Thursday 14 November 2019

HANKALI NA YANA TASHI IDAN NA TUNA DA WANNAN

Tura Wannan Zuwa Ga
HANKALINA yana tashi idan na tuna wata rana babu ni yanzu kuma akwai ni.


Hankali na Yana Tashi..

Marubuci: Hassan Abdul

HANKALINA yana tashi idan na tuna yanzu ina motsi.

Wata rana kuma zan zamo gawa.

HANKALINA yana tashi idan na tuna kullum gidanmu nake kwana.

Wata rana kuma a kabari zan kwana.

HANKALINA yana tashi idan na tuna Kullum dakaina nike wanka.

Wata rana kuma wasu zasu yimin.

HANKALINA yana tashi idan na tuna harda ni akeyin jana'izar wasu.

Wata rana kuma jana'iza ta za'ayi.

HANKALINA yana tashi idan na tuna ni mai laifi ne.

Gashi kuma hisabi yana jirana.

HANKALINA yana tashi idan na tuna annabawa ma sunji radadin mutuwa.

Balle ni mai  yawan aikata zunubi.

HANKALINA yana tashi idan na tuna mutuwa dole ce.

Gashi kuma banyi wani tanadi ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Kowanne Miji ya Kula dasu Idan Zai Yi Magana da Matar Sa

KARANTA MUHIMMAN ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI KAFIN KU FARA LALATA 'YA'YAN MUTANE

KARANTA BAMBANCI TSAKANIN MUTANE DA MALA'IKU !

HANKALINA yana tashi idan na tuna inada sutura masu yawa.

Amma watarana linkafani shine karshen sutura ta.

Daure ka turawa abokan Ka domin samun rahama da gafara a wajen Ubangijin Ka.

Allah yasa mu da ce Amin

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user