanta abin da kowane ɓangare ya faɗa ba. Sai dai tambayar ta zo daga wajen wani mutum mai kima a idona. Don haka na rubuta wannan bayani. Amma ba wai na rubuta ba ne a matsayin dole sai na gamsar da kowa da kowa ba. Wannan ba zai taɓa yiwuwa ba. Na dubi mas’alar ne da kyau gwargwadon abin da Allah ya huwace a yanzu-yanzu. Allah ya bamu sa’a da dacewa.


1-Yana da kyau a riƙa sanin tarihin wasu abubuwa da yadda suka taso da yadda suke amfani da sauran wasu abubuwan da suka shafesu. Saboda ta haka ne za a iya basu hukuncin da ya dace da su a Shar’ance. Imamu Shafi’i yana cewa, “Na ɗauki lokaci ina karanta ilimin tarihi, shekara kaza da kaza! Amma na karantashi ne kurum don na taimaka da shi wajen fahimtar ilimin Fiƙihu”.-(Al-Istiksa Li Akhabril Duwalil Magribil Aksa:1/59)
الإمام الشافعي رضي الله عنه كان يقول:"دأبت في قراءة علم التاريخ كذا وكذا سنة وما قرأته إلا لأستعين به على الفقه".


2-Akan haka, bari mu fara da ɗan tarihi kaɗan. Abin da ake nufi da POS shi ne ‘Point of Sale’ "نقاط البيع" . A wani lokacin kuma ana kiransa da sunan POP wato Point of Purchase. Duka biyun a asalinsa suna nufin tsarin ƙididdige cinikin da mai kanti ya yi a nan take ba tare da wata wahala ba. An fara ƙirƙiro tsarin POS tun a 1879 M. Da sunan ‘Cash Register’. Sunan wanda ya fara ƙirƙiro shi James Ritty. Yana da babban shago kayan masarufi. Amma sai ya fahimci ma’aikatansa suna yi masa ɗingushe. Don haka sai ya sa aka ƙirƙiro inji da sunan ‘Incorruptible Cashier’ don ya riƙa sanin adadin abin da ya shigo lalitarsa. A 1906 M. a ka fara jona wannan inji da wuta, ta yadda ya ƙara sauri wajen aikinsa. Sai kuma a shekarun 1970s aka fara haɗa wannan fasaha da na’ura mai kwakwalwa. Haka ya wanzu har shekarun 1990s a inda aka fara ƙera injina na zamani, waɗanda su da kansa kwanfiyuta ne. Shigowar shekarun 2000s a nan ne aka fara samar da irin waɗannan injin amma waɗanda za a iya ɗauka a hannu daga nan a kaisu can, suna kiransu da ‘mPOS’-wato Mobile POS

 

3-Tsarin POS ya shigo Nigeria sosai  2012 M. a lokacin da Babban Bankin Tarayya ya huwacewa ‘yan ƙasa su riƙa amfani da shi saboda rage zirga-zirga da kuɗaɗe a hannu. Kafin haka kaso 90% na cinikayya ana yinsu da kuɗaɗe a hannu tsirara! –(Challenges to the Efficient Use of Point of Sale (POS) Terminals in Nigeria na Adeoti).


4-Akwai POS kala-kala wanda kamfanoni da wuraren sayar da abinci da abin-sha da otel-otel suke amfani da su. Kowanne yana neman wanda ya dace da buƙatarsa. Amma amfani da POS a matsayin wurin da za a iya zuwa a nemi su baka wani gwargwado na kuɗi, su kuma su yi amfani da katin mutum na ATM su ɗibi wannan kuɗin su tura zuwa account ɗinsu a maimakon wanda suka bashi a nan take, wannan ya fara ne a ‘yan shekarun nan, ba da daɗewa ba.


5- Kafin mutum ya buɗe wurin harkar POS sai ya bi wasu matakai kamar haka:


i- A dokokin Ƙasa an yarda a buɗe irin waɗannan wurare kamar yadda aka faɗa a baya.


ii- Masu harkar POS suna da alaƙa da bankuna ta fuskar sai sun je sun yi rijista da wani banki tukuna. Daga cikin hikimomin yin haka shi ne don bankin zai ga ana hadahadar kuɗaɗe masu yawa akai-akai, sai ya zamo ba zai damu ba, saboda ya yarda da account ɗin da ake wannan hadahadar da shi.


iii- Akwai certificate da bankin zai bawa wanda ya yi rijista da shi a matsayinsa na “agent”-wakilinsu. Don haka zai yi rawa da bazar wannan bankin a iya ɓangaren da suka yarjewa POS ya yi hidima.


vi- Bankin da aka yi rijista da shi yana son ya ga motsin wannan POS a ƙalla sau goma a rana don ya tabbatar da yana aiki. Wannan ba tare da ya kula da yawan kuɗin da zasu shiga ko zasu fita ba ta hanyar wannan POS ɗin.


v- Zai biya kuɗin hayar shago da wutar lantarki da kuɗin data da yake amfani da ita don hawa kan intanet ko kuɗin cajin waya, da sauransu.


