Thursday 31 October 2019

Karanta Addu'a Yayin da za a Yi Barci

Tura Wannan Zuwa Ga
Idan mutum ya zo kwanciyar barci sai ya hada tafin hannayensa biyu, ya karanta wadannan surori na Alkur'ani.

Addu'ar Yayin da za a yi Barci

Yana yin tofi cikin hannayen nasa;

(قل هو الله أحد)

(قل أعوذ برب الفلق)

(قل أعوذ برب الناس)

(Qul'huwallahu Ahad)

(Qul'a'uuzu Bi Rabbil Falak).

(Qul'a'uuzu Bi Rabbin Nas).

Sannan ya shafu su iya inda zai iya na jikinsa; yana farawa da kansa, da fuskarsa da kuma gaban jikinsa ya yi haka har sau uku.

Ya Karanta Ayatul-kursiy:

(اَللهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ)

Allahu La'ilaha illahuwal Hayyul Qayyum… (Ilaa A'khiruhaa).

Har zuwa karshenta, wanda ya karanta ta yayin da ya zo kwanciya to ba zai gushe ba yana da wani mai tsaro gare shi daga Allah, kuma shaidan ba zai kusato shi ba har ya wayi gari.


{آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللّهِ وَمَلآئِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لاَ نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ وَقَالُواْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ * لاَ يُكَلِّفُ اللّهُ نَفْساً إِلاَّ وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لاَ تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلاَ تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْراً كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلاَ تُحَمِّلْنَا مَا لاَ طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنتَ مَوْلاَنَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ}

Amanar rasulu bim aunzil ilayhi min rabbihi wa lmu'minuna, kullun amana billahi wa mala'ikatihi wa kutubihi wa rusulihi, la nufarriku bayna ahadin m-min rusulihi, la nufarriku bayna ahadin m-min rusulihi. Wa kalu sami'na wa ata'na, ghufranaka rabbana wa ilayka-l-masir.
La yukallifu l-lahu nafsan illa wus'aha, laha ma kasabata wa 'alayha ma kasabata, rannaba, la tuk'akhizina in nasina aw akhta'ana, rabbana wala tahmil 'alayna isran kama hamaltahu 'ala l-lazina min qabilina rabbana wa la tuhammilna ma la taqata lana bihi. Wa 'fu anna, wa ghfir lana wa rhamna. Anta mawlana fa-nsurna 'ala-l-qawmil-l-kafirin.

Manzon ya yi imani da abin da aka saukar gare shi daga Ubangijinsa, haka ma muminai; kowanne ya yi imani da Allah, da Mala'ikunsa, da litattafansa, da Manzanninsa, (suna cewa) ba ma rarrabewa tsakanin daya daga cikin Manzanninsa. Kuma suka ce mun ji (abin da Ka umarce mu da shi, ji na karba) kuma mun bi. Gafararka muke roko ya Ubangiji, kuma gare Ka makoma take. Allah ba ya dora wa rai (wani abu sai abin da yake da ikon aikata shi; abin da ya aikata (na alheri) yana gare shi, kuma abin da ya aikata (na sharri) yana kansa. (Ku ce) 'Ya Ubangijinmu! Kada ka rike mu idan uka manta ko muka yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kada ka dora mana, abin da za mu iya shi ba. Ka yi afuwa a garemu, Ka yi mana gafara, ka ji kan mu. Kai ne Majibincin al'amuranmu, sai ka taimake mu a kan mutane kafirai".

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Idan dayanku ya tashi daga shimfidarsa sannan ya dawo ya kwarya, to ya karkade ta da gefen gyautonsa sau uku, sannan ya yi Bismillahi, domin bai san abin da ya maye gurbinsa ba bayan ya tashi. Idan ya kwanta ya ce;

بِاسْمِكَ رَبِّي وَضَعْتُ جَنْبِي، وَبِكَ أَرْفَعُهُ، فَإِنْ أَمْسَكْتَ نَفْسِي فَارْحَمْهَا، وَإِنْ أَرْسَلْتَهَا فَاحْفَظْهَا بِمَا تَحْفَظُ بِهِ عِبَادَكَ الصَّالِحِينَ.

