Wednesday 7 August 2019

KARANTA FALALAR WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA

Tura Wannan Zuwa
DON ALLAH MU KARANTA KUMA MUYI SHARING GA 'YAN UWA DOMIN NAKARANCI YAZAMA MATSALA TA WANNAN AL'UMMA IDAN ANYI MUTUWA SAI KAGA AN RASA MAIYIN WANKA, KO KUMA KAGA MALAMIN DAZAIYI WANKAN YANA TA MULKI SAI LOKACIN DAYAGA DAMA ZAIZO YAYI WANKAN.

Yadda ake yin Wankan Gawa


Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa:

‘’Duk wanda ya wanke mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau arba’in.’’

A wani hadisin kuma Manzon Allah (s.a.w) Yace:

”Duk wanda ya wanke mamaci kuma yarufa masa asiri, to Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljannah Kwarra, (wato Launin Tufafin).

SHARUDDAN WANKAN GAWA:

Daga cikin sharaddan wankan gawa sune:

{1}. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa misali:
Iyaye. kanne ko yayye “ya”yansa da sauransu).

{2}. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke Matarsa haka ma Mace za ta iya wanke Mijinta).

{3}. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi.


Yadda ake yin Wankan Gawa


YADDA AKE YIN WANKAN GAWA

Ana yin wankan gawa mara-mara ne misali:
Sau Uku (3) ko
Biyar(5) ko
Bakwai(7) ko
Tara(9)).

Hakan ya tabbata daga Manzon Allah (s.a.w) a cikin hadisin Ummu Adiya (R.A).

Wadanda zasu yiwa mamaci wanka su zasuyi la’akari suga wanka nawa yadace suyi masa.

Da farko dai kafin a fara wankan da akwai abubuwa guda Uku (3) da za’a fara yi wa mamacin.

Sune kamar haka:

{1}. Za’a cire masa suturar da take jikinsa, amma za’a sami dan kyalle a rufe masa al’aurarsa.

{2}. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi masa tsarki, na bangaren mafuta biyu.

(Bawali da Gayadi).

{3}. Idan macece , za’a tsefe kitson da yake kanta, a wanke kan, sannan ayi Lallabi uku a kan ( wato Kalba guda Uku).

Sai a kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata.

Idan namiji mai kitso ne sai a warware kitson gaba daya.

YADDA AKE WANKA SAU UKU (3)

Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi suyi masa wanka sau uku, to bayan sun gama abubuwan da suke sama saisu fara wankan.

Da farko dai zasu tanadi ruwa kashi Uku (3),

kowanne ruwa za'ayi wanka daya dashi.

(RUWAN FARKO)

Wannan wankan za'ayi wa mamacine wanka irin Wankan Janaba.

Da farko za’a fara yiwa mamaci alwalane, kamar irin alwalar Sallah, sai dai wajen kuskurar baki da shakar hanci za’a shafa masa ruwane kawai a bakin da hancin.

Bayan anyi masa alwala, sai kuma azuba ruwa a kansa a wanke masa har sau uku, sannan. kuma a wanke tsagin jikinsa na dama sannan na hagu.


Lokacin da Limami yake Sallatar gawar Mamaci


(RUWA NA BIYU)

Bayan anyi masa wanka na sama wato na Janaba, sai kuma asami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a wanke mamacin dashi.

Wato za’a sami Soso da Sabulu a cuda jikinsa sosai (Kamar dai yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu, saidai za’a iya amfani da Magarya ko Kanwa a maimakon Sabulun).

Bayan angama cuda shi sai a dauraye Kumfar da wannan ruwan.

(RUWA NA UKU)

Bayan anyi masa wanka na sama, wato na Soso da Sabulu, to sai kuma a sami ruwa na karshe wato na Uku a zuba Turare mai kamshi (Sosai) a ciki, sannan sai a wanke mamaci da shi.

Amfi son ayi amfani da Turaren Kafur, to amma idan ba’a same shiba to za’a iya amfani da duk wani Turare mai kamshi sosai.

Bayan angama wankan Turaren, sai a tsane jikin mamacin asa masa Likkafani.

Lokacin da aka Sallaci Gawar Mamaci


YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO BAKWAI (7), KO TARA (9).

Idan masu yi wa mamaci wanka sun zabi su yi masa wanka biyar (5), ko bakwai(7), ko tara(9).

To wanka na biyu(2) wato na soso da sabulu shi za su yi ta maimaitawa.

Amma dolene na Janaba shine a Farko, sannan na Turare shine a karshe.

MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU BIYAR (5).

{1}. Na farko shine na Janaba

{2}. Na biyu shine na soso da sabulu

{3}. Na uku shine na soso da sabulu

{4}. Na Hudu shine na Soso da Sabulu

{5}. Na Biyar shine na Turare.

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ZUNUBAI GUDA 100 WANDA AL'UMMA KE AIKATAWA BASU DAUKE SU DA KOMAI BA

KARANTA ABUBUWA GUDA 5 BA'A SANIN SU SAI DA ABUBUWA GUDA 5

KARANTA YADDA AKE DAUKAR RAYUKAN SALIHAN BAYIN ALLAH (MUMINAI)

KARANTA MAGANIN BASIR KO WANE IRINE DA YARDAR ALLAH

YA UBANGIJI KASA MU CIKA DA IMANI KA KYAUTATA KARSHEN MU AMIN.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: TAFARKIN TSIRA


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user