Sunday 10 November 2019

DAN ALLAH MALAM ME NE NE BAMBANCI TSAKANIN MUTANE DA MALA'IKU?

Tura Wannan Zuwa Ga
                                Tambaya

Assalamu alaikum
Malam inada tambaya Menene bambancin mutane da mala'iku?

Bambancin Mutane da Mala'iku                             Amsa

Wa'alaikumus salam, Akwai Bambanci tsakanin mutane da Mala'iku ta fuskoki da dama, ga wasu daga ciki:

1. An halicci Mala'iku daga haske su kuma mutane an halicce su ne daga Yumbu kamar yadda hadisi ya tabbatar.

2. Mala'iku ba sa ci ba sa sha, mutane kuma suna cin abinci suna shan ababan sha.

3. Mala'iku suna iya rikida su canza kamanni, mutane kuma ba su da damar hakan.

4. Dukkan mutane suna sabon Allah, amma Mala'iku ba sa sabon Allah kamar yadda Allah ya fada a suratu Attarim.

MAKALOLI MASU ALAKA:
5. Mala'iku suna da fika-fikai sabanin mutane.

Allah ne mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user