Friday 19 April 2024

Hukunce-Hukunce 8 Na Rancen Airtime Na Layi

Tura Wannan Zuwa
A Azumin bara (1436H) an mini tambaya game da bashin da kamfanin MTN yake ba wa masu mu’amala da shi. Ka ranci airtime na misalin N50, a ba ka na N45. A karon farko na bayar da amasar cewa, Haramun ne! Kuma zai shi ga babin ribal Qardh!.

Hukuncin Rancen Airtime Na Layi
Hoto: Tingtel



Daga baya na janye wannan fatawar saboda yadda na ƙara fahimtar mas’alar, na ba da fatawar halaccin ta, saboda dalilai kamar haka:

1. Wannan mas’ala ba bashi ne na kuɗi da kuɗi ba, ballantana batun ribal Kardh ta zo.

2. Abin da yake haƙiƙanin mas’alar shi ne, wani ne mai amfani ne da wannan kamfani na MTN ya sayi hidima ta aritime (airtime service) wadda suke sayar da ita N45, sai suka sayar masa ita a N50.

3. Kasancewar an ambaci kuɗi a ciki ba shi yake tabbatar da cewa kuɗi da kuɗi ne aka yi musanyan su ba. An yi musanyan kuɗi ne da wata hidima (airtime service) wanda masu ita suka ƙi ba shi ita a farashin da suke sayar da ita kuɗi hannu, suka ƙara masa wani abu akai. Wannan ba komai ne ba a shari’ance ba, saboda kayansu ne, suna da damar su yi maka ƙari kamar yadda suke da damar su yi maka ragi, kuma ka karɓa.

4. Abin da zai tabbatar maka da cewa, wannan abin da ka nema su ba ka ba tsurar kuɗi ne ba, hidima ce kawai, wanda aka ba shi ita a wayarsa ba za iya sayen komai da wannan ba a gurin wani ya ce yana da kuɗin biya a gurinsa, a she ka ga ba kuɗi ne ba, koda an rubuta alamar kuɗi a tare da shi.

5. Kamar yadda ya halatta katin waya na N100 a sayar wa da mai buƙata akan N110, duk da cewa ga shi a rubuce an rubuta N100. Ko a sayar masa da shi N95, wanda babu wani masani da ya taɓa cewa, wannan riba ce ko haramun ne, saboda musanyar kuɗi da kuɗi ne. Domin alal haƙiƙa wannan katin wayar mai ɗauke da N100 a kansa ba kuɗi ne ba, wata hidima ce, aka yi mata ramzi da wannan 100, shi ya sanya da zarar ka kankare ka shigar da ita cikin wayarka  za ka jefar da wannan katin tare da cewa an rubuta kuɗi a jiki, To wannn masa’al ta rance kamar haka take, don haka, duk wanda ya haramta wannan to wajibi ya haramta sana’ar sai da kati. Wanda ba na  jin akwai mai faɗar hakan.

6. Don haka ba magana ce ta an ba ni fatawa a baibai ba, magana ce ta sake nazari akan fatawar farko, wanda wannan abu ne sananne a gurin manyan malamanmu magabata da suke canza fatawoyinsu yayin da wasu dalilai suka bayyana gare su.

7. Wannan matsaya kuma shi ne matsayar wasu daga cikin abokai na ɗaliban ilimi bayan sun kalli mas’alar ta mahanga lilimi da sanin abin da ake kira riba, daga cikinsu akwai abokina Dr. Bashir Aliyu Umar kamar yadda daga baya na samu labari. 

8. Daga ƙarshe ina kira ga sauran ‘yan uwana ɗiliban ilimi mu yi kaffa-kaffa wajen sakin baki game da sha’anin halal da haram, al’amarin yana da haɗari. sanin madafar shari’a ta wanda ya karanta ta ne.

Allah ya sa mu dace. Amin. 
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user