Saturday 26 October 2019

KARANTA ILLOLIN ZAMA DA MATAR AURE GUDA DAYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Kwanakin baya da na wallafa wani rubutu mai taken OPERATION KARIN AURE DOLE nayi alkawarin cewa zan wallafa rubutu mai taken illolin zama da matar aure guda daya, Alhamdulillah yau Allah Ya bani iko.

Matsalolin Ma'aurata 


Marubuci: Datti Assalafiy

Ga bayanin illolin kamar haka.

1- Sai ka hada da hakuri domin watarana za'a kawo maka abinci babu ruwa ko cokali ta mance, bata tunanin akwai kishiya da zasuyi gasa wajen kyautata maka.

2- Idan kai matafiyi ne, dole kayi hakuri domin watarana zaka iya dawowa gida a gajiye, ka tarar da matarka bata nan tana makwabta, ta kulle gidan saboda ita kadai ce, dole ka jira a waje kamar bako sai ta dawo, musamman idan kayi rashin dace wayarta babu caji.

3- Zama da mace daya yana haifar da matsala na rashin fita sallah asubah, ko yawan makara a sallah musamman na asubah, saboda watarana zatace ta gaji, watakila ta manta ba ta tanadi ruwan zafi a flask ba, musamman a lokacin sanyi da maza sukafi jaraba, kuma bincike ya tabbatar da cewa iyaye mata sunfi samun juna biyu a lokacin sanyi fiye da lokacin zafi.

4- Idan matar aure daya gareka, ba lallai bane kayi dace a kullun sai ta kai maka ruwan wanka, watarana dawainiyar yara zaisha gabanta, ko idan bata da lafiya, amma idan akwai wata zata dauke maka wannan nauyin.

5- Wankin kaya, idan kai malalaci ne kana da kiwuyar yin wanki da guga, kuma sai ya kasance matarka daya, dole watarana lalura zai tarar da matarka ka kwashi kayanka ka kai gurin mai wanki, haka mai wanki zai hada kayanka da na wasu masu dauke da cututtuka da ake iya dauka ta jikin kaya ya wanke, karshe kaje ka kwaso cuta a sanadin zama da matar aure guda daya.

6- Idan kai mai yawan sha'awa ne, watarana matarka idan kwaya daya ce zata iya tsintar kanta tana jinin al'ada, ba yadda ka iya dole kayi ta fama da lemon-tsami da kunun-kanwa don ya rage maka sha'awa, wasu masu raunin imani basa iya daurewa matansu su kammala jinin al'ada, sai sun fita rage zafi da matan banza a waje, amma inda ya kasance matanka biyu shikenan zaka iya tsira da imaninka.

7- Idan matarka ta haihu, sannan idan ka kasance jarababbe, dole zaka jira sai ta kammala jinin-biki, musamman idan bata iya dabarbarun da zata rage maka sha'awa ba, saboda ita kadaice, wannan yayi sanadin da yawa daga cikin masu mata daya sun koma neman matan banza a waje suna kwaso cututtuka.

8- Idan matarka tayi tafiya na tsawon wasu kwanaki, musamman idan ta tafi aikin hajji, zakasha yunwa kafin ta dawo musamman idan baka iya girki ba, kuma baka iya cin abinci a waje ba, idan kai mai karfin sha'awa ne hakan zai iya kai ka ga aikata sabon Allah.

9- Idan matarka daya, kuma yaranka sun fara wayo, zaka shiga cikin yanayi na takuri, domin watarana kana ji kana gani yaranka zasu haramta maka yin jima'i da matarka, kuyi ta jira har sai sunyi bacci amma suki suna ta wasa abinsu, watarana sai kun basu kwayoyin da ke sa bacci kafin ku samu lokacin soyewa, illar zama da mata daya kenan.

10- Bincike ya nuna masu mata daya sunfi gajeren kwana a duniya fiye da masu mata biyu, uku zuwa hudu.

11- Mai mata biyu yafi mai mace daya samun lada a sallah na farilla kamar yadda wasu malamai sukayi bayani.

12- A babin ciyarwa da ilmantarwa da tufatarwa ga magidanta, masu mata sama da daya sunfi samun lada fiye da wanda yake matarsa daya ce tal kamar wutar fitilar vespa.

13- Anfi ganin kima da mutunci da darajar mutumin da yake da mata sama da daya fiye da wanda matarsa daya ce, domin anfi jingina rashin iya adalci ga mutanen da suka hakikance sai sun rayu da mata daya tilo, jama'a zasu zargesu cewa watakila ba zai iya adalci bane shiyasa ya hakura da mata daya.

14- Hakikancewa zama da mata daya yana haifar da barna a doron kasa, yana haifar da yawan fasadi da sabon Allah, kuma zama da mata daya kacal mugunta ne wa sauran iyaye mata da suke so a auresu, kuma zama da mace daya ba taimakon al'ummah bane,  musamman ga mutanen da suke attajirai.

Ina ku ke masu mata daya, ku fadi tsakaninku da Allah ba kwa fuskantar daya daga cikin matsaloli (14) da na liassafa a sama?

Idan jama'a sun fahimta, illar zama da mace daya ba wai ya shafi magidancin shi kadai bane, har da matar da tace ita dole sai dai a barta ita kadai, zata iya fuskan illoli, kuma illa ne ga al'ummah da a kullun mata kara ninka maza suke a yawa.

MAKALOLI MASU ALAKA:




Don haka duk wanda Allah Ya hore masa iko to yaji tsoron Allah Ya kara aure, akwai albarka da falala mai dunbin yawa a gidan aure, musamman idan aka gina auren saboda Allah.

Muna rokon Allah Ya taimakemu, Ya bamu ikon karawa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user