Bismika rabbee wada'tu janbee wabika arfa'uh, fa-in amsakta nafsee farhamha, wa-in arsaltaha fahfathha bima tahfazu bihi 'ibadakas-saliheen.

Da sunanka ya Ubangijina na kwana, kuma da izininka ne nake tashi. In ka rike raina (da mutuwa), to Ka ji kanta, in Ka sake ta kuwa, ka kiyaye ta da abin da Kake kiyaye bayinka salihai da shi.

اَللَّهُمَّ  إِنَّكَ خَلَقْتَ نَفْسِي وَأَنْتَ تَوَفَّاهَا لَكَ مَمَاتُهَا وَمَحْيَاهَا، إِنْ أَحْيَيْتَهَا فَاحْفَظْهَا، وَإِنْ أَمَتَّهَا فَاغْفِرْ لَهَا. اَللَّهُمَّ  إِنَّي أَسْأَلُكَ الْعَافِيَةَ.

Allahumma innaka khalaqta nafsee wa-anta tawaffaha, laka mamatuha wamahyaha in ahyaytaha fahfazha, wa-in amattaha faghfir laha. Allahumma innee as-alukal-'afiyah.

Ya Allah! Kai ne Ka halicci raina, kuma Kai ne Kake karbarsa. Gare ka kadai mutuwarsa da rayuwarsa suke. In ka rayar da shi, to ka kiyaye shi; in Ka dauke shi, to Ka gafarta masa. Ya Allah! Ina rokonka aminci daga dukkan mummuna.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya zo kwanciya sai ya sa hannunsa na dama karkashin kuncinsa. Sannan ya ce;

اَللَّهُمَّ قِنِي عَذَابَكَ يَوْمَ تَبْعَثُ عِبَادَكَ. (ثلاثَ مراتٍ)

Allahumma qinee 'azabaka yawma tab'athu 'ibadak. (3).

Ya Allah! Ka kiyashe ni azabarka a ranar da Kake tayar da bayinKa (bayan mutuwa). (su uku).

بِاسْمِكَ اللَّهُمَّ أَمُوتُ وَأَحْيَا.

Bismika l-lahumma amutu wa ahya.
Da sunanka Ya Allah nake mutuwa kuma nake rayuwa.

سُبْحَانَ اللهِ، ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ
وَالْحَمْدُ ِللهِ، ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ
وَاللهُ أَكْبَرْ. ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ.

Subhana l-lah (33),
Al-hamdu li-l-lah (33),
Allahu akbar (33).

Tsarki ya tabbata ga Allah (Sau 33)
Yabo ya tabbata ga Allah (Sau 33)
Allah ne mafi girma (Sau 33).

اَللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ وَرَبَّ العَرْشِ الْعَظِيمِ، رَبَّنَا وَرَبَّ كُلِّ شَيْءٍ، فَالِقَ الْحَبِّ وَالنَّوَى، وَمُنَزِّلَ التَّوْرَاةِ وَاْلإِنْجِيلِ،وَالْفُرْقَانَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ شَيْءٍ أَنْتَ آخِذٌ بِنَاصِيَتِهِ. اَللَّهُمَّ أَنْتَ اْلأَوَّلُ فَلَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ،وَأَنْتَ اْلآخِرُ فَلَيْسَ بَعْدَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الظَّاهِرُ فَلَيْسَ فَوْقَكَ شَيْءٌ،وَأَنْتَ الْبَاطِنُ فَلَيْسَ دُونَكَ شَيْءٌ،اِقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ وَأَغْنِنَا مِنَ الْفَقْرِ.

 Allahumma rabbas-samawatis-sab'a, warabbal-'arshil-'azeem, rabbana warabba kulli shay', faliqal-habbi wannawa, wamunazzilat-tawra, wal-injeel, walfurqan, a'oothu bika min sharri kulli shayin anta akhithun binasiyatih. Allahumma antal-awwal, falaysa kablaka shay', wa-antal-akhir, falaysa ba'daka shay/, wa-antaz-zahir falaysa fawqaka shay', waantal-batin, falaysa doonaka shay', ikdi 'annad-dayna wa-aghnina minal-faqr.