6- Mafi girman ayyukan da masu shagunan POS suke yi guda biyu ne:


a- Zasu bada kuɗi cash ga wanda yake so, sai su karɓi ATM card ɗinsa su ciri daidai kuɗinsu su tura cikin account ɗinsu. Misali an biyashi albashi dubu goma (10,000) sai ya zo suka bashi tsurar kuɗi dubu goma cash, sannan sai ya basu katinsa mai ɗauke da waɗannan kuɗaɗe, sai su kwashe daidai kuɗin da suka bashi daga accout ɗinsa zuwa nasu.


b- Mutum zai iya kawo kuɗi kamar dubu goma ya ce a tura masa cikin account ɗinsa ko kuma a turawa ɗansa da yake karatu a wata ƙasa ko a tura a account na mahifiyarsa ko ɗan uwansa ko zai biya kuɗin wutar lantarki, ko kuɗin makaranta, da dai sauransu.


A duk waɗannan hidimomi da masu shagon POS suka yi, zasu buƙaci a basu wani abu a matsayin ladan aikin da suka yi. A yadda al’adarsu ta gudana a yanzu akwai wani gwargwado na kuɗi mara yawa da suke karɓa bisa duk dubu ɗaya ko biyar ko goma ko ɗari ko miliyan ɗaya da suka bawa mutum ko suka tura masa. Za a iya basu daga account ɗin mutumin idan da akwai wasu kuɗin a ciki ko ya kawo ladan ya basu hannu-da-hannu daga cikin kuɗin da suka bashi.


7- Waɗannan ayyuka na POS dukansu sun halatta ta fuskoki marasa iyaka ba tare da wani dabaibayi ba. Ga kaɗan daga cikinsu:


i- Akwai abubuwa masu yawa da banki koda kuwa wanda ba na Musulunci ba ne yake yi. Kuma ba a ƙirgasu a matsayin haram. Wannan sun haɗa da tura kuɗi daga wani wuri zuwa wani “transfer” "التحويلات المصرفية. Wannan ba wani laifi a kansa. Mutum kuma zai biya banki ladan aikin da ya yi masa. Abin da masu shagunan POS suke yi a matsayinsu na wakilan banki, waɗanda ya san da zamansu a wannan sana’a, bai gaza ko kuma na ce irinsa ne kwabo-da-kwabo da wanda bankunan suke yi. Malaman zamani kuma bakiɗaya suka ce daidai nan yana da kyau a aikin banki.Wato ba haram ba ne a biya banki kuɗin aikin transfer-(Kararu Majma’ul Fikihil Islami:9/1/370; Al-Bunukul Islamiyya na Abdullahi Addayar sh/25; Al-Ma'amalatul Masrafiyya Wa Hukmuha Fil Islam sh/14-15; Al-Masariful Islamiyyah: Dirasah Li Adadin Minha na Rafik Yunus Al-Misri, sh/53-55; Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad:12/234-243)


ii- A zahiri ma shagon POS wani ƙaramin banki ne da yake gudanar da wasu daga ayyukan bankin da yake da rijista da su. A lokacin da mutum ya yi amfani da ATM ya ɗebo kuɗi daga injin da banki suka ajiye don ɗibar kuɗaɗe, zai ga bankin sun ɗebi wasu ‘yan kuɗaɗe na hidamar da suka yiwa mutum. Bankin da mutum yake da account suna ɗan yi masa ragi. Amma wani bankin daban suna ɗiba fiye da yadda nasan suka ɗiba. Don haka, shi kansa mai POS ba dalilin da zai sa ba zai karɓi wani kaso na hidimarsa ba!


