Wednesday 10 April 2024

Shin Ya Dace Dukkan Mata Su Fita Sallar Idi?

Tura Wannan Zuwa Ga

Sunnah ce mata su fita Sallar idi kamar yadda Hadith ya kwaɗaitar da kuma maganganun magabata da suka yi bayani akan halarcin fitar mata zuwa sallar idi.


Sallar Idi
Hoto: Britannica


Marubuciya: Faridah Bintu Salis


Ummu Aɗiyyah Nusaibah Bint Ka'ab Al-ansariyyah (RA) ta ce: Annabi (ﷺ) ya yi umurni a ranar idi mata su fita, da 'ƴan mata, da mai al'ada amma ita ta nisanci wajen sallar (tunda ba yi za ta yi ba).” [Bukhari: 981, Muslim: 890]


Abdullahi Ɗan Abbas (RA) Ya ce: “Manzon ALLAH (ﷺ) Ya kasance yana umurtar ƴaƴansa. da matansa, su fita a idi guda biyu (Babba da ƙaramar Sallah).” [Sahihul Jami'i: 3888]


Sayyidina Abubakar (RA) Ya ce: “Wajibi ce Sallar Idi ga duk wacce take da kwatankwacin malulluɓi da zai rufe ta, ta fita zuwa idoji guda biyu ƙarama da Babba.” [Ibn Abi Shaibah ya ruwaito shi a Musannaf 2/182 da sanadi ingantacce] 


Alhafiz Ibn Hajar (Rahimahullah) Ya ce: “Alƙali Iyad Bn Musa ya naƙalto wajabcin Sallar idi hatta ga mata daga Abubakar da Aliyu da Ibn Umar.” [Fat-hul Baary 2/545] 


Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy (Rahimahullah) Ya ce: “Toh a sani wannan shi ne gaskiya da babu ƙoƙonto a kai na wajabcin idi hatta ga mata, saboda yawan hadisan da aka ruwaito game da haka, Hadisin Ummu Aɗiyya da ya gabata ya isar mana, ba sharʼanci kawai ya ke nunawa ba, hatta wajabcin hakan yake nunawa ga su matan, saboda umarnin da Annabi (ﷺ) ya bayar, asali kama umurni wajabci ne.” [Salatul Idaini: 15] 


Sunnah ne mata su fita zuwa Sallar Idi, don haka mata ku yi ƙoƙari ku halarci Idi, sannan a kiyaye sanya turare ko bayyanar da wani abu na ado, ku lizimci hijabi na Sharia kuma ku zamto masu natsuwa da kamun kai, sannan a yayin tafiya ku kasance masu bin gefen hanya ba tsakiya ba, kuma ku kiyaye cakuɗuwa da maza, idan kuka kasance haka sai dai ace daku: MASHAA ALLAH.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user