Thursday 31 October 2019

Shin dagaske Ne duk 'Yam Matan Jami'a Lalatattu Ne?

Tura Wannan Zuwa Ga
Ya kamata mutane suji tsorin Allah a irin kalaman da zasu ke furtawa. Wani yayi rubutu yana mai ikirarin cewa duk dalibai mata da suke karatu a jami'a suka kai matakin karshe (level four) wai lalatattu ne, wannan zalinci ne gaskiya.


Rayuwar 'Yam Mata a Jami'a


Marubuci: Yasir Ramadan Gwale

Kawai saboda mutum ba shi da 'ya ko kanwa da take yin karatun jami'a, shi kenan sai yayi musu kudin goro yace duk lalatattu ne. Wannan wane irin zalinci ne?

Yaya mutumin da yake da 'ya ko kanwa ko kanne a jami'a zai ji, idan ance musu lalatattu? Ba shakka akwai sosa rai ainun. Yana da kyau mutane idan zasu yi suka akan abu, suyi bincike kuma suyi adalci idan har ya zamar musu wajibi sai sun yi magana kan dalibai mata 'yan jami'ah.

A kowanne fanni na rayuwar yau, akwai nagari akwai lalatattu. Wasu matan basu taba bin ko hanyar jami'a ba, amma abinda suke na lalata yafi na 'yan jami'a, kamar yadda a jami'ar akwai lalatattu.

Haka nan, a jami'a akwai katangaggun mata masu nutsuwa da kamun kai, masu tsoron Allah, wallahi suna nan birjik, abinda da yawa ma basu sani ba, wlh da yawan daliban jami'a mata zaka samu suna yin Azumin litinin da alhamis, suna sallah akan kari.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ILLOLIN ZAMA DA MATAR AURE GUDA DAYA

Karanta Yadda Zaka Gane Budurwar da Ba ta Taba Saduwa da Namiji ba Kafin Kuyi Aure

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

Dan an samu daya ko biyu masu gurbatacciyar dabi'a ba shi zai sanya a yiwa sauran kudin goro ba. Yana da kyau mu dinga kiyaye harshenmu akan abinda ba mu da yakini ko tabbas akai. Allah yasa mu dace.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user