iii- Masu POS cikakkun wakilai ne na karɓar kuɗin mutum daga bankinsa zuwa nasu, sannan sai su bashi daga kuɗinsu. Saboda "wakilci taimako ne" kamar yadda Ibnul Arabi Al-Maliki yake faɗa "الوكالة معونة".- (Ahkamul Kur’ani: 3/223). Malamai sun bayyana cewa ba laifi ka sa wakili sannan ka biyashi ko kuma in ya ga dama ya yi maka wakilcin Fisabilillahi, ba tare da an biya shi komai ba. Imamu Ibnu Kudama ya na cewa: “Ya halatta a yi wakilci ko don wani abu da za a bayar ko kuma haka kurum ba tare da shi ba”-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 5/95)              قال الإمام ابن قدامة:"يجوز التوكيل بجُعُل، وبغير جُعُل"


A zamanin yanzu ba dole ba ne sai an tura wani ya je bankin da ƙafa sannan za a ce an yi wakilci. Hatta tura kuɗin zuwa account ɗin mai POS a matsayin kamar an je an karɓo yake, irin abin da malamai suke kira da “Karbar abu a Ma’ana” "القبض الحكمي". Tunda kuɗin sun shiga lalitarsa, ba laifi don ya bayar da su ta kowace irin fuska.Wato ko ya ɗauko wannan da ya turawa kansa ya bawa mai kuɗin ko kuma ya bashi wasu da yake da su. Sannan a bashi ladansa.


iv- Masu POS suna yin amfani da ƙwarewarsu da wani ɓangare na kuɗin da suka sa a katin wayarsu ko na data ɗin da suka saya. Haka nan suna amfani da wutar lantarki da injin POS ɗin kansa da suka saya da zaman da suke yi na kuɗi a shaguna. Bugu da ƙari, sun ragewa mutane wahalar bin layin ATM ko na cikin bankuna da aka saba yi. Wannan duka a bayyane yake cewa sun yi wa mutum aiki, don haka masu POS suna da cikakken haƙƙin a biyasu kuɗin wahalarsa.


'Transfer' da kamfanin waya suka huwacewa mutane suke yi ta hanyar amfani da wasu lambobi da kowane kamfanin waya yana da irin tasa, shi ma bai gaza irin aikin da masu POS suke yi ba. Waɗannan kamfanoni suna samun wani kaso daga cikin tura kuɗaɗe da mutane suke yi. Duka ya halatta.


v- Kowace mu’amalla tana da asali guda biyu; “Halasci” da “Inganci” الإباحة والصحة. Babu wani dalili da zai haramta sana’ar POS. Sannan kuma masu yinta a halin yanzu suna gudanar da ita bisa asalin inganci. Don haka ba haram suke ci ba, ba kuma ɓatacciyar sana’a suke gudanarwa ba.


vi- Ba bu wani abu na haram ko riba a cikin mu’amalla guda biyu da ake gudanarwa ta hanyar POS. Domin riba tana shiga abubuwa guda uku ne kurum, kuma ba bu wata hanya da zasu shiga wannan mu’amalla:


a- Ciniki: Ba wata cinikayya aka ƙulla tsakanin mai POS da wanda ya zo masa don ya fito masa da kuɗi ko don ya tura masa ba. Don haka riba ba zata shiga wannan ɓangaren ba.


b- Bashi: Ba wani bashi a cikin wannan mu’amalla ta POS. Domin da ya zo shagon POS cewa ya yi yana da kuɗi (10,000) a cikin wannan ATM ɗin a kwashesu a tura wani account ɗin amma a bashi kuɗin cash. Wannan ‘transfer’ kenan ba bashi ba ce. Don haka riba ba zata shiga ba. Kada a ɗauka don ya zo ya bawa mai POS katin ATM ɗinsa, shi kuma ya tura kuɗi zuwa nasa account ɗin cewa bashi ya bashi. Kuɗin kuma da zai ba shi hannu-da-hannu biyan bashin ne. Wannan ba haka ba ne. Domin  ‘Ana ɗaukar komai da manufarsa’ "الأمور بمقاصدها" kamar yadda wata ƙa’ida ta faɗa. An gina mu’amallar ne a kan ‘transfer’, wadda daman bankuna suna yinta. Mai POS ya ɗebo kuɗin daga wani account ne ya zuba a account ɗinsa, sannan ya bada su cash.


