Thursday 14 November 2019

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN JIHAR BAUCHI KASHI NA BIYU

Tura Wannan Zuwa
Kashi na biyu

Sa'ar da lamarin Shehu Usmanu ya bayyana, mutane suka taru a wurinsa har suka yi yawa, sai sarakunan Hausa suka fara fushi da hakan, suka zama masu fitinar jama'ar Shehu Usmanu, suna aike musu da hari, suna kisa da kame su gami da siyarwa a matsayin bayi.

Tarihin Jihar Bauchi

MarubuciSADIQ TUKUR GWARZO

Da wannan abu ya tsananta sai jama'a suka yiwa Shaihu mubaya'ar yaki, suka soma gina ramin ganuwa da ɗaura tuta.

Anan ne Shehu ya Umarci Yakubu ya koma gidasa Bauchi ya kira jama'ar sa zuwa biyayya ga Shaihu.

Yakubu ya tashi ya tafi ga mutanensa a Bauchi da ake kira Gerawa, ya kiraye su amma basu amsa kira ba. Sai waɗansu mutane daban ne suka amsa, acikin su akwai Mallam Adamu, da Ibrahimu, da Abdun-Dumi, da Hassan, da Faruku, da Muhammad Kusu, da Muhammad Yaro, da Hammada, da Mallam Badara, da waɗansun su da dama.

Yakubu ya ja taron jama'ar sa zuwa wani wuri da ake kira Warunje ya zauna, sannan ya tashi zuwa Inkel, mutane na ta zuwa wurinsa a hankali suna yi masa mubayi'a.
Daga nan sai ya shirya yaki zuwa wani gari da ake kira da suna Kanyallo, ya yaƙe su yayi galaba akansu, ya ƙone gidajensu ya washe dukiyarsu, sannan ya koma wurin zamansa. Wannan kuwa shine farkon yakin sa.

Bayan wannan sai ya ƴara shirya wani yaƙin, inda ya sarauta Galadima Faruku a matsayin Sarkin Yaƙi sannan ya aike su zuwa Miri, da zuwan su kuwa sai suka faɗa musu da yaƙi.

Anan ma suka karkashe mutanen Miri, suka kamo ƴaƴansu, suka rushe gidajensu, Sarkin su ya gudu, ya tura iyalan gidansa cikin kogon dutse sannan ya karkashe su, daga bisani kuma ya kashe kansa.
Galadima Faruku ya komo wurin Yakubu da ganimar yaƙi mai yawa cikin murna da farin ciki.

Daga nan sai Yakubu ya shirya wani yaƙi zuwa Gubi.

Su kuwa mutanen Gubi ance Kafirai ne masu girman kai, gasu jaruman gaske masu ƙarfin rai, babu mai iya samun su.
Haka kuma suna zaune ne a wani wuri mai yawan duwatsu da wuyar shiga saboda santsin wurin shigar da kuma ƙafe-ƙafe gami da ƙayoyi.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN JIHAR BAUCHI KASHI NA FARKO

KARANTA TARIHIN YADDA TURAWA SUKA AZABTAR DA AL'UMMAR YANKIN AREWACIN NIGERIA

Kalli Yadda Aka Kashe Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto A Kan Idona - Inji Direban Sardauna

Amma duk da haka, sai da Yakubu yaci galaba akan su. Ya kore su suka bar gidajensu zuwa cikin duwatsu, shikuwa ya shiga cikin gidajen nasu, ya kashe na kashewa, ya kama na kamawa. Sannan ya koma gida Inkel cikin aminci da nasara.
Ai kuwa wannan yaƙi shine ya tsoratar da dukkan kafiran ƙasar Bauchi, musamman mazauna saman duwatsu.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user