Ya Allah! Ya Ubangijin sammai bakwai, Ubangijin Al'arshi mai girma, Ubangijinmu kuma Ubangijin komai, mai tsaga kwayar tsiri da kwallon dabino, mai suakar da Attauna da Injila, da Alfurkani! Ina neman tsarinka daga sharrin komai wanda kai ne mai rike da makwarkwadarsa. Ya Allah! Kai ne na farko, babu wani abu kafinka, kai ne na karshe, babu wani abu bayanka, kai ne bayyananne, babu wani abu da yake sama da kai, kai ne boyayye, babu wani abu da yake boyewa gare ka. Ka biya mana basussuka, kuma ka wadatar da mu daga talauci.

اَلْحَمْدُ ِللهِ الَّذِي أَطْعَمَنَا وَسَقَانَا، وَكَفَانَا، وَآوَانَا، فَكَمْ مِمَّنْ لاَ كَافِيَ لَهُ وَلاَ مُؤْوِي .

Alhamdu lillahil-lathee at'amana wasaqana, wakafana, wa-awana, fakam mimman la kafiya lahu wala mu'wee.

Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da mu, ya shayar da mu, ya isar mana, ya ba mu makwanci. Da yawa wanda ba shi da ma'ishi, wala mai ba shi makwanci.

اَللَّهُمَّ عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَاْلأَرْضِ رَبَّ كُلِّ شَيْءٍ وَمَلِيكَهُ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ نَفْسِي، وَمِنْ شَرِّ الشَّيْطَانِ وَشِرْكِهِ، وَأَنْ أَقْتَرِفَ عَلَى  نَفْسِي سُوءاً أَوْ أَجُرَّهُ إِلَى مُسْلِم.

Allahumma 'alimal-ghaybi washshahadah, fatiras-samawati wal-ard, rabba kulli shayin wamaleekah, ashhadu an la ilaha illa ant, a'oozu bika min sharri nafsee wamin sharrish-shaytani washirkih, wa-an aktarifa 'ala nafsee soo-an aw ajurrahu ila muslim.

Ya Allah! Masanin abin da ke fake da na sarari! Mai kagen halittar sammai da kassai! Ubangijin komai, kuma mamallakinsa!  Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ina neman tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin shaidan da shirkarsa, da in tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wani Musulumi.

Ya karanta suratu As-sajdah (Alim lam mim, tanzilul) da suratul mulk (tabaraka).

اَللَّهُمَّ أَسْلَمْتُ نَفْسِي إِلَيْكَ، وَفَوَّضْتُ أَمْرِي إِلَيْكَ، وَوَجَّهْتُ وَجْهِي إِلَيْكَ، وَأَلْجَاْتُ ظَهْرِي إِلَيْكَ، رَغْبَةً وَرَهْبَةً إِلَيْكَ، لاَ مَلْجَأَ وَلاَ مَنْجَا مِنْكَ إِلاَّ إِلَيْكَ، آمَنْتُ بِكِتَابِكَ الَّذِي أَنْزَلْتَ وَبِنَبِيِّكَ الَّذِي أَرْسَلْتَ.

Allahumma aslamtu nafsee ilayk, wafawwadtu amree ilayk, wawajjahtu wajhee ilayk, wa-alja'tu zahree ilayk, raghbatan warahbatan ilayk, la maljaa wala manja minka illa ilayk, amantu bikitabikal-lathee anzalt, wabinabiyyikal-lathee arsalt.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Addu'o'in Tashi Daga Barci

Karanta Zikirin Safiya da Maraice

Karanta Zikiri Yayin Shiga Gida

Ya Allah! Na sallama raina gare ka, na maid a al'amarina gare ka. Na fuskantar da nufina gare ka, na dogara da kai (a cikin dukkan al'amurana) saboda kwadayin abin da keg are ka, da tsoron ka. Babu mafaka, babu matsira daga gare ka sai zuwa gare ka. Na yi imani da littafinka da ka saukar da kuma Annabinka da ka aiko.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user