Ko da za a ce banki su ma ajiya, ake cewa mutum, ya kai musu, amma kuma aka hana mu'amallar, saboda ta ginu ne a kan bashi. Wannna haka yake ta fuskar cewa su banki tun ranar da aka kafa tsarin bankunan da aka saba da su yau-da- gobe (Conventional Banks) ya ginu ne a kan bashi da ruwa. Sañnan har yanzu haka yake a rubuce a kan dokokinsu. Ko da mutane suna cewa sun kai ajiyar kuɗaɗe banki, shi bankin ya san ba ajiya aka kai masa ba, shi a wurinsa rance aka ba shi. Amma saɓanin wañnan mu'amalla ta POS wadda tun asali tsakanin mai kuɗi a ATM da mai shagon POS ba wanda yake da manufa ta bashi da rance, kowannensu manufarsa ita ce za a yi transfer ta kuɗi kawai. Don haka suka bambanta da tsarin da mutanen suke kira "ajiya a banki".


Wani abu mai matuƙar muhimmaci da ya kamata kowa ya daɗa ganeshi shi ne, idan har mun ƙaddara cewa alaƙar bashi da rance ce tsakanin mai POS da mai kuɗi a katinsa na ATM, to abin la'akarin shi ne shi mai kuɗin shi ne fa ya bada rance sañnan shi ne kuma ɗin dai ya bada ƙarin da sunan ladan aiki. Ba wai mai shagon POS ne ya mayar da kuɗin da aka ranta masa (in har mun ɗauka ma bashi aka bashi!), sannan ya ƙara wani abu a kai ba. Domin malamai sun faɗa cewa riba ita ce ƙudin da wanda ya karɓi rance zai mayar da kuɗin da aka bashi da wani ƙarin'. A mas'alar POS kuwa ba shi ne ya ƙara ba, shi aka ƙarawa. Wañnan yanayin kuwa ba malamin da ya kirawoshi da sunan riba!!


A yi la'akari da wañnan sosai, domin ina ganin rashin ganeshi da fayyaceshi ne, ya sa wasu suke ɗaukar akwai riba a mu'amalar POS, wanda kuma a haƙiƙa, kamar yadda aka gani, ba bu!


c- Canji: Duk da akwai burbushin cinikayya a cikin canji, sai dai a ilimi Fiƙihu ana wareshi saboda ƙarfin ma’anar da take cikinsa wadda zata iya sawa ya ci gashin-kansa. Abin nufi dai masu POS ba canji suke yi ba. Kuɗin mutum ne za a bashi irinsu. Sai dai a lokacin da ya bada Naira aka turawa ɗansa ko wakilinsa a wata jiha ko wata ƙasa, zai ɗebi daidai da canji da ƙimar wannan kuɗi a can.


Abin da hadisai suka hana na canji kamar wanda ya shafi dinare da dinare ko azurfa da azurfa ko naira da naira ko dala da dala shi ne, misalin a sami jan gwal sosai da kuma farin gwal, wanda ba mai ja sosai ba, sai a ce za a ɗauki wani abu a cikin wanda ba mai ja sosai ɗin ba. Kamar sabuwar naira da tsohuwa, sai a ce za karɓi wani abu a wurin mai tsohuwa don an bashi sabuwa. Wannan shi ne haram. Amma idan ya zamo gwal ko naira ɗin suna wani account sai aka turashi wani account ɗin daban sannan aka bawa mutum irinsa, shi kuma ya bada ladan wani kuɗi don wahalar turawa da rage masa wahalar zuwa banki da aka yi, wannan ba laifi.


Shi kuwa mai POS ya bawa mutum kuɗinsa yadda suke, sai dai yana cewa za a bashi kuɗin fito da ya yi! Ba wai mutum zuwa ya yi, a misali, ya miƙa masa ₦10,000 hannu da hannu, shi ma ya mika masa ₦9,990 a matsayin canji ba.  Ba irin wañnan aka yi ba.


Dangane da ita kuma misali naira ɗarin ta ladan fito, mai ATM zai iya bawa mai POS ita daban, ko kuma ya yarjewa mai POS ya haɗa da ita a cikin transfer ɗin da ya yi daga cikan katin, a matsayin ladan aikinsa. Masu canji kuwa cewa zai yi zan baka sababbin 'yan naira ɗari-ɗari na ₦10,000 amma zaka ɗora mini naira ɗari, to a nan sai a ce an yi riba! Domin amfanin sabuwar naira ɗari da tsohuwa duk ɗaya ne, ba bu dalilin karɓar wani abu a nan!


A cikin Mazahabin Hambaliyya, duk da cewa saɓanin Mazahabin Jumhurun Malamai ne, amma sun halatta cewa mutumin da ya sana’anta wani gwal ya zubashi a wata kama da ado na musaman a zo a sayi gwal da kuɗin da ya yi daidai da shi, sannan a ƙara wani abu a matsayin ladan sana'arsa da fasahar da ya nuna a wajen ƙera ɗankunne da sarƙa da wannan gwal ɗin. Shehul Islami Ibnu Taimiyya da Ibnul Kayyim da Ibnu Mani’, duk sun tafi a kansa haka. Sheikh Al-Mardawai ya ce, 'A kan haka fatawar malamanmu na Hambaliyya ta gudana'. Ga kuma bayanin da Ibnu Kudama ya yi. Ya ce: “Idan mutum ya ce da gursimeti  ka ƙera mini zobe azurfa, nauyinsa kamar dirhami ɗaya, zan biyaka dirhami ɗayan. Sannan zan baka wani dirhamin a matsayin ladan aikinka, wannan ba ya cikin irin abin da aka hana sayar da dirhami ɗaya da guda biyu. Malaman Mazahbinmu na Hambaliyya suka ƙara da cewa: gursimetin zai iya karɓar dirhami biyun, ɗaya a matsayin kuɗin zoben, ɗayan kuma sakamakon ladansa“-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 4/130-131; Al-Majmu’u na Nawawi:10/87-88; Al-Ikhtiyarat Al-Fikhiyyah na Al-Ba’ali:sh/473; Al-Fatawal Kubra na Ibnu Taimiyyah:5/391, I’lamul Muwakki’in na Ibul Kayyim: 2/159-162, Al-Furu’u na Ibnu Muflih:4/149; Al-Insaf na Ala’uddini Al-Mardawi:5/15; Azzahbu Wa Ba’adu Khasa’isihi Wa Ahkamihi na Ibnu Mani’ a Majallar Majma’ Fikhil Islami, Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad:11/273-322)
قال الإمام ابن قدامة:"فأما إن قال لصائغ: اصنع لي خاتما؛ وزنه درهم، وأعطيك مثل زنته. وأجرتك درهما. فليس ذلك بيع درهم بدرهمين. وقال أصحابنا للصائغ أخذ الدرهمين؛ أحدهما في مقابلة الخاتم. والباقي أجرة له".


8- Kulawa kada mutum ya faɗa cikin haram ko ya ci riba  yana daga cikin muhimman abubuwan da Musulmi yake ƙoƙari a kowane lokaci. Sayyadina Umar ya yi bayanin yadda mas’alolin riba suke da wahalar sha’ani wajen ganesu, sannan ya ce, “Ku  ƙauracewa riba da duk wani abu na kokwanto”.-(Sunanu Ibnu Majah, L:2276)
  قال عمر بن الخطاب- رضي الله عنه -"دعو الربا والريبة".


Duk wata mu’amalla da wani yake yi, in ya ji shi a zuciyarsa bai gamsu da ita ba, sai kurum ya ƙaurace mata. Wannan kuma bai hana waɗanda suka gamsu da ita su ci gaba da yinta ba, matuƙar akwai mafita ta Shari’a a ciki. Malamai suna faɗa a wata ƙa’ida cewa, “Abin la’akari a mu’amalla shi ne manufa da ma’anonin da suka ƙunsa, ba wai zahirin lafazi da ginin kalmomi ba”.
"العبرة في العقود بالمقاصد والمعاني، وليست بالألفاظ والمباني"


Amma saɓanin masana ko malamai a kan wata mas’ala ba shi ne yake nufin an bawa mutane damar yin zaɓi-ka-tika ta hanyar mutum ya zaɓa wani ra’ayi kurum ya darje shikenan ba! Mutum yana zaɓar maganar da tafi tsayawa a kan dalilan Kur’ani da Sunna ne kurum, ba wai ya bi yarima a sha kiɗa ba! Ko ya bi hanyar tsanantawa mara tushe! Imamu Sufyanu Assauri yana cewa, “Ilimi a wurinmu shi ne samun rangwame daga yardajjen malami. Amma matsantawa kuwa, wannan kowa zai iya yinta”.-(Jami’u Bayanil Ilimi Wa Fadlilihi na Ibnu Abdilbarri: 2/77/ 766)
قال الإمام سفيان الثوري رضي الله عنه أنه قال إنما العلم عندنا الرخصة من ثقة، فأما التشديد فيحسنه كل أحد".


Allah ya bamu tsayawa a kan neman halal da ƙauracewa haram bisa yadda Shari’a ta tsara. Ya bamu ikon tsayawa a kan tsarin addininmu da bin sahun Annabinmu – Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi da Alayensa da Sahabbansa bakiɗaya Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user